← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

S
ai biki ya koma sabo dal sakamakon zuwan Angon. Dan Nahuche jikan Nahuche. Habib, Mustapha, Bilyamin Nahuche. Biki yayi biki, biki irin na fulanin Girei wadanda suka hade da Zamfarawa suna nuna musu irin nasu culturesandtraditions din, wannan ya sa mutanen Nahuche suka dauki aniyar in suka dau amarya zuwa Zamfara sai sun kai ta har garin Nahuche ta gaida Kekun Nahuche da Uban Dawakin Nahuche suma su nuna irin nasu al’adun. Tunda burin iyayen Rahinah shi ne su nuna ita ‘yar asali ce ‘yar dangi ce suma dole su nuna Habibu dan asali ne dan dangi ne, ba’a fi su jela ba baza’a fi su iya taka rawa ba, kamar yadda ba’a fi su kwarkwata ba baza’a fi su iya susa ba.
Allah kadai ya san irin farin cikin da duk family din nan ke ciki na kowanne bangare. Habibu kuma da zuwan sa ya bude bakin aljihu ga dangin amarya da iyayen ta, komai sai da aka sauke mota guda tun daga kan ruwan sha. Lemo kuwa kamar a wanke gidan sarkin Fulani da shi. Kaji da zabbi kamar a tuka a yi tuwon su. Mutanen Girei sun dade basu ga biki irin na Rahinah ba, gashi dai a al’adance aka yi komai babu surkin modernity, amma komai ya wadata sannan tun daga fara bikin har zuwa karshen sa traditionalattire wato kayan saki na gargajiya Rahinah ke sawa irin na Fulanin usli, wadanda cousins din ta ’yammata sa’annin ta suka kakkawo mata matsayin gudummuwar su.
Habibu da Rahinah basu hadu ba ko sau daya a garin Girei, sai ana I gobe za su wuce Zamfara. Aunty Badiya ta yi kokarin su hadu, ko sau daya ne su gaisa a Girei, kowanne ya nuna mata ba ya bukatar hakan.
Yau kuma da suka hadun, Sarkin Fulani ne ya kira kowannen su da kan sa zuwa turakar sa, kusan a tare suka iso, Rahinah ta sha ado, sanye da wata guntuwar rigar Karen miski ruwan hanta, ta yi dauren zanin daga can saman cikin ta ta yi lullubi da yalwataccen mayafi fari, an yi mata wadansu irin kananan kitso wadanda aka lankwaso jelar su ta gaban goshin ta zuwa bayan kunnen ta, kitson ya saka fuskar ta tayi fresh tayi cute da ita ya fito da kyawun fuskar ta na halitta. Kan ta babu kallabi sai lullubin babban mayafin da ta yi.
Habibu sanye yake da yadin voyel mai taushi fari sol, da gani yau ya soma saka su, ‘yar ciki da babban riga wanda aka yi wa sassaukan aiki da farin zare. Komi nasa a saukake, kwalliyar sa mai sanyaya idanu, amma kallo daya zaka yi masa ka san ya kama kasa, kuma komai da yake sanye da shi mai daraja ne. Sassaukar rayuwa ra’ayin sa ce kawai amma kada kaso ka tona tsadar sittiru da takalmin da agogon da ke jikin sa.
Tana saka kai a kofar dakin sarkin Fulani shima yana sawo kai, saura kadan su yi karo da juna, itace ta yi saurin ja da baya ta bashi hanya ya fara wucewa bayan sun jefi juna da mummunan kallon da kowanne ya kunshe cikin idanun sa.
A ran ta ta ce “umh, mutum har mutum, fuska da zubi irin na salihai amma halin sa da zuciyar sa irin na mutanen farko (jahiliyya period).
Shi kuwa Habibu gani yayi gabadaya Rahinah ta canza a idanun sa, kuruciya ta karu mata, duk ta danyance masa kai bazaka ce ta taba haihuwa ba, balle katon yaro kamar Abdallah mai neman cika shekaru goma sha biyu. Kwatankwacin abinda ta fada a tata zuciyar shima haka ya fada a nasa ran, kamannin ta, innocent fuskar ta, zubin halittar ta duk basu yi kama da behaviours din ta na rashin tausayi ga mijin auren ta, na rashin compassion a zuciya da rashin karbar kaddara.
Ta fi kama da salihan mata masu sanyin rai, masu tausayawa da tallafawa mijin auren su, ba kamar nata halayen na zahiri ba. Ga ta stubborn ga ta unforgiving and wicked.
“Ku shigo daga ciki” inji sarkin Fulani, suka zauna suna fuskantar sa shi yana daga gaban su, sai da ya tabbatar sun bashi dukkannin nutsuwar su sannan ya fara da addu’a suka shafa, kafin ya maida hanklin sa kan Habibu Nahuche.
“Duk abinda ya faru da ku a baya, mun ji labarin sa, Ambasada ya gaya mana. Ina so ku dauka kaddarar ku kenan ta haihuwar wannan yaron, don haka ku maida komai ya zama tarihi, ku fusknci rayuwar da zaku fara yanzu.
Habibullahi na aika an kirawo ka ne domin in baka amanar marainiyar Allah RAHINATU wadda Allah ne ya hada ku ba mu muka hada ku ba, bata da uwa bata da uba a duniya sai mu da muka rage a raye, idan ka cutar da ita Allah ba zai barka ba.
Ke kuma Rahin, kin gama sanin gidan nan ba’a yaji, ba’a kawo kara, sannan ba’a zawarci. Don haka ne ma bana gaggawar aurar da ‘ya’ya na sai ga mazan da na tabbatar suna son su kuma zasu rike min amanar su ko bayan rai na. Sannan ya zamanto cewa soyayya ta hada su ba tursasawa ba.
