← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ambasada ya fada cikin kulawa. Ya taka a hankali zuwa cikin kayataccen falon na tsohon Ambasadan, kyawawan kafafun sa na nitsewa cikin lallausar kilishin falon, har kasa ya tsugunna yana gaishe su, Uncle Usman ya nuna masa kujerar da ke fuskantar su, amma sai bai hau ba, ya zauna akan kafafun sa daga nesa da su.

Sun dauki dan lokaci su duka ukun babu wanda yayi magana a falon bayan gaisuwar data gudana. Zuwa can Ambasada ya ce “ya hanya? Kuma ya kokari? Ya a ka ji da jama’a?”

Uncle Usman bai bari ya amsa ba ya yi kwafa, sannan ya ce.

“Kayi hakuri Habib, wannan mahaukaciyar ta taso ka daga wajen neman abincin ka, amma yanzu Ambasada yake gaya min ya sa ta taje ta janye karar.

Na zo da zummar zane ta da dorina kan wannan rashin kan gadon nata, sai shi Baban nata ya bani hakuri ya ce yanzu haka ta tafi ne ta janye karar”.

Shi dai bai ce komai ba, amma a cikin ran sa cewa yake “Kash! Ai da kun bar ta, an goge rainin da ke tsakani na da ita a kan idanun duniya, watakila da ta fi hankalta, in ta gane ni ba sa’an yin ta bane. Ambasada ya kira sunan sa a hankali,

“Habibu!”

Bai amsa ba amma ya dago ya dubi Abba Jakadan. “Har yanzu kuna nan a kan bakan ku na cewa bazaku sulhunta ba ko saboda yaron nan? Wa ya gaya muku ana jayayya a kan yaro?”
Uncle Usman ya ce “ai su duka ya kamata su zauna yau a gaban mu, mu yi magana ta gemu kuma ta karshe mu da su, babu yaro cikin mu, kuma babu sa’an ku, wasa da hankalin da kuke yi mana ya isa haka”.

Ambasada ya dauki wayar sa yana kiran layin Rahinah, tana kallon wayar na ringing kamar yadda hantar ta da hanjin cikin ta ke kadawa suma, bata iya ta daga ba har ta katse. Sai ya kira Nene Balki.

“Ki zo min da Rahinah falon saukar baki yanzu”.

Nene ta hau kwankwasa mata kofa, ai kuwa Rahinah ta kara tsurewa. Bata son fuskantar kowa a cikin su sabida kallon da Habibu ya yi mata dazu a danja ya lalata dukkan karfin zuciyar da ta ke ji da shi. Ga shi bata san kiran me aka yi masa gidan ba.
Nene kawai sai ta murda kofar toilet din don ta fahimci ba wani abu take yi a ciki ba, ta ce “Rahinah lafiya? Buya ne kuma a toilet? To ki wuce Abba Jakada na kira”.

Koda ta dago ido yau Nene sai ta ga rauni a cikin idon ta, kafin a yi haka she’s always bold akan duk wani al’amarin ta da Habibu Nahuche.

Nene sai ta kamo hannun ta, ganin idanun ta sun cika da kwallah, ita kuma sai ta bi ta tamkar Rakumi da akala.

Shigowar su falon tare da Nene bai sa Habibu ya dago ido daga sunkuyawar da yayi ya dube su ba, but her presence overwhelmed him (ya ji kasantuwar ta a wurin acikin jikin sa). Amma hakan bai sa ya nuna ya san da shigowar su ba.

Gefen Habibu Uncle Usman ya nuna mata ya ce ta je ta zauna, zaman ta daura da inda ya ke zaune, da dan motsawar da yayi kamar ya kara zakudawa (ja baya) ya sa ta shako sassanyar kamshin ‘Carolina Herrera’ wanda ya tuna mata haduwar su ta farko a cikin jirgi, ranar da ta fara mannuwa da shi ta shaki wannan kamshin. Sannantheir second encounter at Cologne Public Library (haduwar su ta biyu a labiraren jami’ar Cologne) ranar da ta barar masa da littatafai ta shaki the same perfume, the subsequent encounters (sauran haduwarwakin da suka biyo baya har zuwa firstnight din su (ranar daren farkon su na aure).

A take ta ji dukkan karfin zuciyar ta ya dawo, kwanan nan ya kira ta muguwa, azzaluma. Shin tsakanin ita da Habibu idan aka dora a sikeli wanene mugu kuma azzalumi?

He took away her pride by force, sannan a arha, with no love nor affection. Wannan duk bai ishe shi ba, ya mayar da ita bazawarar shekara goma (ta manta ita ta nemi sakin by all means) ya kuma dauke dan ta kwalli daya da Allah ya bata tun yana zanin goyo ta hanyar sacewa.

Don haka wannan mutumin ba abun tausayi bane, selfishness and rudeness din sa are in style, sun barranta (banbanta) da kamannin sa na zahiri na kamili kuma salihin mutum.

Uncle Usman ya soma Magana cikin bacin rai. Bacin rai irin wanda daga Habibu har Rahinah, babu wanda ya taba ganin sa cikin kwatankwacin sa.

“Yau na ke fatan komai ya kare a tsakanin mu da ku. Ya kuma kare a tsakanin ku. Kodayake tsakanin ku ba zai taba karewa ba tunda zuri’a ta hada, amma bazamu zuba ido ku zubar da mutuncin junan ku a idon duniya ba, shi kuma yaro ku sa bakin duniya ya lalata shi.

Wannan shine zama na karshe da zai guda na, mun baku dama kowa ya fadi abinda ya sa ya kasa yafewa dan uwan sa da abinda yasa kuka zabi zama shekara goma babu aure”.

