← Book details Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 13

Sashe 13

Mijin Babata Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FaÉ—uwa ta tafi tayi Ahmad da sauri ya rungumota haÉ—i dayi mata sannu, kallonshi ta farayi amma ta kasa magana har suka shiga É—akin da yake kwance sai wari yake saboda yayi kashi kuma anrasa mai kula dashi.

A wannan lokaci Ahmad ne ya rufe hancinsa, ita ko saboda shiga ruÉ—ani ko warin É—akin bata jiba, a hankali ta buÉ—a baki tace,

" Ahmad shine ma haifinka?".

Bai ce da ita komai ba ya riƙo hannuta yafito waje kana yace,

" Kiyi haƙuri Baby nazo dake wannan wajan ko?".. ...tsawa ta daka masa tace,

" Tambayarka nayi kabani amsa?".

" Eh shine Hauwa, nasan bai dace yazama ubana ba ko, kiyi haƙuri nima bana jinshi a matsayen uba".

Hannu Hauwa ta É—aura saman kai kana tace,

" Shikenan tawa ta ƙare!.

Ta faÉ—i haka hawaye na zuba a idonta.

Da sauri ta bar wajan cikin tafiyar gudu-gudu sauri-sauri.

Ahamd na ganin haka shima ya fara sauri yana kiran sunanta amma ko wagowa batayi ba bare yasa ran zata karɓa.

Yana ciki sauri dumin ya kamota sai ga mai napep ta tsayar shiga tayi haÉ—i da faÉ—a masa inda zai kaita tace yayi sauri.

Dai-dai ƙofar gidansu aka sauke ta, kuɗi ta bashi batare da ta karɓi canji ba tashiga gida hankali tashe.

Tun a soron gida ta fara jin hayaniya natashi haÉ—i da jin sautin kukan Babarta, cikin azama ta faÉ—a gidan kamar walkiya, abinda idonta yaganine yasa tayi tsayuwar daba tashirya ba.

Kayan ɗakin Babarta ne aki fitar wa waje ga Alhaji Abu na tsaye yana faɗin wallahi in har bazaki zauna wancan ɗaki ba wallahi sai dai ki bar gidannan da tabbas ba wanda ya isa ya hanani aure......tun bai kai ƙarshin zanci ba Hauwa tayi dirar mikiya kansa tace,

" Aure ? da wace abu zakayi aure? wace kaddararrace zata aureka?".

" Uwaeki ce kaddarra ita da ta aure tsohon É—an tashi irin ubanki".

Ido da hanci Hauwa ta saki tana kallon Alhaji Abu, a hankali ta furta mike shirin faruwa dani ne!.

Bayan su Mumy sun sauka gida É—aki É—aya aka warewa Hansa'u akace shine É—akin ta, kuma idan bai mata ba za'a sauya mata É—aki, godiya tayi harda kukanta saboda wannan kularce bata samu ba a wajan Babarta.

Kwanan shi biyar garin abuja sannan ya dawo gida, kai tsaye part É—inshi yashiga, wanka yayi sannan ya nemi waje ya kwanta dan ko iyayenshi basu san ya dawo ba bare abokanshi, sam ya manta da wata yarinya gaba kiÉ—aya ya manta da ita bare yace yaje gidan hutawarshi.

Baccinshi yayi mai isarshi sannan ya tashi yayi wanka kana yayi sallah sannan ya fito dan ya gsishe da Mumyn shi.

Abdulrazak kenan yaro kyakyawa ga kuÉ—i ga aji.

Koda gari ya waye ya je karɓar mashin akace ba'a kawo ba sai sati mai zuwa, dan haka yazo ya shaidawa Mumy halin da ake ciki da ta tambayeshi ba kasuwa yaje saya ba, sai yace akwai wanda yayarda dashi kuma shi mutmin yasan mashin mai kyau shiyasa ya bashi yaje legos ya sayo masa.

