← Book details Matar Lameer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Matar Lameer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin hankalin da bata taba shigaba taji ta shiga batasan sanda tayi jifa da wayar ba tace “Hauwah kuma wace Hauwah Muneef?" Cikin nuna rashin damuwa yace “bafulatanar karuwarsa mana kinga hakan ya isa ya tabbatar miki bakya gabansa itace a qasan qalbinsa ko yarku bai tambaya ba Hauwah yake tambaya gsky matarnan kina ruwa har saman goshi"
Miqewa tayi ta shiga safa da marwa tanajin wani tuquqin baqin ciki yana taso mata “komawa tayi ta rushe da kuka tace “Muneef akwai matsala aure Lameer zaiyi amma Hajiya ta munafurceni bata fadamin ba saboda ba ita ta haifeni ba ashe soyayyar da take nunamin ta banza ce hqrn da take cewa nayi duk naa cuceni ne ina bazai taba yuwuwa ba Muneef dole asan abinyi idan yayi auren nan asirinmu tonuwa zaiyi...."

Rufe mata baki yayi yana murmushin gidan boss yace “saidai naki ya tonu amma ina tabbatar miki ni nawa a rufe yake kuma murna zanyi idan kin tafi gantalun bin mazanki shi kuma ya tafi nemomin kudi ni inada wata a gdan zanzo kota qarfi nayi ban ruwa"
Yana gama fada mata haka ya miqe ya sake cafkota kafin tace zata kwaci kanta ya fara caccakarta babu yanda zatayi haka ta biye masa sukayi aikinsu suka gama.
Sukayi wanka ya dauketa a mota saboda cewar da tayi zataje taga Hajiya, har harabar gdan suka shiga yayi parking ta fito shima ya fito suka jera kamar shine mijin suka shigo ciki Hajiya na ganin haka ta daure fuska don batason shigewa junan da sukeyi gudun abin Allah wadarai saboda sarai tasan halin Muneef yanzu ma fama takeyi dashi akan neman Mata.

Zama sukayi yace “bansan meye yasa Hajiya bakya sona ba babu dama ki ganni da matar Yaya sai kin kawo wani Abu a ranki an fada miki ni Dan akuya ne da yayana zaiyi fito nima nayi haba haba Hajiya meyesa kika gurbata tunaninki akaina ne?"
Shafa fuskarta tayi tace.
“Autana kai dinne rawar kanka tayi yawa nikam kafidda mace mu killace ka" dariya yayi yace “wa waini? Haba Hajiya aini saidai a auro min" bata gane me yake nufi ba ta tafi ta kama Ina ka saka Ina ka aje da Mubaraka ta cika Mata gabanta taf da kayan ciye² sannan ta zauna tace.

“Ashe kina tafe yanzu mukayi waya da ja'irin yaron nan me neman mgnr tsiya baicemin zakizo ba?" Turo baki gaba tayi tace “dama ya zaayi yace miki zanzo yayimin laifi" rushewa tayi da kuka nandanan hankalin hajiya ya tashi ta shiga sallalami tace “meye ya faru yarnan na shiga uku ni jikar me sabulu"
Karkacewa Mubaraka tayi tace “ashe Hajiya wulaqancin da Lameer yakeyimin ba banza bane ashe mace ya ajiye a duk inda yake zuwa jiya Muneef yake fadamin sunje nema masa auren wata yar fulani babanta yana cewa ya lalata masa ya da dare na kirashi muryarsa cikin wani yanayi yakw cemin Hauwah abin qasanki da dadi wlh saina aureki babu uban daya Isa ya hanani yana nishi yana cakal² dazu kuma na kirashi wata ta daga take cemin bacci yakeyi Hajiya Yaya zanyi me nayiwa Lameer yakeyimin wannan izayar....."

