← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bud'ar mahaifita wato Baba Auta sai ya ce" Halak take nema domin shi yana da labarin komai, saboda haka kada na sanya mata ido ko nayi mata ba'kin ciki, tunda dai ni bani 'kwakw'kwarar sana'a to babu lefi don ta nema duk rufin asirinmu ne.''

Wannan shine abinda Hajiya ta maimaita domin itama tayi goyi da bayan Fatiman.

Sai kawai na tattara na rabu dasu, amma duk sanda na dawo gida ta kawo min abinci, wanda nasan bani nayi cefenan ba, to bana ci haka zai wayi gari ta d'auka ta bawa almajirai tana surutai irin na rashin kunya.

Duk da shan 'kwayar da take hakan bai hana Allah Zartar da ikonsa ba, ciki ta samu, kuma bai tashi bayyana kansa ba sai da yayi wata hud'u a jikinta sannan ta gane cewa tana da ciki lokacin da taje asibiti likita ya tabbatar mata da watanninsa.

Halin damuwa ta shiga mai tsanani! ta daina walwala a gidan, kullum idan na dawo daga gurin aiki cikin damuwa nake samunta, har dai na gaji na tambayeta, kawai sai ta fara min rashin kunya tana k'okarin zagi na, wai ba zata sake amincewa da bu'katata ba.

Na ce" Duk me ya janyo hakan?" tana kuka ta ce" Ciki ne dani watansa hud'u harda kwanaki."

Na ce" Na gode Allah! yanzu kin tabbatar da cewa; ba a yiwa Allah wayo ko?"

Tayi shuru tana kallona, na ce" Duk abinda ki ke a gidan nan ina sane, nasan cewa kina amfani da k'wayoyin hana daukar ciki, amma na zuba miki ido kawai, saboda kin fi k'arfina Fatima, amma yanzu Ubangiji ya nuna miki cewa baki da dubara."

"Wallahi sai na zubar dashi" tafad'a tana gurshe'ken kuka! na ce" To babu lefi sai ki d'aura d'amara" tashi nayi na bata guri, domin ina kallonta zuciyata zata iya tarwatsewa saboda b'akin ciki!

Bayan kwanaki shida da faruwar al'amarin, na fita gurin aiki da kamar minti talatin, sai kawai na gilmawar mota ta wuce ta gabana. babu shakka Fatima ce a ciki domin ita d'in ba sabuwar hallita bace a gurina, sai dai wacce take tuka motar ce ban gane ba.

Hankalina ya kasa kwanciya domin ba muyi da ita cewa zata fita ba, aiki nake amma gabad'aya hankalina can wani guri.

Daf da mariba na tashi daga aiki na nufi gida domin hankalina ya kasa kwanciya, a bud'e naga gidan, sai naji nutsuwa a raina, domin na tsani yawon dare, amma duk da haka sai na tuhumeta wane guri taje d'azu!

Ina sanya 'kafa ta a d'akin na ci karo da wata leda viva! a bakin k'ofa, ban kawo komai a cikin raina ba, na shiga dakin na sameta a kwance duk tayi zuru-zuru!

Na ce" Fatima ina ki kaje d'azu?"

Shuru tayi min, sai da na sake maimaita tambayata tukkuna ta ce" Wani guri na je" na ce" Kin gaya min zaki fita ne?"

Ta girgiza kai. na ce" Ina ne wani guri? ko bashi da suna"

Zum'bura baki tayi ta ce" Ni fa bana son damuwa don Allah ka rabu dani na ji da ciwon da yake damuna"

Na ce" Billahil-lazi la'ilahaillahuwa sai kin fad'a min gurin da ki kaje, idan ba haka ba sai na ji miki ciwo a gidan nan"

Zaune ta tashi tana kallona kafin ta ce" Sai dai kuwa ka kashe ni wallahi domin zuwa nayi na zubar da wannan jarabar daka 'kunsa min, ga d'anka can a leda a bakin k'ofa!

