← Book details Matar Lameer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Matar Lameer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abune ya caki zuciyar Lameer amma sai ya dake ya miqa masa hannu suka gaisa yace “Mal Garba gurinka mukazo" shafa kansa yayi yace “to ai gani" kallon Jiddoh Lameer yayi yace “tashi kije ki jirani jikin mota"
Sumsumsum ta miqe ta koma jikin motar tana ganinsu suna magana an yamutsa hazo sosai kafin haqan Lameer ya cimma ruwa sannan suka taso tare da Ardo Garbati Lameer ya kalli Hauwah yayi Mata murmushi ya bude mota ya dauko dumbujen kudi da shi kansa baisan nawa bane ya bawa Ardo Garbati yasa hannu ya karba da sauri yayi dariya yace “dama Kaine ka dace da ita Allah ya baka Jiddoh yarinya kyakkyawa me zamani".…………

*UMMUH HAIRAN CE...✍️*
[7/2, 6:48 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *M.L*
_____________________________
*22*
_____________________________

____________📝Kama hannunta yayi yasata a mota ya shiga yaja suka tafi tanata zuba masa hira bata ankara da cewa sun fito daga garin ba saida taga sun dauki kwalta sosai sannan tayi shiru cikinta ya fara qugi ganin tafiya taqi qarewa yasata dago manyan fararen idanunta tace.
“Kado Ina zaka kaini nan hanyar inane?" Shiru yayi Mata baice Mata qala ba saima wani kallo da yayi Mata yayi ya kawar dakai.
Tafiya sai miqawa takeyi Jiddoh na qara tsurewa ganin sun yanke sun fita daga yankinsu yasata Dora hannu aka zata zunduma ihu yayi saurin kallonta tare da Dora hannunsa akan  bakinsa yace.

“Shitttt" dole ta hadiye kukanta ta rinqa jan zuciya tana rawar jiki saboda tsoro tariga ta ta saddaqar yau angama cinikin kanta dama Baffa yasha fada mata kanta zaiyi tsada.
Qwallah takeyi tana sharewa saboda gudun kada ya qara daka mata tsawa irinta dazun, batasan inda sukazo ba saida taji yayi horn ta dago firgigit kamar me bacci ta zubawa qofar ido cikinta na qara yawan kukan da yakeyi yana wani qulululuuuuu.
Juyowa yayi ya kalleta yayi murmushi yanda yaga alamun tsoro a fuskarta yayi bala'in qayatar dashi yace “gobe zaa yanka kannan naki jibi asha dabge"

Ai kafin ya gama mgnr ta fara kuka tana mammatse cinya saboda tsoron kada ta sakar masa fitsari a mota, Jan motar yayi da mugun gudu ya shiga cikin gdan gonar da gabaki daya dogayan bishiyun turare ne suka kewaye ko Ina na sai mangoro da gwaiba da zaitun gefe kuma dashen bishiyun zogale ne da auduga.
Bude qofar yayi ya fito itama ya bude Mata a zummar ta fito amma Ina ta tafi duniyar tsoro jikinta sai kyarma yakeyi, hannu yasa ya tabata yace “sauri nakeyi fito muje na kaiki inda zaki zauna kafin na dawo"

Kuka ta rushe masa dashi ta fado daga motar ta riqe qafarsa tace “don Allah Kado kayimin rai mutuwa mutuwa wayyohhhh mutuwa idan aka yankani a cinye naman jikina dama ance ku yan birni cinye naman mutane kukeyi shikenan Baffa shikenan Gwaggo......"
Dagata yayi cak yayi mata daukar jarirai ya nufi wata yar siririyar hanya da ita ya tura qofar ya shiga ya mayar ya rufe ya direta a saman kujera ya zauna a kusa da ita ya dago kanta yace “bakyaso nasa a yankamin ke?" Saurin daga kai tayi ya hadiye dariyarsa yace “ok tashi ki shiga dakin can kiyi wanka akwai kayan tsarabar da nazo miki dasu a mota zan kawo miki kisa idan kin fito kuma kici abinci kafin na dawo idan kikaqi ci aradun Allah sai nasa anyi gunduwa gunduwa dake da fatan kin gane?"