Ta qarasa mgnr cikin gunjin kuka na son ita sai an gasqatata, sallalami Hajiya takeyi tare da Dora hannu aka tace “naga takaina ni jikar me sabulu dama biri yayi kama da mutum ashe abinda yakeyi kenan shiyasa ya massheke TV abar adon gida kawai yanzu abinda Lameer ya koma kenan"
Shiru ce ta ratsa kafin daga bisani Hajiya tace “to yarnan kodai bakida dadine"😂 saurin dagowa sukayi tace “eh kinsan akwai abinda idan dandano bayi masa ba baya miqewa nidai naga abar Lameer da kaurinta da tsayinta to bayan ya girma ta lalace ne ko kuwa a gurinki ne qur'anin Allah kota auta batakai tashi ba balle ta yayansu dake England shikam tashi yar quininiyace"…………….

*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[7/2, 8:05 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *M.L*
_____________________________
*21*
_____________________________

___________📝Da sauri Mubaraka da Muneef suka kalli juna Muneef yace “haba Hajiya ba wannan zancen kawai dai kiyiwa danki fada yasan darajar iyalinsa kuma yasan girmansu yamayar da hankalinsa kansu ya daina leqe²"
Numfashi Hajiya ta sauke tace “shikenan ki tashi kije idan yazo zai gamu dani har ubannasa da yake daure masa gindin iskanci zaizo ya samene ba bagulatana ba ko rugace sai taci ubanta a gurina"

Miqewa Mubaraka tayi ta shige dakin Hajiya ta dauko yarta ta fito ko sallama batayiwa Hajiya ba saboda takaici itakam ta rasa wacce irin uwar miji ce da ita da indai ka kawo Mata qarar danta sai ta dawo da laifin kanka “wai ko bakya da dadine 😂”
Tana fita Muneef ya miqe ya bita daqyar ta shiga motarsa suka fantsama gari sune gurin shan ice cream da guraren shaqatawa.

Basu dawo ba sai wajen goma na dare suna zuwa suka zube a falon suka fara cin abinci bayan sun gama suka shiga wanka tare suka fito aka kira Nanny aka jorner ta da ita suka tafi dakinsu sukuma suka shige dakin Mubaraka.
Da farko taso tayi gardama amma yanda ya rinqa bi da ita yana shiga jikinta yana wani nishi yana kiran sunanta yasata miqa kai bori ya hau wadannan mutane akwai jarababbu Mubaraka haka takeso a kwana ana haqarta shikuwa Muneef dama hakan shine burinsa aikuwa aka kwana ana bawa shuka ruwa.

______________Da safe jirgin qarfe shidda Lameer ya biyo zuwa birnin dabo da farko yayi kamar yaje gda kawai sai ya wucce office ya had a reports na abinda ya kaishi Lagos yabada takardarshi ta transfer sannan yayi wanka anan ya huta.
Sha biyu ya dauki hanyar Rugar Sambajo zuciyarsa cike da nishadi zaiga farin cikinsa, saboda gudun da yakeyi tafiyar awa daya da rabi ce ta kaishi Alqalawa daga Alqalawa ya yanke burji ya nufi garinsu Jiddoh.

Nesa da gidansu yayi parking lkcn tana bayi tana wanka ta dawo daga tallan nono taji qugin motar, ta danga ta leqo taga motar cikin saa kuwa yana bude motar zai fito aikuwa tayi maza ta zari zaninta ta daura a qirjinta ta zura rigarta ta ta kama dangar ta tsalllake saboda tasan idan tace zata fita ta qofa bazaa barta ba.
Yana tsaye ya bawa gurin baya kawai yaji an masa cakulkuli ya dago da sauri suka hada ido taja da baya tare da qyalqyalewa da dariya tace.