Da saurin gaske na juya ina kallon bakin kofar, ashe abinda na ci karo dashi gudan jinina ne, jikina na rawa na kalleta da fadin" Yanzu sai da ki ka zubar da cikin nan Fatima?"

"To meye amfaninsa, ni wallahi ba zai katse min hanzari ba, domin saudia za mu tafi tare da Jamila zaman shahada"

"Innalillahi-wa'inna-ilahi rajiun! wannan adduar nayi ta nanatawa kafin na samu nutsuwa!

Na kalleta tana zaune turmin danya babu abinda ya dameta, na ce" Da izinin wa zaki tafi zaman shahada?"

"Kai nifa dama na gaji da zama da kai wallahi! dube ka, kullum jiya i yau, babu wani cigaba a tare da kai, ka dube ni da kyau kai kanka, kasan yanzu nafi 'karfinka don haka wallahi dole ka sake ni na gaji"

Na ce"Shine hujjarki na zubar min da ciki?"

"Kwarai kuwa domin ba zan tafi da nauyinka a kaina ba"

Wallahi a lokacin rasa bakin magana nayi domin duk wasu dabaru na sun 'kare, jiki a mace babu kuzari na shiga daki na dafe kaina, hawaye masu tsananin zafi suka shiga kwaranya a saman fuskata.

Koda ta shigo d'akin ta sameni ina zubar da hawaye, ko a jikinta, ina kallonta ta shirya ta kama hanya ta fita tana 'kananun maganganu, cewa ita ta gaji da zama cikin talauci, bayan ban gaza mata da komai ba.

Ashe kukan da nake shafar mai ne, domin ledar gudanan jinin da aka fara yiwa hallita ta d'auka ta nufi can gidanmu, har d'aki ta samu Mamana a kwance tana fama da kanta ta ajiye mata ledar, tare da fad'in" Gashinan an fara yi masa hallita saboda haka sai ayi masa suttura a aje a binne, ita bata shiryawa haihuwa yanzu ba, bayan haka kuma ta gaji da zama cikin talauci lallai ita a sawwa'ke mata, domin ta je ta auri daidai da ita"

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! ai tana fita daga dakin da 'yan mintina Mamana ta had'iyi zuciya ta mutu, sai gawa muka tarar! likita kuma ya tabbatar min da cewa zuciyarta ce ta buga sakamakon 'bacin ran da ta jima a ciki.

Wallahi na shiga tashin hankali da damuwa a lokacin, domin kamar zautacce haka na dawo, babu ci babu sha! na rasa ina zan tsoma rayuwata na ji sanyi, gashi a lokacin kowa ya san Fatima ce sanadin mutuwar mahaifiyata amma saboda rashin adalci suka ce a lullub'e maganar kada wasu a waje su ji abinda yake faruwa.
Amma Hajiya jikinta yayi sanyi sosai! domin kuka sosai ta dinga yi lokacin da aka fito da Mamana za a kai ta, gidanta na gaskiya sai neman afuwarta take.

Har aka share makoki Fatima bata tako k'afarta gidan ba, daga karshe ma sai samun labari nayi cewa; sun tafi saudia ita Jamila 'kawarta.

A lokacin Hajiya tayi tur! da Allah wadai da halinta, ta kuma kira Baba Auta ta rufe shi da fad'a sosai! da yake 'yar tasa ta toshe masa baki da kud'i ko gezau! bai nuna damuwarsa ba, sai ma ya ce" Shi ya gaji idan auran nan, ba zai yiwu ba to a rabu kawai domin ya gaji da sasanci." Hajiya ranta ya 'baci sosai! a take gurin ta umarce ni dana sake ta, ban jira komai ba na furta cewa na sake ta, na kuma rubuta a rubuce, na bashi sheda! bai damu ba, ya kar'ba tare da buge rigarsa ya ta tashi ya tafi ya bar mu a zaune a gurin cikin tsananin mamaki.