Dukkan su kan su na kasa, amma Rahinah gumi ta ke kashirban. Habibu ya dago a hankali ya dubi Ambasada idanun sa sun kada, sannan ya dubi uban Rahinah, kuma ubangidan sa sannan surukin sa Alh. Usman Girei. Murya babu karsashi yace,
“Ni ba abunda ta yi mun, ni ne ma na yi mata laifi kan laifi, na kuma roki afuwar ta tun a wancan lokacin. I’m not sure (bani da tabbas) ta yafe din ko bata yafe ba.

Rashin aure na shekara goma kuwa mai yuwuwa ne wannan ce kalar kaddarar mu. Amma ni ba don ita na ki aure ba, sabida ba ita ce autar mata ba.

A bayan haihuwar ta da kafin haihuwar ta an haifi dubunnan mata wadanda suka fi ta duk abinda ta ke takama da shi. Kawai bana ra’ayi ne. Don na san zan iya rike kaina. Amma yanzu na baku wuka da nama, ni Habibu Mustapha Nahuche, na amince ku aura min kowacce ‘ya kuke da ita, tsohuwa ko yarinya, budurwa ko bazawara, ko daga ina ta ke, komai munin ta, akan dai ku mayar min da wannan.....”. Ya nuna Rahinah da bakin sa cikin izgili, disgustingly da son tura haushi.

Ta dago a tsanake, idanun ta sun kada, domin sosai kalaman nasa sun buge ta, sun tura mata haushin har fiye da yadda yake so su tura. Maimakon ta dube shi ta maida masa martani, sai ta dubi Baban ta Usman Girei.

“Uncle, ba ka dade kana min maganar CMD ba? (Chief Medical Director) na Nizamiye, ina cewa ya dakace ni? Ai tuni na bashi damar fitowa kuma ya ce cikin satin nan zai je Yemen ya zo da Baffannin sa, su karbi auren. Ni wannan mutumin (ta nuna Habibu da baki) ba abinda ya yi min. Dan da ya shiga tsakanin mu kadddara ne. Amma ba don shi na ki aure ba.

Ban samu wanda ya kwanta min bane tuntuni sai yanzu, ina so ne in yi settling sosai da ayyukana kafin na yi aure. Kuma alhamdulillahi lokaci ya yi yanzu, na baiwa Dr. Irshad damar fitowa already”.
Ta kare da sunkuyar da kai sabida hawayen da ke son bada ita. Daga Uncle Usman har tsohon Ambasada sakin baki suka yi galala! Suna kallon su, sun rasa mai ya kamata su ce kuma, ko ta ina kuma za su bullo musu?

Sai Uncle Usman ya ce “toh-toh, yanzu kin yarda da auren bakon hauren kenan duk da baki ko san al’adun kasar shi ba balle irin mutanen da yake tare da su? Nasaba, halayya da dabi’a duk baki sani ba?”

Rahinah ta runtse ido ta ce “Uncle shi na zaba, na dade da sanin wasu daga cikin halayen sa musamman neman mata, amma wallahi ya fi min wannan sau dubu….” (ta sake nuna Habibu da baki). Kuma tunda kun hana ni kai shi kotu sharia’ah ta kwatar mun Da na, to ku karba ku bani......”.

Kawai sai ta fashe da kuka, ta jingina kai a jikin kujerar da Habibu ke jingine tana ta yi riiii-riii-riiiii”.

Ambasada ya ce “ai na sha gaya miki muddin ina raye Rahinah, babu mai yi miki auren dole, not evenyour father (ya nuna Uncle Usman). Na tsaya miki Rahinah, and I will foreverstand by you (kuma har abada zan cigaba da tsaya miki a matsayin ki na marainiya”.

Sai dai kuma Rahinatu bana son yadda kuke ta jayayya akan yaron nan, Allah da ya halicce shi ya fi ku son sa, kada ku tabo fushin sa. Yau da iyayen da suka haife ki suna raye, na tabbata zasu maida ke gidan uban dan ki ne ko ba tare da yardar ki ba.
Mu da mu ke matsayin iyayen ki a yanzu muna neman “ALFARMA”. Ki yi mana alfarma ki koma gidan mijin ki, zai je har GIREI ya nemi auren ki cikin mutunci, adalci da girmamawa yadda duk ya kamata a hannun iyayen ki, sadaki kuwa sai abinda kika yanke.

Bayan auren kuma, za mu cigaba da bibiya mu tsaya mu ga cewa ya rike ki da amana, adalci, soyayya, daraja da mutumtawa.

For our sake! For Abdallah’s sake, for your late Daada’s sake, for the sake of the love you have for your son……(sabida mu, sabida Abdallah, sabida marigayiya Dadan ki, sabida kaunar ki ga dan ki) ki manta komai, ki komawa Baban sa. In na ce komai ina nufin KOMAI”.

Ya hada hannayen sa biyu cikin alamun roko. Kafin Ambasada ya kai karshen maganar sa kukan Rahinah ya cika falon, ya nunka na baya. Ta rasa inda zata saka kanta. Habibu ban da jibi (zufa) ba abinda yake yi.

A wannan lokacin ya rasa takamaimai a matsugunin da zuciyar sa take, wani irin duka zuciyar sa ke yi tana lugulgude a tsakiyar kirjin sa. Addu’a yake Allah yasa kada Rahinah ta amince da rokon Ambasada Shehu, don bashi da gurbin da zai saka ta cikin rayuwar sa yanzu.
Chapter 4 · 0% Book details