Sai Mumy tace ai tunda ga kuÉ—i isasu da kasaye abunka anan yafi tsayawa jiran aje logos, yanzu da hanya ba kyau.....har ta buÉ—a baki tayi magana ya daka mata tsawa yace,

" Badan kin bani kuɗi bane zaki tsareni da faɗa, idan kuɗin ki kike so sai a mayar miki ai ba dole, kuma ba roƙonki nayi ba ke kikayi ra'ayi ki bani, sannan zaki zo ki tsareni da maganar banza".

Jiki a sanyaye Mumy tazo ta faÉ—a jikinshi tana faÉ—in,

" Dan Allah Baby kayi haƙuri wallahi ni ba haka nake nufi ba dan Allah Baby".

Ta faÉ—i haka kamar tayi kuka.

Tsaki ya jamata haÉ—i da tunkuÉ—eta daga jikinshi ya tashi ya shirya yafice gida.

To tundaga lokacin ya sauya ma Mumy, idan ya fita gida baya dawowa sai ƙarfe ɗaya na dare idan kuma gari ya waye tun ƙarfe bakwai na safe yafice kuma sai ƙarfe ɗayan dare, Mumy tayi kuka har ta zuba masa ido, shiko duk ba komai ke riƙeshi ba sai hidimar bikinshi......

Commen and share.

*SUMMY M NAIGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*

*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*

*SHAFI NA 20*

Haɗe yayi a jikinshi haɗi da buga bayanta, sosai ya kijin yadda take sauke zuciyar, haƙuri ya fara bata kana yace,

" Kinsan Allah duk son da nake miki da kinyi min haukar nan da mata keyi wallahi zaki sha mamaki dan wallah zan baki horo wanda bakiyi tunani ba, shawara nake baki gara ki natso ayi komai cikin kwanciyar hankali".

Yana faɗar haka ya sauke ta daga jikinshi cikin nuna ɓacin rai

Tana ganin haka ta tashi jikina na karkarwa tace,

" Baby karka damu wallahi na ɗau alƙawri bazanyi tashin hankali ba, amma kasan dai dole nayi kishi akanka ko?".

" Naji".
Haka yace da ita a taƙaice.

Fuska haÉ—e ya tashi ya shirya ya bar gidan ko beark bai tsaya yayi ba, ba yadda batayi ba yace a'a akwai inda zai je.

Badan taso ba haka yashirya ya bar gida.

Tunani ta fara tayaya za ta karɓo mijinta dan itakam tabbas bata son ya barta, sosai take sonshi , dan haka dole tayi haƙuri ta nuna kamar ba komai ba ne.

Tundaga ranar bai sake zama gidaba kullum yana can shida abokanshi da ƴan uwanshi ana shiri-shirin aure, ana gobe ɗauren aure shine bai shigo gida ba sai ƙarfe biyu saura na dare.

Har wannnan lokacin zaune take sai tunani take haɗi da tunanin Hansa'u shikenan tunda ta koma gidan kakarta ta barta ko, to ko ita bazata nemeta ba, taje can wajan dangin ubanta ta zauna, tana cikin haka yashigo tashi tayi ta tarɓoshi, abinci ta kawo masa amma yace ya ƙoshi, wanka yayi ya kwanta batare da ya kalleta ba, taso susha soyayya ta bankwana, dan tasan ita dashi sai bayan kwana biyu amma yace shi yagaji ko ruwan jiki bashi da yanzu dan haka ta saurara masa .

Tashi yayi daga kwanciyar ya kai dubanshi gareta yace,

" Saboda kina baƙin ciki zanyi aure shine baki je komai na biki ba bare kije kiyiwa iyayena Allah ya sanya alhairi ko?".

"A'a daman nace bari sai gobe sai naje da safe inyaso sai dare zan dawo".

Tsaki yaje ya koma ya kwanta ya barta zaune tana ta gumi, ahaka bacci yayi auwon gaba da ita.