Saurin daga masa kai tayi ya miqe ya kama hannunta yace “ok muje na nuna miki bathroom din" miqar da ita yayi ya kama hannunta ya bude wani daki ya shiga tana rakube a bakin qofar har yakai bakin bathroom din yana Mata bayanin komai ya juyo yaganta tana mutsuniya a cikin labulen ta kasa budeshi wai ta shigo.🤣
Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yace “meyene kikeyi anan?" Shassheqar kukanta ta qara ya girgiza kai ya qaraso ya bude Mata tare da janyo hannunta yace “na fada miki banson kuka fah ko?"

Daga masa kai tayi yace “ok oya aje ayi wanka idan na dawo insha Allah komai ya daidaita da kaina zan wanke miki gashin nan" ajiyar zuciya ta sauke taja baya ta riqe qugu tace “cabdi kaji wani iskaro kuma kawai sai ka kama kaina ka wankemin aa yaseen nikam bazaayi iskancin nan daniba kuma ma aradu bazaka tafi ka barni a gdan yankan kaiba saidai mu tafi tare idan ba hakaba nayi arwala na hau ksn buzu nayi maka addu'a idan ka fita karka dawo ka makance ka kasa gane hanya"

Tunda ta fara mgnr ya qura Mata ido yana kallonta har saida tasa aya yaja numfashi yace “to je kiyi ina jirankin" neman guri tayi ta zauna tace “ni yar iskace da zanyi wanka dagani saikai a gdan salon ka rinqa leqoni..."
Dariya yakeso yayi amma takaici ya hanashi dariyar sai daga wayarsa da yayi yace “eh nayiwa Baba Mai unguwa magana yace zaayi abinda ya dace yanzu nasan hisba sunje nima yanzu nake shirin komawa"

Kashe wayar yayi ya fita tabisa da sauri tana kiransa ko juyowa baiyi ba ya fice da sauri ya kulle qofar yaja motarsa ya fice ta zube a gurin tana shure² tana kuka tana jijjiga qofar Amma ta kasa budeshi hakanan ta miqe ta koma can gefe ta rakube tanata kukanta tana Kiran Baffa Gwaggo Inna Jumme.🤣
Kuka tayi sosai tare da kifa kanta a kujera a haka har bacci ya kwasheta itadai batasan meye ya faruba Jiddoh anji baqon guri A.C na ratsata sai juyi takeyi harta bingire a qasa tanata baccinta.

__________Yana fita a kwanar komawa garin yaci karo da motar Hukumar Hisbah tana fitowa daga lungun yayi parking Suma sukayi suka gaisa ya tambayesu ya akayi nan fa suka fara bashi lbr wani cikinsu yace “Ai ranka ya dade munsha fama da tsohon nan taurin kaine dashi saida mukayi dan qaramin yaqi don cewa yayi babu ubanda zai hanashi daurawa yarsa aure da  Barau dan jaji a cewarsa daya baka aure gara ya kashe yar tasa, duk wani bayani da kake tunanin zamuyi masa munyi masa qarshe saida muka gwada masa qarfi muka kirawo abokan aikinmu police wlh yana daura auren yana kuka wai an shusheshi an qwace masa yarsa zaa siyar da it's a birni, hmm waifa bayan angama mun qirga sadakin mun bashi munce ya riqe cewa yayi shi Allah ya tsareshi riqewa kuma itama yar ya sallamata tunda ance kaine ka saceta ka gudu da ita"

