← Book details Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 10

Sashe 3

Nahuce Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinci ta ke ci a dakin Yafendo, abinci mai rai da motsi da Nene Balki ta dafa mata na musamman, tana ci suna hira ita da Yafendo hankalin ta kwance ya tsumma a randa. Tana fadi cikin ran ta jibi I yanzu suna gaban alkali ita da dan Nahuche. Har Lawyer ta dauka mai zaman kan ta daga Chambar Lauyoyi masu zaman kan su na garin Abuja.
Sai ganin Daddy Ambassada ta yi tsaye a kan ta rike da jarida, tsabar bacin rai ko sallama bai yi musu ba. Ya ce
“Rahinatu, me na ke gani haka?”
Ashe baki da hankali baki da tunanin dana ke ganin kina da shi?”
Ya jefa mata jaridar ‘Daily Trust’ akan cinyar ta sannan ya ce “maza-maza ki je ki janye karar nan, kafin in kifta ido na, wa ya ce miki ana jayayya a kan yaro? Kina so Ubangiji ya yi hukuncin sa a kan sa? Kina son ku rasa shi gabadaya ko? In kina son rayuwa da yaron da gaske, me zai hana ki koma gidan uban sa?”
Rahinah ta sunkuyar da kai, bata ce komai ba, ganin yadda Ambasada ke tafarfasa, ko wa ya kai wa ‘yan jarida labarin kuma? Bata yi don ta bata ran iyayen ta ba da masu kaunar ta, ko don a yayata su a mediasai don kwatarwa kan ta ‘yancin ta da Habibu ya bi ya danne ya ke kuma kan dannewa, domin so ya ke har ta mutu ba ita babu dan ta.
Ita ba don a sa a media ta kai Habibu kara ba, ta kai shi ne don shari’ah ta kwatar mata dan ta, tunda ta bi shi ta lalama ba wanda ya ji ba wanda ya gani amma ya bi ta da gatse da bakar Magana. Ya raina mata hankali.
“Maza-maza ina umartar ki da ki tashi ki je ki janye karar nan, yanzu yanzun nan kafin isowar Usman, ya gaya min ya taso a jirgi, zai saba miki yadda ba kya zato. Don ta ni kin sani mai sauki ne, har kullum Uba nake mai fahimtar ki da bin ra’ayin ki, mai yawan yi miki uzuri, hadi da baki damar da Allah ya ce a baki. Amma a wanan karon bana bayan ki Rahinah.
Akwai muhimmiyar Magana da dama nake so mu yi a yau, kawai na ci karo da wannan shirmen naki ana sayarwa a hanyar motoci, tashi maza-maza ki je ki janye ki dawo kafin isowar Usman don ya gaya min kan azahar zai sauka a garin nan.
Rahinah ta dan tsuke baki da fuska cikin alamun gardama, karo na farko da zata yi wa Ambasada musu, Yafendo da bata gane akan me ya ke ta fadan ba ta ce.
“Me ke faruwa ne Jakada?”
Nan Daddy yayi mata bayani a takaice “Rahinah ta kai Habibu kara kotu, a kan ya bata dan ta!”.
Sai ga Nene Balki ma ta shigo, ta tsinkayi karshen maganar da yake fadawa Yafendo, salati suka hau yi a tare, Nene na fadin “Rahinah kan ki daya?” Yafendo ta ce “ko kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? Don an ce min yanzu a kasar nan mata sun koyi shaye-shaye, kuma kika kunshe baki kika yi shiru kina sabgogin gaban ki hankalin ki kwance kamar kin kashe rai, sai zabga lomar abinci kike, Allah ya raba mu da kotu, ko makiyin mu kada Allah ya kai kotu balle Baban Abdullahi, ‘yar nema, ja’ira.”
Nene kuma ta ce “Rahinah ki komawa uban sa mana! In kin san kina son yaron ki da gaske? Ki rayu da su har abada cikin salaama da aminci, wannan taurin kan da girman kan ba naki bane a matsayin ki na ‘ya mace, na rasa ina kika koyo su, ita ‘ya mace da rauni aka san ta da yafiya ga mijin auren ta, ki tashi maza ki bi umarnin Abba Jakada, kin ga shi bai iya fada ba, kada ki sa yau a kan ki ya koya”.
Cikin bacin rai Ambasada ya ce “ai ni bata dauke ni Uba ba shi yasa ina ta Magana tana ji na ta yi kunnen uwar shegu da ni, ku bari uban ta na halali ya zo, shi in ya sa ta za ta yi, ya ce min har da dorina sai ya buge ta wallahi”.
Kalaman Ambasada Shehu na “bata dauke ni Uba ba, ku bari uban ta na halali ya zo” sun taba zuciyar Rahinah sun kuma karya ta. Ta mike tana hawaye ta isa gaban Ambasada ta durkusa, cikin rawar murya take magana.
“Ba ni da uban da ya fi ka Daddy, ka yi min abinda kowanne uban halali yake yi wa ’yar sa. Ka yi hakuri zan je in janye yanzun nan. Saboda kai!”.
Ambasada ya juya ya fita sakamakon kiran sa da ake ta yi a waya duk akan maganar, wadda ke kara yaduwa kamar wutar daji a garin Abuja. Ita kuma ta dauki Jilbaab din ta da mukullin mota jikin ta na rawa ta fita.
Lawyer data dauka wato Barr. Hanifa Suraj Kumo (AMANATA) ta fara kira tana hawaye tana tuki, ta gaya mata Baban ta ya ce ta janye karar, so ta janye, amma kudin da ta riga ta bata ta bar su. Barr. Hanifa ta ce baza’ayi haka ba, zata maido mata da ko rabi ne. Sannan ta karasa kotun, cikin dan lokaci ta janye karar.
Al’amarin da bai yi wa ‘yan jarida dadi ba, don sun so samun kudi sosai da issue din Nahuche da ex-wife din sa. Kasancewar Habibu Nahuche wani matashin miloniya mai farin jini a kasar Najeriya. Tana hanyar dawowa gida, Uncle Usman ya iso, Ambasada ya tura direban sa ya dauko shi daga filin jirgi, suna falon saukar bakin sa suna kara tattaunawa akan al’amarin.
“Na tura ta yanzu kan ta je ta janye” inji Abba Jakada.
Sai ga wayar Habibu ta shigowa Uncle Usman, inda ya gaya masa “ga shi ya sauka daga Lagos shima yanzu, an aika masa SAMMACI, wai wata mahaukaciyar Likita ta kai karar sa, zai halarci zaman kotu jibi tare da ita”.
Uncle ya kasa gane halin da muryar Habibu ke ciki a wannan lokacin. Sai ya ji sunan da ya kira Rahinah da shi ya ba shi dariya, ya kuma dace da ita ya ce masa,
“ina gidan Ambasada yanzu haka, nima ban dade da shigowa garin ba, ka bar duk abinda ka ke, ka zo ka same ni a can. Maitama ne”.
Habibu ya juya yayi wa PA din sa na Abuja Magana wanda shi ya dauko shi, ya bashi umarnin su fara zuwa gidan Ambasada Shehu kafin ya kai shi gidan sa na Abuja da ke a ‘Life-Camp’.
A dai-dai wani shatale-tale (roundabout) na kan titin da zasu bi su dauki hanyar unguwar Maitama, danja ta tsayar da su.
Kusan a tare suka tsaya da motar da ke barin daman su kirar KiaPicanto fara sol, kamar an ce da shi ya kalli matukin motar, sai ya dan janye jaridar ‘daily trust’ da ke hannun sa yana dubawa, wadda ke dauke da kanun labarun kai shi kotu. A gefen nasu mace ce fara sol ke jan motar, sanye da (Egyptian Jilbaab) ruwan kasa-kasa, hannayen ta biyu da ke dafe da sityari sun sha zobban zinare guda uku-uku, bai dauki ‘yan sakanni ba kwakwalwar sa da kyawawan idanun sa suka gane ta; Dr. Rahinah Omar Girei.
Itama jin alamun idanu a kan ta, sai ta waiwaya kadan, motar su kirar bakar ‘Chevrolet-Volt’ wadda bata da yawa ko a cikin Abuja ba itace ta dauki hankalin ta ba, kamar HandsomeMan din, mai wani irin sassanyan kyau da aji na musamman, wanda ke kwance cikin lallausar farar shaddah Wagambari a bayan motar.

