← Book details Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KuÉ—i ya bawa Auntyn shi yace a sayo ma Babarshi kayan da zata sa ita da Babanshi ranar aurenshi, aikuwa sun jidaÉ—i ba abinda suke samasa inba albarka ba, daga bisani yayi musu sallama ya fita.

Yau duk wani abu wanda ya rage sai da ya kammalashi na aurenshi har kayan da zai sakawa sai da ya saye ya kai É—inki, sauran kuÉ—i ya kai ajiya saboda idan Amarya tazo yasamu abinda zasu kashe.

Bayan ya kammala sannan yaje wajan abokinshi yace dan Allah sutafi wajan mai gidanshi mashin yake so abashi yana acaɓa.

Haka kuwa akayi suka je mai gidan abokinshi yace yaje gobe za'a bashi mashin amma fah shekara É—aya ne zai gama, sosai yaji daÉ—i yayi masa godiya sannan ya koma gida wajan Mumy ya shaida mata gobe za'a bashi mashi.

===================

Babu ɓata lokaci Hauwa ta isa wajan da aka shaida mata Ahmad na can, koda taji ta sameshi, yana ganinta yayi murmushi yace,

" Rai kanga rai, tun ranar bansake ganinki ba?".

Murmushi Hauwa tayi tace,

" Koni bansake ganinka ba , ko yanzu hanya ce ta haÉ—a mu, saboda har zan wuce na ganka zaune shine nace bari na zo mu gaisa".

Murmushin jin daÉ—i yayi yace,

" Gaskiya kin kyauta kuma nagode".

" Bawani ka gode zo karakani wallahi daman ina ta tunanin yadda zanyi tafiya ni kaÉ—an, hala ina Hajiyar ka ta barka kai kaÉ—ai?".

Hauwa tafaɗi haka haɗi da ruƙo hannusa suka fara tafiya.

" Wallahi yau biki garesu, ai jina nake duk ba daÉ—i".

" Ayya ai tunda kasaba kullum kana jikinta dole kaji ba daÉ—i".

Ta faÉ—i haka dai-dai lokacin da suka tsayar da mai napep.

Shiga sukayi basu tsaya ko ina ba sai unguwar da ta kama hayar É—aki, kai tsaye É—akin ta buÉ—e suka shiga sai wani rangwaÉ—a take mishi, shiko sai kallonta yake yana murmushi birgewa.

Lemo ta kawo masa mai sanyi ta aje gabansa, zama tayi kusa dashi kamar ta mayar dashi ciki sosai Hauwa ta birgeshi dan yanzu shima yasan sirrin gari, gwara ya tsaya ya kwashi gara, suna ciki haka Hauwa sai daÉ—i takeji tarkonta yayi, wayarshi ta fara rura, kin É—auka yayi saboda ya shagala sai wasa suke shida Hauwa.

Sai da aka saki kira sannan yayi ƙarfin halin ɗauka, koshi dayaga sunan Mamarshi ya bayyana.

Tun baiyi magana ba Mamarshi tace,

" Duk inda kake kazo wallahi ance ga mahaifinka can rai hannun Allah, dan Allah Ahmad kaje ko dan albarkar haihuwar dana maka".

Ta kai ƙarshin zanci da fashewa da kuka.

Bai ce da ita komai ba ya tsinki wayar kana ya dube Hauwa yace,

" Bari naje na dawo?".

" Ina zaka tafi?".
TafaÉ—i haka tare da zare ido.

"Wallahi mahaifina ne ba lafiya shine zanje".

" Ayya to in ba damuwa ko zamu iya zuwa tare".

Yace muje bawata damuwa........

*COMMEN AND SHARE*

*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*

*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*

*SHAFI NA 19*

Har Hauwa zata ɓuda baki ta yi magana sai Inna tace

" karki kuskura ki gayawa mijina magana ai ko ba komai ubanki ne".