“Na bashi tsoro Ina wanka naji tsayuwar motarka shine nayiwa su Baffa wayo na fito dama na matsu na matsu kazo ranan nan wani me kama dakai sukazo gdan nan yayita kallone nima nayita kallonsa amma fah kafishi kyau shi kodaddene kamar jan qosai"
Murmushi yayi a hankali ya sanya hannunsa ya riqo nata yace “Baffa ya yarda da mgnr aurenmu Hauwah?" Dagowa tayi tare da girgiza masa kai tace “ni bansani ba kawai dai naji yace wai gobe Ardo Garbati zai kawo shanuwar aurena....."

Rufe mata baki yayi da sauri jikinsa na bari ya jata yasata a mota shima ya shiga ya kulle ya zuge glass din yace “waye Ardo Garbati?" Kukan da take hadiyewa ne ya kwace Mata yayi saurin janyota jikinsa ta janye tace “ka kadaina tabani banaso iskanci ne"
Kada Mata kai yayi saboda ya matsu yaji waye Ardo Garbati yace “ki fadamin waye Ardo Garbati?" Cikin kuka tace “baban su qawata larai ne da Zahira da nayiwa duka karon wacca saboda sunce kai Dan iskane wai wai saboda Madi yace bazai aureni ba shine baffa yaje yace yabashi ni sadaka yabada shanuwa daya a daura aurena dashi"

Wata zabura yayi yace “kina nufin idan yabada shanuwa gobe shikenan zaa daura miki aure dashi?" Kukanta ta qarawa qarfi tace “kuma auri saki yakeyi matansa goma sha bakwai duka ya sakesu saura hudu a gdan to ya kuma sakin daya saboda zai aureni yayansa kuwa sun kusa hamsin bakaga kuma baya basu abinci kowa saidai ta nemi nata da kanta, jiyama da yazo wai yazo gurina tadi nikuwa nayi masa atule shine wai yace Allah yakai damo ga harawa wai sai yasa anyi mini dinkin qwary......"

Daga mata hannu yayi yace “ya isa jiddah muje ki rakani gurinsa" zaro ido tayi tace “kutqel tarnatsa bani zuwa Gwaggo ta hanani tace fyade yake yiwa yara" girgiza mata kai yayi yace “muje ki rakani babu me tabaki a gabana koda kuwa Baffa ne"
Dariya tayi tace “yaushe zamu tafi birni tare kasamin irin haqorin bakinka?"
Yarfa hannu yayi tare da dukan kansa yace “oh my God luv kina wahalar dani muje na gama da wancan tsohon banzan tukunna sai muyi mgnr zuwanmu birni Hauwah naga alama sai na shigo da hukuma cikin mgnr nan sannan Baffa zai bani ke"

Wani murguda masa baki tayi tace “idan suka kamamin Baffana kuma fah?" Shidai bai kuma ce Mata komai ba saboda surutunta ya fara sashi ciwon kai yaja motar zaiyi ribbers tace “aa Tasha zamuje acan yake zama matsiyaci ne shanunsa uku duk ya siyar yayi aure"
Yanda yakejan motar cikin nutsuwa yafi komai bata sha'awa tace “kado itama zaka koyamin?" Shiru yayi Mata suna tafe tanata surutun ta har sukaje tashar Alqalawa sukayi parking ya fito itama ta fita abinka da qauye duk sai suka zama abin kallo.

Fusgo hannunta yayi ta wani tsaya ita a dole sai tayi abin yan birni sai kwarkwasa takeyi yace “dallah ki ware kiyi tafiya banson shirme" yanda yayi mata tsawar yasa ta nutsu har suka isa inda Ardo Garbati yake zama suka tambaya yananan akace eh ya zagaya.
Neman guri sukayi suka zauna bayan kamar minti goma ya fito yazo zai hucce caraf idonsa ya fada cikin na Jiddoh da taketa harararsa da murguda masa baki, murmushi yayi yace “oye amaryata aradun Allah Ina son tsiwar nan taki nan da jibi ma bazakiyimin itaba gishiri ya hau kan kaza"
Chapter 10 · 0% Book details