A tsakankanin lokacin sai da na kwanta a asibiti domin tsananin ciwon kai da ya addabe ni, jina ne ya hau sosai! sai da likitoci suka rufu a kaina da kuma taimakon Allah na samu lafiya, na dawo gida da tarin magunguna tare da kokarin cire damuwa daga cikin raina, kamar yanda likitana ya bu'kata.

Wata uku da rasuwar Mamana wani abokina da mu kayi karatu tare dashi a kano, ya kira ni a waya ce maza na zo ya samar min aiki a wani kamfani, amma nazo da takarduna.

Banyi 'kasa a gwiwa ba, na shedawa Hajiya halin da ake ciki, tayi min addu'a sosai kafin na kama hanya na tafi.

Faruk ya dafa kafad'a ta da fadin Abokina insha Allah wahalarmu ta 'kare domin
"Babban kamfanin sarrafa shinkafa ne dake unguwar harad'a suke neman injiniyoyi irinmu, wannan dalilin yasa na kira ka nace maza kazo ko Allah zai sa a dace, domin ni har na fara zuwa aiki cikin satin da ya gabata"

Na ce" Na gode sosai Faruk Allah ya 'kara zumunci" ya ce."Babu komai abokina duk yiwa kai ne.

To shi dama lamarin ubangiji ne yana faruwa ne a lokacin da ba kayi tsammani ba, kuma wani lokacin baka samun farin ciki kai tsaye sai an jarabce ka.

Kasancewar takarduna sunyi kyau sosai! yasa aka daukeni aiki, akan matsayi mai girma! da albashi mai tsoka, kuma da yake shugaban company yana da tarihin rayuwata, wallahi gida ya dauka ya bani tare da abun hawa mota sabuwa mai kyau da 'kwari!

Nayi masa addua sosai da sosai! kuma na d'auki alkawarin yin aiki cikin gaskiya da amana.

Wannan shine mafarin dawowata garin Kano da zama, tare da Hajiya na tare a sabon gidana domin tun bayan rasuwar mahaifiyata take tausaya min, wannan dalilin yasa ta ce " Duk inda nake tana gurin" Baba Auta ya dinga kishi! ya kuma kasa 'boye hassadarsa akan abun alherin dana samu.
'Bangaran Baba Audu kuwa addua yayi min sosai, wannan yasa na dauki kudi masu yawa na bashi. Sadiya ma har gidanta na je na kwantar mata da hankali, na ce duk abinda take bukata ta kira ni, a waya insha Allah zan share mata hawaye! cikin damuwa muka rabu da juna.

***
Bayan shekara biyu da fara aiki na, rayuwa ta sauya min sosai! hankalina ya kwanta domin bani da wata matsala gagarima, kullum cikin nasara nake fita aiki na kuma dawo cikin fatahi!

Rana tsaka Fatima ta kira ni a waya, nayi mamaki sosai! na d'aga wayar muka gaisa, na ce "Ina fatan lafiya?

Sai cewa tayi " Kayi hakuri da abinda ya faru"

Na ce"Shine dalilin kiran?"

Ta ce"A'a" na ce" To ina sauraranki"

Ta ce" Na samu labarin abun alherin da ya sameka Allah ya sanya alheri ya kara d'aukaka"

Na amsa da "ameen ya Allah"

Ta ce"Ka bani address din gidanka zan zo maka da wani albishir wanda zai sanya ka farin ciki."

Tsaki na ja da fadin" Baki da hankali har yanzu Fatima" sai kawai na kashe waya ta na rabu da ita, tayi ta kira ban daga ba har ta gaji ta hakura

Ina tsammanin number wayata ta bibiya har ta samu gidana.karfe takwas na dare sai ganinta mu kayi tare da wata 'karamar yarinya da bata fi shekara daya da rabi ba.
Chapter 9 · 0% Book details