← Book details Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 13

Sashe 5

Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wallahi Babu shina ke so kuma shi zan aure...." dukan da Inna ta ɗana min ne a gadon baya yasa ban ƙarasa sauran maganar ba, ƙara nasaka ina faɗin,

"Inna dan Allah ku barni wallahi shi nake so na aura".

Ajiyar zuciya Mahaifina ya sauke kana yace,

" Wallahi Maryam badan komai zan hanaki auren wannan bawon Allah ba sai rashin halinshi kuma kowa yasan gidansu basu da asalin mai kyau, gaba nake guje miki ba baya ba Maryam, ke kaÉ—ai gareni dan haka ina son rayuwarki tayi fiye da tawa".

Hannu na É—aura akai ina kuka tabbas ba wanda zan aure sai Abbas, Inna ko ta tafi tayi min hukunci sai Babu ya hanata yace ba duka ya kamata ba, addua ya kamata muyi ma maryam Allah yasa ta gani abinda muke mata hange.

Ina taƙaitamuku na wahala iya wahala tun Babu na bina ta lalama har ta kai da harshi ke dukana, saboda na gani abinda suke nufi har abinci sun hanamin sun ɗauke min duk wata sutura tawa sun kyautar ba abinda nake a gida sai akin wahala duka safe dab na rana dab, amma duk da haka bai sa naji na sauya ra'ayi na ba.

Da ƴan uwa suga naƙi sauya ra'ayi na, dan haka suka bawa Babu shawara akan ya bari ayi auren tunda nace shi nake so, danaje na jawowa zuri'ar su abin kunya gwara anmin auren kowa ya huta.

Ba dan Babu da Inna sun so ba aka ɗaura min aure da Abbas, kuma duk da haka lnna da Babu sunyi min sha tare na arziki dan kowa yaga ɗakina sai ya jinjinama ƙoƙarinsu.

Bayan wata biyu da auren mu da Abbas lokacin ne ya fara nuna min wayeshi kuma ya halinshi suke kuma a lokacin kuÉ—i sun zaunawa Abbas fiye da tunanin mai karatu......

_*PLEASE AND PLEASE JIYA KUNJINI SHURU DAYAKE MUNA HUTUN WEEKEND KUMA ƊANKU JA'AFAR BASHI JIN DAƊI SHIYASA KUKA JINI SHURU, INA MAI BAKU HAƘURI DUK DA BA LAILENE NARIƘAYIN POSTING A WAƊANNAN RANANKUN BA SABODA AIKWAI UZURI.*_

*Comment and share pls*

*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

*Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haÉ—u*
And now
*Mijin Babata ne*

*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE ZUWA GA MASOYIYATA KUMA ƳAR UWATA MUMY KULSUM, (Zakiyya).*

*SHAFI NA BAKWAI*

Tunda na cika wata biyu Abbas ya daina zama gidana ya daina kulani ba abinda ke haɗani da Abbas face ya bani abinci nace, idan ya fita baya dawo wa sai cikin dare koshi gaf da sallah asuba, kuma da an dawo masallaci zai fita, ashe Abbas ya gama gina wani gida ya zuba ƴan aiki maza da mata to a can ya tare komai nashi ya koma can, kai ina taƙaice muku halin Abbas shine ɗan bala'in son mata ne, dan a yadda Abbas yake ga wannan lokacin ko ƴarshi zai iya kwana da ita bai damu ba.