Ko mutuwa ta yi ta dawo wannan fuskar bazata taba bace mata ba, lumsassun idanun nan masu son shigewa cikin nata a yawancin lokuta, har yanzu suna nan yadda suke farare kal, a lumshe, cikin farin glasses tar-tar da shi kamar ba glass ne a idon sa ba sabida garai-garai din sa; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche, shi ke kallon ta cike da wata irin lumsassar ‘tsana’ kwance cikin kyawawan kwayan idanun sa.
Yatsun ta masu dauke da zobban zinare ta kai tana danna maballin dake jikin motar ta, glassai bakake suka maye gurbin masu haske su ka yi sama zuuu! Kamar yadda ta kautar da kai itama, cikin tsananin faduwar gaba marar misaltuwa.
Dai-dai lokacin danja ta basu hannu, ta wani irin zugi motar da gudu ta tsere musu. Ashe an yi ba’a yi ba, an gudu ba’a tsira ba.
Domin kuwa kusan a tare su duka suka isa gidan Ambasada Shehu Bichi da ke unguwar Maitama, ta riga su shiga, har ta adana motar ta a ma’adanar motoci kafin su iso, akan idon ta mai gadi ya bude musu kofa suka sulalo cikin gidan kamar ita kan ta motar tasu tafiyar takama take yi tamkar Ba-Rumen ubangidan nata (dan kabilar Rumawa).

Kafin PA Mr. Atiku ya gama parking ya fito don ya bude masa, ya bude da kan sa ya fito.
Rahinah bata tsaya ba, kusan da gudu-gudu ta karasa shigewa cikin gida, bata sani ba ko da ace ta tsaya din sun jera, ko alfarmar kallo ba zata samu daga Habibu ba.
Dakin Nene Balki ta fada ta shige toilet ta rufe, don ta san nan ne kadai waje na karshe da za’ayi tunanin neman ta cikin gidan. Addu’ar ta daya kada ya kasance wani ya ga dawowar ta, balle a neme ta.
Sai dai kuma tana shiga toilet din Nene na shigowa dakin, ta kuma ga rufo kofar toilet din data yi, sannan kamshin turaren ta ‘Nina Ricci’ shi ke fallasa ta a duk inda ta s higa.
Nane bata kawo komai ba a ran ta, ta dauka ta shiga ne don yin alwallar sallahr azuhur.
******

Is not for free. It's 1000 via
3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank
[8/11, 12:21 PM] +234 816 049 3429: *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870

*BAKO DAGA IKKO*

"Karaso daga ciki Habibullah”.
Chapter 3 · 0% Book details