Abinda ke damunta ne yasa ta kyalesu ta fara É—aukar kaya tana kaiwa É—akin da yace, sai da ta kammala sannan lnna tashi É—akin haÉ—i da zama gyafin katifa, kallonta Hauwa tayi idonta taf da hawaye tace,

" Kaicona lnna! lnna bakimin zaɓin uba ba wanda zan nunawa duniya nace shine ubana, kisana yau ina cikin ƙunci da ta kaicin kasancewa ta ƴa ga Babana, ashe lnna Baba na da ɗa Ahamd shine baki taɓa gaya min ba?".

Kallonta lnna tayi ciki da mamakin ta tace,

" Wani Ahamd kuma? ni dai nasan tunda mahaifinki ya sakeni bansanshi da wani É—a ko Æ´a ba wadda akace yau ya aure ya haifa, sai dai idan na matan da yake tare da sune, to wani abu ne ya faru?".

" Barshi kawai lnna bazaki gane ba, danshi ake so mutum yasan wanda zai aura".
Ta faÉ—i haka lokacin da take tashi ta bar É—akin.

Tana fita dai-dai lokacin da ake shigo da kayan amaryar Alhaji Abu mata sai kuÉ—a suke, tsaki Hauwa tayi kana ta dube matanshi da Æ´aÆ´anshi dake tsakar gida kowa na sabgar gabanta tace,

" An daiyi asara, ni banyi dacin uba ba wasu basuyi dacin uba da miji ba".

Tana faɗin haka tasa ƙafa ta bar gidan saboda taje ta samu mafita.

Sosai hankalinshi ya tashi ganin Hauwa ta tafi kodan halin da taga mahaifin shine, wata ƙila haka ne, amma har ga Allah Hauwa tashiga ranshi dan shi yanzu burinshi bai wuce yaganshi tari da ita sona shan soyayya ba, amma gaskiya Mamarshi bata kyauta ba, da yanzu yana can yana hutawa da Hauwarshi mai kayan ni'ima, yajima tsaye yana tunanin yadda zaiga Hauwa sannan ya samu wasu almajirai manya ya gaya musu aikin da za suyi musu sannan ya dawo wajan mahaifinshi, gyaran jiki da ɗaki akayi haɗi da sanya turare aka sauya mishi ɗaki sannan ya biya su suka tafi.

Bayan ya bashi fura yasha ne yasamu ya buɗe baki da ƙar yace,

" Amadu ina Hauwa'u, ba yanzu nagan ku tare ba, amma gaskiya naji daÉ—i da kuka san juna".

Kallon Baban Ahamd yayi tsaf sannan yace,

" Baba daman kasanta ne?".

Murmushi yayi irin na Æ´an duniya yace,

" Kamar ya nasanta Ahamad, na haifita sannan kace na san ta"......." mikace Baba!".

" Nace nasan wannan aikin iyayenku ne suka haɗa ku, ko dai kun je gidan lya gaishta ta haɗaku, dan haka kasani baka da ƴar uwa kamar Hauwa, duk nine na haifeku , amma kuyi haƙuri da yadda rayuwa tazo".

Jikin Ahamd ne ya É—au karkarwa kana yace,

" Kana nufin Hauwa Yaya tace?".

" Eh wallahi hala kai ka ɗauka kaine yaya, saboda ka ganta da ƙaramin jiki ko, kai ko ka biyoni da Babban jiki".

" Nashiga uku, amma Baba kacutar damu dan wallah a halin yanzu Hauwa budurwa tace!!.

Da ƙafi uban ya tashi zaune abinda yajima baiyi ba, kullum yana kwance saboda ya kasa koda tankwashi ƙafar bare asa ran zai iya mutsi yau shine ya tashi zaune saboda razana.

A hankali yake taka ƙafarshi har ya isa parlour da yake tunanin zai sami mahaifiyar tashi, zaune take tama kallon labarai tayi kyau abinta da ka ganinta ba abinda ke damunta.

Da sallama yashigo, karɓa masa tayi batare da ta ɗago ta kalleshi ba, wanja ƙafarta yazo ya zauna sannan ya gaisheta haɗi da jingina kansa a ƙafarta.