Gani yana da kuɗe ne yasa yake ta iskancin da yaso, kowani gari yaji an buɗa sabowar bariki sai Abbas ya kai ziyar, ba barikin da ba'a san Abbas ba sai idan ɗan barikin ya kasance sabo, kuma duk barikin Abbas bai kwana da macen da wani ya taɓa kwana da ita, yara ake kawo masa guda biyu ƴan mata waɗanda suka karɓa sunan su ƴan mata, Abbas ko bai je barki ba yana da kwalwanai masu kawo masa ƴan mata har gidan hutawarshi, kullum kwanan duniya Abbas sai ya kana da ƴan mata sama da biyu saboda shi zai iya zube ko nawa ne dan ya samu mace, idan yaga mata jikinshi har rawa yake shi da burinshi ya kai gare su, ashe duk wannan abun da yakeyi iyayenshi na sane, ranar da nagaji da jin jita-jita na wanke ƙafa naje na gayawa iyayenshi halin da ake ci wallahi kamar sumin duka, faɗa suka riƙa yimin wai ya nake so yayi , ni ke bashi kuɗin da zaije ya nemi mata da zan samishi ido, haka dai na dawo gida zuciya ba daɗi.

Haka naci gaba da zama da Abbas har nayi haihuwa uku dashi kullum cikin kunci nake, duk wanda ya dubeni ya san ina cikin damuwa amma iyayena basu taɓa cemin miyake damuna ba, haka nima ban taɓa cewa ga abinda ke damuna ba, ina cikin haka har ciyon zuciya mai tsanani ya kama ni, ina nan tsaye ban kwanta ba sai ranar wata safiya ina zaune yara sun fita makaranta sai ga dan dazon mutane sun zo ƙofar gidana wai suna neman mai gida nace musu baya nan jarirai suka bani guda biyu wai idan ya dawo nace gashi inji wance, kin ƙarɓa nayi suka ce wallahi sai na karɓa nace wallahi bazan karɓa ba sai dai sukaiwa mahaifiyarshi, haka kuwa suka je suka kaiwa mahaifiyarshi, tundaga lokacin ciyo zuciya ya fara kaini ƙasa nayi baƙi na rame na koɗe kamar wata ƴar unwa.

In taƙace muku abin Abbas kullum ƙaruwa yake ba ragowa ba, dan haka na yanke sharar zan barshi kuma zan nemi ya sake ni, da yake namiji idan yana ji da kuɗi duk abinda yake son yi shi ya keyi, ban sha wahala wajan ƙarɓar takarda hannunshi ba sai dai niko nasha wahala kafin ya bani yara, duk da iyayena ba ruwansu a wannan lokacin sai da suka min baki na ƙarɓi yarana amma Abbas yaki ya bani su, Hauwa ce kaiwa nasamu na saceta na gudu garin iyayena, bayan kwana biyu da guduwana aka aiko min da cewa yarana mota tabi ta kansu sun mutu, wai makaranta zasu je ba wanda zai tsalakar dasu ti-ti shine suka tsalaka da kansu to basu ankara ba sai ganin mota ta take musu kai, nashiga tashin hankali sosai nayi kuka har na dangana nabarwa Allah na dawo riƙon ƴarta Hauwa, kuma babu wani lokaci mai tsayi tsakanin rasuwar yarana da Babu, itama lnna sanadin haka ne hauwan jini ya kamata koda aka waye gari babu ita.

Nashiga damuwa kuma nashiga baƙin ciki daga baya na zo na fara sana'a har na sanya Hauwa makaranta kuma ko makaranta ta ƴaƴan musu kuɗi nasa Hauwa duk wani gata da ɗa ke son samu wajan iyayenshi to naba Hauwashi , ta sauki alƙu'ani har ta fara harda, ana cikin haka nasamu miji nayi aure kuma ya yarda naje da ƴarta.

Intaƙaice muku Hauwa girama ya kamata son kowa ƙin wanda yarasa amma sai me, tunda Hauwa ta girma aka fara kamata ɗakin samari, tsofafi nasata longo suna taɓa mata jiki suna bata kuɗi, dana ji labari sai na gayawa mijina dama to akwai yaron da ke son Hauwa da aure dan haka muka haɗashi aure da ita ashe duk da haka ban tsira ba.