Ajiyar zuciya yayi cikin sanyin jiki yace “alhmdllh na gode sosai Allah yabar zumunci na gode sosai" komawa motar yayi ya dauko wani envelope ya suka karba sukayi masa gdy tare da qara jaddada masa cewa Ardo yace indai yaganshi ko yaga Jiddoh a saiya radesu da sanda.
Murmushi yayi yace “karku damu komai zaizo da sauqi insha Allahu burina kawai tseratar da yarinyar daga fadawa muguwar rayuwar da jahilci yake neman jefata insha Allahu zanyi qoqarin daidaita tsakaninta da iyayenta a lkcn da suka fahimci wacece ita suka gane kurensu na baya"

Juyawa sukayi suka nufi gdan daya killaceta suka shiga yanata washe baki kamar anyi masa busharar rahamar ubangiji.
Bude qofar sukayi suka shiga harda Amininsa Salees tare da sallama tana kwance tanata sharar baccinta, ya matsa gabanta ya tsugunna ya sanya hanunsa ya shafa fuskarta kasancewar batada nauyin bacci tayi miqa tare da banqarewa tana salati yayi saurin qara rufeta saboda riqarsu ce ta fulani iya cibiya a jikinta hatta cibiyarta a waje take.
Bude idonta tayi ta kalleshi Salees yace “Captain zamu iya tafiya tunda mun gama aikinmu? Ai bata jira yabada amsaba ta zabura zata miqe ya fincikota jikinsa kasancewar bazai iya bari aganta a haka ba yace “ke meye hakan ki nutsu kefa matar aure ce....." Wata bangaza tayi masa ta miqe kamar walqiya ta tsalllakeshi ta shige dakin ta kulle, ba Salees ba hatta yan hisbar saida abin ya basu dariya Salees yace “sunan wani littafi wai mijin qwaila kai yanzu duk izzarka akan mace wannan qaramar alhakin ce ta ruda duniyarka?"

Miqewa yayi yace “wlh itace har nakejin kamar bazan iya rayuwa ba in babu ita Salees cikin wata uku son Hauwah ya haukata duniyata ni yanzu banmasan ya zanyi da itaba shegen tsokana ta yasa nace gidan yankan kai na kawota"
Dariya sukayi sukace “haka zaka sauko ka zama daidai da ita ka rinqa yimata mu'amala irin ta shekarunta saiku daidaita kassan yaro abokin yaro ne"
Miqewa yayi yaje bakin qofar ya murda ya shiga tana zaune nata kuka tana juya kai hatta kallabin data daure kanta ta cire ya matsa gabanta tanajin dumin jikinsa ta zabura ta miqe tayi baya a guje tana girgiza masa kai cikin sarkewar murya ta wanda yayi kuka ya gaji tace “nidai kada kabasu ni su yankani yanzu idan na mutu na dena ganinka na daina ganin Baffa na daina ganin Gwaggo na daina ganin Inna Jumme har Lamunde na daina gani"............

*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[7/2, 11:16 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *M.L*
_____________________________
*23*
_____________________________
_*BY*_
*UMMUH HAIRAN*
_____________________________

Ajiyar zuciya yaja ya miqe ya matsa gabanta yace “ki nutsu kizo kiyi sallama dasu abokai nane tafiya zasuyi"
Noqe kafada tayi tare da qarayin baya yayi murmushin takaici yace “kedai bazaki daina shirme ba" juyawa yayi ya fita ta sake zama tana kukanta tana Kiran “wayyohhhh Gwaggota ya saceni barawon mutane ne Kado aradu bazan qara yarda na shiga motarka ba tunda kai azzalumi ne....."😂

Turo qofar da yayi ya shigo da kayan abinci a hannunsa shine yasata qara miqewa ta tattare zaninta ta tura tsakanin cinyoyinta zuciyarta tana bugawa da qarfi saboda mugun tsoronsa da takeji.
Ajiye kayan yayi ya nufeta ta janye ya qara nufarta ta janye ya tsaya yana kallonta yace.
“Dagani saike zamu kwana a gidannan idan kika wahalar dani nima zan wahalar dake" yana fadin haka ya janyota ya mannata da jikinsa.
Chapter 11 · 0% Book details