Yajima ahaka amma bai ji tayi masa abinda take masa ba, wato tasanya hannuta akansa tana ya mutsar masa suman kanshi, haka take masa tun yana yaro shiyasa yake son tayi mishi haka.

Dubanta ya yi har ya buÉ—a baki yayi magana sai yaji muryar Dady na faÉ—in,

ÆŠan Hajiya saukar yaushe?".

" Duk da yanzu ka girma shiyasa naga ko tafiya zakayi babu dole kasanar damu".

Murmushi yayi haɗi da basu haƙuri yace tafiyarce ta zo a bazata, sai Dady yace to muma yau zamuyi maka baza ta, dan tabbas ƙarshin watannan zamu ɗaura maka aure da wadda duk wadda muka ga dama, amma idan kaga mu bamu isa da kai ba kaje kagayawa Hajiyar da ke goya maka baya.

Har ya buɗe baki yayi magana sai Dady yace bana son jin komai daga gareka nariga na gama magana sai ka farashirin karɓar amarya kai da abokanka da ƴan matan ka.

Dady na gama faÉ—ar haka suka barmishi parlour kanshi sai juya masa yake.

Yau saura kwana biyar a ɗaura aure Kabir da amaryarshi Nana, kuma a yau ne Kabir yake so ya gayawa Mumy zaiyi aure, danshi koda gari ya waye ba inda yaje, duk abinda take son shi yake yimata, sai kwasar soyayyya suke ta mutunci, ita ko Mumy sai kafa-kafa take kar tayi abinda zai ɓata mishi rai, ranar gida ya wuni har dare, bayan sunci abinci sunyi wanka, dan yau ko wanka tare sukayi , har man shafawa shi ya shafa mata haɗi da sanya mata kayan bacci waɗanda ranshi ke so, kallonta yayi ciki da nuna mata tsantsar so yace,

" Baby wallahi sonki ko da yaushe ƙara ruruwa yake a zuciya na, dan Allah ki taimaka min kici gaba da zama dani kada ki barni, duk da a halin yanzu ni mai laifine a gareki".

Bata ce dashi koma ba ta haÉ—a bakinshi da nata waje É—aya suna kissing É—in juna, sai da sukayi son ransu sannan tace,

" Baby duk yadda kake sona ni nasan nafika sau dubu wallahi soyayayarka zata illatani dan Allah kar ka barni, burina a koda yaushe naganin tare da kai".

" Muna tare masoyiya ta, ba wanda ya isa ya rabamu ko anƙi ko ansu dole abarmu, amma ina so ki fahince ni, wallahi nima badan son raina haka zata faru ba, kiyi haƙuri kinji, saboda Mumy ce ta haɗa ni da ɗiyar abokiyar ta, wai ita yarinyar ce ta ganni wai ba wanda take so sai ni, duk wanda yafito tace sai ni, shine su Baba suka ce tunda yarinya tace ni take so nayi haƙuri ayi aure, tun kafin na buɗa baki sai Mamarta tace komai ta ɗauke min har sadaki itace zatayi komai, burinta kawai na aure yarinyar, shine Baba yace to tunda haka ne ranar alhamis za'a ɗaura aure".......wata ƙarace Mumy ta sanya wadda gidan gabaki ɗaya sai da ya amsa.....

*SUMMY M NA'IGGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

*SHAFI NA 18*

Tashi sukayi kai suka fita, É—aki ta rufe kana suka kama hanya zuwa dubin Baban Ahamad, mai napep suka tsayar Ahamad ya gaya mishi sunan unguwar da zai kai su, tana jin sunan unguwar tace itama idan sun gama dubiyar Babanshi itama su zo aduba Babanta, yace da ita ai ba damuwa Allah ya basu lafiya.

Dai-dai ƙofar gidan mahaifinta yace mai napep ya tsaya, kallonshi tayi sosai amma ta kasa buɗa baki tayi magana.

Bayan sun sallami mai napep suka kama hanyar shiga gidan, gabanta ne yayi mummunar faÉ—uwa lokaci É—aya wani jiri ya fara É—i barta.
Chapter 12 · 0% Book details