← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shaidar biya
07030137870
[8/13, 10:16 PM] +234 816 049 3429: A hankali ya sunkuyar da kai, kafin ya dago ya dubi Yayar sa da mijin ta.
“Ku yi min alfarma ku ci abinci ku yi sallah ku natsa” yace da su finallycikin muryar sanyi, bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, daga Aunty har Uncle basu katse masa hanzari ba sun bashi dama yayi tunanin sa positively.
“Ba zan iya cin wani abinci ba sai ka tabbatar min zaka bi mu zuwa Girei Habibu”. Inji Badiya.
A hankali ya gyada mata kai alamar zai bi sun. Uncle ya ce, “to alhamdulillahi, ina Abdallah? Cikin kunkuni ya ce.
“Ba zan gaya muku inda yake yanzu ba don ban shirya ba da shi ga uwar shi ba”.
Dariya Aunty ta yi, sabida farin cikin ya yarda zai bi su zuwa Girei kadai ya karbi auren sa da kan sa ya wadatar da ran ta.
“Can ta matse muku, a bamu masauki mu je mu huta”. Inji Aunty.
Waya yayi wa mai kula da share-sharen gidan ya zo ya tafi dasu sassan baki, Kuku kuma tuni ya shirya musu abinci ya kai, ya san ba wanda zai yi masa wannnan karambanin na kawo su Anty Ikoyi sai Mr. Rasak.
Amma bai ce masa komai ba don shima yanzu ya ji dadin zuwan nasu, domin ya yaye masa damuwar da yake ciki kaso tamanin cikin dari 80%. Kuma shine babbar maslaha ga mutuncin sa aidanun iyayen Rahinah, dama ita Rahinar kan ta.
Ba wai sulhu yake nema da ita ba, illa shi mutum ne mai yawan submissiveness, wanda idan yayi laifi ya kuma gane daga baya yayi laifin, ko aka nusar da shi, yake gaggawar mika wuya nan da nan ga gyara wannan laifin.
Sun tattauna sosai a daren shi da ‘yar uwar sa. Duk abinda suka kashe ita da Hajiya da Uncle da su Baban Nahuche wajen hidimar auren sai da ta kwashe ta labarta masa, don ya san ba a banza ya samu Rahinah ba wannan karon.
Tace atampopin ‘suddaje’ kawai daga Super sai Holland muka zuba, sauran da suke kanana ‘yan uwa ne suka baka gudummuwar su har da Shafa’atu".
He felt loved! Sabida ko kana da shi, idan ‘yan uwan ka da iyayen ka suka yi maka aikin zumunci da kara irin wannan dadi ka ke ji. Ya ce da Anty zai maida mata kudin kayan suddaje din da na lefe cikin account din ta, Aunty ta harare shi nan ta hau shi da fada, inda ta ce,
“ka ji min yaro, lefe ai gudummuwata ne dama, suddaje gudumuwar Hajiya, Paute gudummuwa ne daga gare mu zuwa ga zuri'an amarya, sauran hidimdimun kuwa duk daga ‘yan uwa na Nahuche suka fito, fatan mu Habibu kada ka bamu kunya, ka zauna lafiya da uwar dan ka, domin dukkan ku kuna bukatar juna”.
Bai ce komai ba, domin duk jikin sa ya yi sanyi, sai ya samu kan sa yana mai tambayar kan sa da gaske yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa ta yanzu ko kuwa Anty ta dai fada ne don ta ji dadin bakin ta???

Daga can kasan ransa sai ya ji wani sako na amsawa da cewa "YES! Har gobe yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Irin bukatar da nisan shekaru ko tsufa ba ya taba canza ta.
Iyayen sa da ‘yan uwan sa basa bukatar komai daga gare shi duk da Allah ya bashi wadata, burin su kadai ya zama cikakken mutum ta hanyar yin aure da wadda suka tabbatar ita kadai yake so.
Ko don albarkacin Hajiya, Yayar sa Badiya da Uncle Usman zai sassautawa zuciyar shi, zai karbi Rahinah da duk irin fuskar da ta zo masa; da tsiya ko da arziki. Wato duk irin rayuwar da ta zaba musu ita za su gudanar.
Aunty ce ta katse masa tunani da cewa “in aka zaba mata ta zauna?”
Ya dan zakuda kafada yace “I have no idea. The choice is her’s (wato zabin nata ne). Tunda ni ba mazauni bane na wuri guda ba”, Aunty ta ce,
“na san ma Abuja za ta zaba, ko don saboda ayyukan ta”.
Dan kyabe baki yayi irin na ba matsalar sa bane wannan.
A daren yayi musu booking din jirgin da zai juya da su Adamawa a washegari har da Mr. Rasak wanda ya nemi alfarmar halartar auren Ogan su, don Aunty ta gaya masa tun jiya da ya dauko su.
“Halan bai gaya muku cewa shi ango bane ko? Maman Abdallah za ta dawo!”.
“Congratulations Oga, congratulations Boss!”
Inji duka ma’aikatan gidan.
"May yours be among the best!".
Kowa sai da ya fadi irin fatan alkhairin sa, domin hakika sun yi farin ciki.
Washegari tun sassafe gabadayan su suka biyo Arik-Airdaga Ikko zuwa Adamawa.
******

ADAMAWA, GIREI
A
saukar sa a Adamawa, ba abinda ya fara zuwa ran sa illa, da ya samu nutsuwa abu na gaba da zai sa a gaba shine zai samar da Nahuche Hotel a jihar Adamawa, tunda Adamawan ta zama wani bangare nasa yanzu.
Ita ce tushen mahaifiyar Abdallah kuma garin kakannin sa na wurin uwa, ko don su samu wurin sauka idan suka zo garin. Ilyasu Uncle ya yiwa waya, ya dauko motar sa da ya bari a Girei ya zo ya dauke su zuwa Girei. Basu tsaya a ko’ina ba sai kofar familyhouse din su Rahinah, wato gidan Sarkin Fulani.
Tuni labari ya riski jama’ar gidan, da ma ita Rahinar kan ta, cewa Angon Rahinah ya iso daga Lagos. Safeenah ce ta shigo mata da wannan labarin, wanda ya sa ta saurin runtse idon ta a ahankali tana ambaton sunan Allah. Ba don ta yi farin ciki da zuwan nasa ba sai don faduwar gaban da ta bakunce ta.
Tana so ta tambayi Saffeenah ko tare da yaro Abdallah suka zo? Sai dai ta daure ta yi fulako ta yi shiru.
Yau wace rana ta gwada kawaici akan Abdallah. For the first time a tarihin rayuwar su da ta ji zuciyar ta ta dan rankwafa akan Habibu Nahuche, tunda dai har ya sauke girman kan sa ya biyo ta garin iyayen ta.
*****
Chapter 7 · 0% Book details