← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce." Saboda me?" murmushin takaici nayi kafin na ce" Na ga gabad'aya kun d'auki lefi kun d'ora min, domin na shigo na ga Hajiya tana kuka tana sheda min cewa; damuwata ce ta haddasa ciwonka ya tashi, bayan haka kuma, a gabanka Shukura ta ja min tsaki tana min kallon banza! idan da matsala kawai ka rabu da ni, domin ni bana so shiga cikin zargi, bayan da bakinka kafad'i ga wacce ta haddasa maka ciwon tun fil-azal, amma ana neman d'ora min jakar tsaba."

"Kiyi hakuri." Wannan kalmar ya furta kafin ya rintse idonsa, alamun sun nuna baya bu'katar doguwar magana.

Na ce" Ya jikin naka?" da sauk'i ya fad'a ba tare da ya bud'e idonsa ba.

Shiru d'akin yayi na 'yan mintina kafin na ce" Yanzu me kake bu'kata?"

Bud'e idonsa yayi yana bi na da kallon mamaki!

Fuskata na saki amma ban ce komai ba.

Ya girgiza kansa tare da fad'in" Ba abinda nake bukata a gare ki, sai alfarmar ki zauna tare da ni, ki kuma cire shakku a kaina, bayan haka kuma ki ri'ke ni amana."

Jim nayi na minti biyu kafin na ce" Shikkenan zanyi 'kokarin ganin nayi hakan muddin zan fita daga zargi don bana so wani abu ya same ka mutane su ce ni ce sanadi.

Murmushi yayi, yana min wani irin kallo kafin ya ce'' Babu wanda zai zarge ki don kin taka sawun 'barawo, kin 'karasa gawar da ba taki ba, dama can bani da cikakkiyar lafiya, ko da Hajiya tayi wannan maganar, ba da wata manufa ba, tayi ne domin ki gyara kuskuranki, ma'ana ki zama mai kula da mijinki domin ki samu rabauta ranar gobe 'kiyama."

Sunkuyar da kaina nayi tare da wasa da yatsun hannuna, ya tashi a hankali ya nufi band'aki cikin 'kwarin jiki, sai kawai na tsinci kaina da bin sa da kallo da tausayinsa 'kadan a cikin raina.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 88&89
Gadon na shiga bi da kallo kamar me neman wani abu. wayoyinsa ne akai sai farin gilashinsa da kuma littafin husunul muslim a ajiye a gefe, sai kuma 'kamshin turaransa da ya mamaye d'akin, komai nasa a tsanake babu harigido a ciki, dattijo ne mai kamala da hallin dattako.

Ajiyar zuciya na sauke tare da tsirawa k'ofar 'bandakin ido! fitowarsa daga band'akin yasa nayi gaggawar d'auke kaina, kai tsaye 'katuwar wardrobe din da ta cinye bango guda ya nufa yana neman kayan sawa.

A nutse na je na tsaya a kusa dashi tare da fad'in" Ka je ka zauna na duba maka kayan.

Kallo na yayi da mamakin magana ta.

Sai na d'an saki fuskata tare dasa hannuna kan kayan nasa ina dubawa.

Ban an kara ba kawai na ji shi a jikina, ya zagaye k'ugu na da hannuwansa tare da d'ora ha'barsa a kafad'ata.

Cikin fad'uwar gaba na juyo rigar dake hannuna ta fad'i a gurin.

'Kokarin k'wace jikina nake yana sake matse ni a jikinsa dake wani irin karkarwa!

'Kafafuna suka shiga kyarma! jin yanda yake yawo da hannuwansa a sassan jikina.

Kuka nasa tare da ture shi da 'karfi na matsa gefe ina gyara zif d'in rigata da ya zuge min.

Da azama! na kama hanyar fita, sai yayi saurin tarar gabana, ya sanya mukulli a jikin 'kofar d'akin, ba tare da ya ce komai ba ya ja jikinsa da babu 'kwari ya hau gado ya kwanta har da jan bargo.