***********

Hanyar da suka bi ya bi da kallo yana tunanin maganar da iyayenshi suka faɗar masa, to miyayi zafi haka da zasu yanke masa wannan huƙunci, ko wani abu aka zo akace yayi?.

Ahankali take taka ƙafarta cikin shigar da tayi riga da sikt na atamfa, sosai tayi kyau, kwanan biyu da tayi gidan har haskinta ya fito ta kuma wata ƴar lokota sosai tayi kyau ba kaɗan ba, mutsin da yaji ne yasa shi ɗaga ido a tunaninshi Mumy ce ta dawo, idonshi ne ya faɗa kan fuskar ta, lokaci ɗaya ya mike tsaye sai yanzu ya fara tunan yarinyar da yarufe gidanshi, bata kula dashi ba har ta ɗau abinda zata ɗauka ta koma ɗaki, ido ya kifa mata har ya daina ganinta sannan ya fita cikin tashin hankali.

Kai tsaye mota yashiga ya fige ta bai tsaya ko ina ba sai gidanshi, Baba mai gida tunda ya buɗe masa get yake ta gaisheshi amma ko kallonshi baiyi ba bare yasa ran zai karɓa masa, bedroom ɗinsa yashiga wayam yagani bai ganta ba, gabanshi ne yayi masifar faɗuwa, lokaci ɗaya ya ƙara tuna yarinyar da yagani gidan iyayenshi.

Cikin zafin nama yafita zuwa wajan mai gadi, ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya tambayeshi waya shigo gidannan da baya nan? kai tsaye mai gida yace ba wanda yashigo, wuyan Baba mai gida ya cinkomu ya matse haÉ—i da zari ido yace,

" Wallahi ko ka gaya min ko yanzu nayi maka yankan rago wajannan".

Irin yadda yaga idonshi sun sauya sun koma kalar ja lokaci É—aya yasa Baba mai gida cikin rawar É—ari yace,

" Alhaji ne yazo shida Hajiya suka.....kasa ƙarasawa yayi......tsawa ya daga masa yace,

" Suka yi me!".

Hanyar bedroom É—insa ya nuna masa da hannu yace,

" Suka shiga".

Hannu ya É—aga zai wanke tsohon mutane da mari, kuma miya tuna sai ya fasa.

Tunkuɗe shi yayi sai da ya faɗi ƙasa kana yashiga mota ranshi a matuƙar ɓace, to waya gayawa Dady da Mumy ya kawo wata gidan? tabbas in ba abokansa ba to wannan tsohon mai gadi, dan yasan suna shiri da Dady kuma asali ma Dady ya kawoshi gidan dan yayi masa gadi.

Kai tsaye gidan iyayen nashi ya koma.
==========
Hawaye ne suka fara zubar masa kana ya dube Ahamd baki na rawa yace,

" Amma ba abinda ya haÉ—aku da Yayar taka ko?".

Ya faÉ—i haka a É—an tsorace.

Ahamd bai samu damar buÉ—a bakinsa ba ya fito É—akin da Baban nasu yaki ciki da tashin hankali, kai tsaye gidan Babarshi ya isa, koda yaje tana É—aki ita da mijinta.

Ko sallama baiyi ba ya faÉ—a É—akin, da sauri ta tashi tasaka hijab É—inta haÉ—i da rufe mijin nata da zanin gado kana tace,

" Ahmad wai yaushe ka lalace! ashe zaka iya shigowa É—akin nan batare da neman izini ba, kasan halin da zaka tarar damu? ai ko ba komai yana da kyau kayi sallama"......hannu ya É—aga mata yace,

" Ni bashi nazo ji ba, yau ina so ki sanar dani waye mahaifina, kuma ya muke da wancan dakike cewa shine mahaifina".

Hannu ta É—aura akai tace,

Yau minake shirin ji ko gani, Ahmad yau ni zaka zo kacewa haka!?".

Ta kai ƙarshin zanci tana kuka.....

*Comment and share*

*SUMMY M NA'IGE✍️*
Chapter 13 · 0% Book details