Sun jima a haka shida ita yasata jikinsa yana bugun bayanta itama haka da yake mata har ta soma jin bacci, mutsi ta farayi kana tace ita gida zata koma ya zo sutafi Mumy zata ganshi.

Baiyi musu ba ya sanya kayanshi suka koma gida, ranar Mumy da kanta ita ta É—aura sanwa ta dafa mishi abinda take so.

Bayan sallah isha'i sai ga ruwa kamar da bakin ƙwarya dan haka sukayi saurin bacci.

Dare ya tafi sosai sai mijin Mumy ya taso a hankali har yazo parlour saman kurar da Hansa'u ke kwance ya ƙaraso, zama yayi a hankali kana ya fara shafar fuskarta, da yaji bata farka ba sai ya shigar da hannusa cikin rigar baccin ta yana lalobar sassan jikinta.

Can cikin bacci ta fara jin sabon yanayi sai ta fara miƙi alamu zata farka, amma bata buɗe idonta ba, kuma baccin bai sake ta ba, shi koma bai daina yawo da hannunshi cikin jikinta ba, da abin yayi masa daɗi ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya fara ƙoƙarin shigar da hannunshi cikin pant ɗinta, cikin bacci taji wani abu mai zafi yashige ta, lokaci ɗaya ta farka a riƙece haɗi da sanya wata ƙara tana faɗin,

" Wayyo Mumy kwarto!!!.

Da yake É—akin duhu gareshi sosai kafin mumy ta taso shi yayi kamar fitowa zaiyi daga É—akin da Mumy take yana faÉ—i,

"Ina yake Hansa'u!".

Mumy ce ta fito haɗi da kunna fitala ta ƙaraso wajan Hansa'u tace,

" ina yake bai miki komai ba?".

Ta faÉ—i haka jiki na karkarwa kamar tayi kuka.

Da sauri yacewa Mumy bari yaje ya duba.

Fita yayi yayi dube dubinsa ya dawo yace shi bai ga komai ba, wata ƙila ma mafarki ne takeyi tunda kinsa ba yau ta saba irin wannan mafarkin ba, ai ko shekarnjiya sai da kika zuba mata ruwa ga jiki sannan ta farka ko ba haka ba".

Duben Hansa'u Mumy ta sakiyi da kyau kana tace,

"Ke gaya min gaskiya mafarkine kika yi ko yaya?".

"Wallahi mumy najishi yanasa min hannu cikin nan É—ina".

Ta faɗi haka tana kuka haɗi da nuna ƙasanta.

Tun Mumy batayi magana ba yace,

"Ba abinda ya sameta mafarki ne takeyi dan haka ki tashi mutafi mu kwanta dare yayi".

Ya faÉ—i haka a tsawace.

Ran mumy baiyi daÉ—i ba amma duk da haka ba yadda zatayi ta cire Hansa'u daga jikinta ta tashi ta bi mijinta É—aki.

Ba jimawa da shigarsu sai taji sun fara ihun da suka saba.

Kai ta haɗe da ƙafafu ta fara kuka ƙasa-ƙasa.....

*More comment*
*More typing*

*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️MIJIN BABATA NE*🤦‍♀️🤦‍♀️

*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

*Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haÉ—u*
And now
*Mijin Babata ne*

*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE ZUWA GA MASOYIYATA KUMA ƳAR UWATA MUMY KULSUM, (Zakiyya).*

*SHAFI NA 8️⃣*

Haka Hansa'u tayi rabbin bacci a zaune, sai dai bacci ɓarawo ne ya saceta, amma duk hankalita a tashi yake.

Mumy suna cikin ɗaka ita da mijinta amma gaba ki ɗaya yau hankalinta yanaga ƴarta dan sosai abin ya bata tsoro musamman ƙarar da taji Hansa'u ta sanya, itama haka suka gama abinda suke suka bi lafiyar gado, bacci ɓarawo ne ya sace ta.
Chapter 5 · 0% Book details