A sanyaye na ce" Ka bud'e min 'kofar na fita.

Shiru yayi be ce min komai ba.

Ganin haka yasa na zauna kan kujera tare da zabga tagumi! abinda yayi min yanzu ya tsorata ni, mutumin da bashi da lafiya.

Motsin ta'ba 'kofa na ji sai nayi sauri na kalle shi har yanzu yana cikin bargo a lullu'be.

Na ce" Za'a shigo fa."

Shiru babu amsa.

Gurinsa na nufa domin neman mukkulin, ya bud'e fuskarsa da alamun bacci ya bani mukullin da fad'in."Amma don Allah kada ki ce zaki koma wannan gurin ina bukatar ki zauna tare dani, ina neman wannan alfarmar."

Jikina ne yayi sanyi jin yana had'a ni da Allah kamar ya san kud'iri na kenan. Ni kaina ina jin wani iri a duk lokacin da yake 'kas'kantar min da kai.

A sanyaye na je na bud'e 'kofar. Shukura ce ta shigo hannunta ri'ke da kwandon abincin. wani irin wula'kantaccan kallo tayi min kafin ta wuce cikin d'akin.

Sosai raina ya 'baci da iskancin da yarinyar take min, idan tayi min wulakanci a can baya nayi ha'kuri, to yanzu zahirin gaskiya ba zan iya jura ba, domin kuwa a matsayin uwa nake a gurinta ko tana so ko ba ta so dole ta girmama ni kamar yanda zata girmama mahaifinta. idan ma ba zata gaishe ni ba to ba zan jure kallon banza da zagi ba.

K'ofar na rufe na je na zauna ina kallonta tana fad'in" Daddy ka tashi ka ci abinci ka sha magani."

Na kalle ta babu walwala a fuskata na ce" Ki rabu da shi mana ko ba kya ganin bacci yake?"

Ta juyo a fusace! tare da cewa" Kin ga malama kada kiyi min shishshigi"

Kafin nayi magana har ya 'bud'e fuskarsa. rai a 'bace! ya kalle ta da fad'in" Tun da kin kawo min abincin, tashi ki je kawai."

A sanyaye ta tashi ta fita kamar ta fashe da kuka.

Na kalle shi yana 'ko'karin sake rufe fuskarsa na ce" Yana da kyau! ka tashi ka ci abincin sai ka sha magani ko."

Minti biyu da magana ta ya ta shi tare da cire bargon dake jikinsa ya sauko da 'kafafunsa 'kasa! sai kuma na ga ya dafe kansa da duk hannuwansa.

Ganin haka sai jikina yayi sanyi na tashi na je kusa dashi na zauna. Cikin zuciyata nake jin d'an tausayinsa, da alama yana jin jiki daurewa kawai yake. kafad'arsa na dafa a hankali na ce"Sannu kan ka ne yake ciwo ne?"

Girgiza kansa yayi ba tare da ya kalle ni ba.

Na sauke ajiyar zuciya da fad'in" Na ga ka dafa kai ne, shine nake tunanin ko ciwon kai ne ya matsanta maka.

Ya cire hannuwan nasa tare da zuba min ido.

Kasa kallonsa nayi sakamakon ganin yanda 'kwayoyin idanuwansa suka sauya jajawur! yanayin kallon da yake min ne yasa jikina mutuwa! gabana kuma na cigaba da fad'uwa!

Hannu na ya ri'ke tare da fad'in" Ina da damuwa mai tsanani."

Nayi shiru ina kallonsa. Ya cigaba da cewa; Kasancewar ki a kusa da ni ya janyo min sha'awa mai tsanani, gashi idan ina cikin wannan halin bana iya sarrafa kaina."

Na kalle shi a lokacin da yake bin ilahirin jikina da kallon kurulla, gabad'aya yanayinsa ya sauya yayi sanyi sosai, hannunsa dake ri'ke da nawa sai karkarwa yake.

"Yanzu me ka ke bu'kata?" Na tambaye shi duk da na harbo jirgin nasa.