Saboda haka na hore ki da yi wa mijin auren ki biyayya da zama uwa ta gari ga ’ya’yan ki. Mahaifiyar ki matar kwarai ce mutuniyar kirki ce da har ta koma ga mahaliccin ta babu wanda ya taba jin kan su ita da Modibbo Ummaru.
Bai taba kara aure ba sai a bayan ranta, inda ya auri Kulun da ta yi sanadin barin ku gida har duka wadannan kaddarorin suka faru”.
Habibu ya muskuta kadan, murya cikin sanyi yace ”wacece Kulu?” Sarkin Fulani ya bashi labarin komai daga farko har karshe har yadda Rahinah ta hadu da su ta sanadin Yafendo, Habibu ya saci kallon ta kadan, (she have never know her parents), sai yaji tausayin ta kadan ya kama shi, gara shi ya girma da Hajiyar sa har gobe yana jin dadin ta, ya dukar da kai yana magana a hankali,
“na karbi amanar ka da hannu bibbiyu Baba sarki, Allah ya bani wuyan dauka da hannun saukewa”.
Kawai sai Rahinah ta ji kuka ya zo mata. Wanda tun fara bikin bata yi shi ba. Don a baya komai ganin sa take kamar almara ko mafarki wanda anjima kadan za ta bude ido ta ga ba haka ba. Amma yanzu da Habibu yayi Magana da bakin sa ta yarda ta amince zahirin kenan.
Ta sake zama matar Hotelier (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche). Bambancin shine wannan auren ba irin na baya bane, wannan auren na mutunci da daraja ne, ya aure ta ne a hannun iyayen ta da kakannin ta, aure na adalci da martaba, to amma anya sauran tabban nasa da lahanin da ya yi wa zuciyar ta zasu taba gogewa daga zuciyar ta?
“Ku ta shi ku je, suna jiran ku za ku wuce. Allah yayi muku albarka”.
Nene Balki da Inna Dudu ne suka shigo dakin sarkin Fulani suka tafi da ita, a motocin Nahuche Hotels zasu wuce zuwa Zamfara wadanda tuni PA Rasak ya sa an kawo su manya-manyan Highlanders har guda 4. Sai wadanda ‘yan Nahuche suka zo a ciki dama ba su koma ba.
Wadanda Mr. Rasak ya kawo matan sarkin Fulani su duka hudun aka dauka a ciki da ‘ya’yan su mata, cousins din Rahinah da sauran ‘yan uwan su aka dauka a ciki. Rahinah da Nene da Aunty Badiya da Inna Dudu suna mota guda, a gidan gaban motar kuma matar Baban Nahuche ce haka suka kama hanya daga Girei zuwa Zamfara.
Habibu da PA din sa tare da Uncle da yaran sa suka wuce, suna tafe a hanya yana ta buge bugen waya yana bada order na yadda yake so PA Mr. Atiku ya tsaya a kan gyaran gidan sa na ‘Life Camp’ duk da gidan baya bukatar komai, amma yanzu mace ce zata zauna a cikin sa akwai bukatar abubuwan da babu cikin gidan. Su Uncle kuma sun ce ya basu dakuna zasu zuba kayan gado da kicin zasu zuba mata kayan girki. Yana ta gargadin PA Atiku kan ya tsaya ya ga cewa komai (is in place). Uncle na ta sauraron sa a fakaice yana ta mamaki, in ya ji kudaden da ake ta ciniki na abubuwan da za’a sa a cikin gidan. Murmushi yayi, a ran sa ya ce,
“sannu sannu ai bata hana zuwa saidai a dade ba’a je ba, yaro wa ya gaya maka Borno gabas take? Wa ya gaya maka ana yi wa matan gidan mu pretending?
******

KOFAR JANGE, ZAMFARA
U
nguwar Kofar Jange ta karbi bakin motocin wajen guda goma a jere da yammaci lis, lokacin da majalisar samarin Kofar Jange ta ke cikke taf! Kamar kullum. Nan da nan samarin masoya Habibu Nahuche suka soma tambayar junan su ko me ake yi? Don kafin isowar motocin wani makwabcin Hajiyar Nahuche ya kawo musu labarin akwai fa kishin-kishin din cewa NAHUCHE ya yi aure duk suka karyata shi, ta yaya zai yi aure bamu ji a media ba? Bayan kwanannan suka gama shari’a da tsohuwar matar sa a Abuja?
Sai ga wadannan bakin motocin nata fakewa a kofar “GIDAN NAHUCHE”.
Mata ne suka rika fitowa kafin su fito da amarya nannade cikin alkyabba, suna shiga gidan Hajiya Kaltume, ai kuwa nan suka gasgata labarin da Kalla ya kawo suka gwale shi, nan wajen ya kaure da sowa da surutun su.
Dai-dai da isowar sa cikin motar karshe, motar Alh. Usman Girei. Suna yin fakin samarin na yanyame motar fadi su ke;
“Allah ya bar mana NAHUCHE” “Allah ya taimaki NAHUCHE” shi kuma sai murmushin da ya saba ya ke yi (broad smile) cikin ginshira irin tasa. Ya kawo ihsanin da ya saba yi musu ya yi musu bayan ya basu hannu daya bayan daya, abinda suka samu yau ya zarta na kullum shikan sa bai san dalili ba, don ba zai ce farin ciki yake ba.....addua suka shiga yi a kan auren da suka samu labarin ya yi, tare da roka masa zuri’a mai albarka.
Wannan daban.
Chapter 8 · 0% Book details