"Ki mallaka min kan ki a wannan lokacin." Ya fad'a tare da kusantar jiki na.

Kai na girgiza. alamar ba zan iya ba.

Ya ce."Saboda me?" Shiru nayi ban bashi amsa ba saboda na san da cewa bani da wata hujja.

Rungume ni yayi tsam! a jikinsa! yana makyarkyata! kuka nasa ina ture shi tare da fad'in" Ka rabu da ni don Allah.

Cikin kunnuwana na ji yana fad'in" Ki taimaka min na rage damuwa ta shekara da shekaru matata ba zan cutar dake ba."

"Ni dai A'a ban shirya faruwar hakan ba.'' Cikin shagwab'a da sangarta nayi maganar ina kokarin raba jikina da na sa.

Yanda na fahimta hakan da nake kamar 'kara masa 'karfin gwiwa nayi domin rikicewa yayi yasa 'karfi sosai ya kwantar dani kan gadon yayi min rufa!

Sosai nayi mamakin abubuwan da yake min tamkar ba mara lafiya ba, hannayensa sai yawo suke a sassan jikinta.

Gabad'aya gwiwa ta tayi sanyi sakamakon abubuwan da yake min, 'kamshin jikinsa ma ya taka muhimiyyar rawa gurin hana ni 'kwatar kaina.

Kamar a mafarki mu ka ji an bud'e 'kofar d'akin an shigo
da saurin gaske ya sauka daga kaina tare da juyawa domin ganin waye ya shigo. gefen rigarta kawai mu ka yi katarin gani domin da saurin ta bar gurin ba tare da ta rufe 'kofar d'akin ba.

Takaice yasa na fashe da kuka da fad'in" Ka gani ko?"

Ba tare da ya ce komai ba ya juyo da nufin sake kwantar da ni, sai na matsa gefe da sauri ina gyara wuyan rigata, sauka nayi daga gadon, k'afafuna sai rawa suke, na ce" Yanzu kayi wannan abun ya za a yi su yarda baka da lafiya.

Murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga band'aki ba tare da ya ce min komai ba.

Na zauna kan kujera gabana sai bugawa yake, komai yana bu'katar sirri ya zama dole ya takawa yarinyar nan burki ta daina bankad'o mana d'aki tana shigowa ba tare da neman izini ba.

Ko da ya fito daga toilet din ban iya kallonsa ba, saboda tawol ne d'aure a jikinsa, cikin zuciyata na ce" Dole ciwo yayi ta damunsa ko da yaushe cikin watsawa jiki ruwa.

Band'akin na shiga na tsafta ce jikina, domin ni kaina ban yarda da kaina ba, abinda ya faru a tsakaninmu yasa wandon dake jikina ya 'baci! wanke wa nayi na shanya a band'akin na fito na same shi a zaune kasan kafet yana duba wayarsa.

Har nayi nufin zama kan kujera, na ji maganarsa. "Kada ki zauna zuba min abinci nan." Ya fad'a ba tare da ya kalle ni ba.

Na zuba masa daidai gwargwado na ajiye a gabansa, niyyar barin gurin nayi, ya ce" Zauna ina so muyi magana.

Zama nayi kaina a 'kasa

Ya ajiye wayar hannunsa a gefe, kafin ya kalle ni, ya ce." Za mu ci abincin tare ko?"

Girgiza kai nayi. Ya ce." me ki ka ci to?" shiru nayi masa tare da d'auke kaina. Ya ce." Na fara gajiya fa da wannan abubuwan da ki ke min zan kai 'karar ki gurin mahaifinki"

Kallonsa nayi da mamakin maganarsa, ya ce." 'Kwarai kuwa! ki kalle ni da kyau! kin san a shekaru na haife ki ko? amma na ajiye girmana ina rarrashinki duk don mu zauna lafiya kina min wasu abubuwa saboda kin fahimci cewa Allah ya jarrabe ni da sonki shin ko ba haka bane?"

Ban ce masa komai ba.
Chapter 17 · 0% Book details