← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tare suka shigo d'akin da Hajiya, sai nayi saurin rufe idona, kunya nake ji kada ta fahimci wani abu ya faru. ashe zuwa yayi ya fad'a mata abinda ya ke da akwa. shine ta shigo ta duba ni.

Kamar na fashe da kuka saboda takaici! ban iya cewa komai saboda nauyi da jin kunya baccin 'karya na tsira, ina jin suna ta maganganu nayi luf! sai da ta fita daga dakin sannan na bud'e idona na kalle shi. yana zaune kusa da k'afafuna yana waya!

Cikin dubara na tashi zaune na d'an jingina da fuskar gado! ganin na tashi yasa ya katse wayar da ya kalle ni, cikin kulawa ya ce." Sannu kin ga yanzu Hajiya ta fita ta shigo duba ki."

Zum'bara baki nayi tare da fad'in" Me yasa ka fad'a mata wani abu ya faru a tsakaninmu?"

"Me yasa ba zan fad'a mata ba? bayan ta damu da nayi aure na haihu, sannan kuma yanda ki ke kuka da gurin shi ya bani tsoro na je na sanar da ita ko da wani taimakon da za tayi mana." Yafad'a idonsa a tsaye a kaina.

Na ce" Gurin fa zai dusashe in sha Allahu.

To "Allah ya yarda, amma na yi waya da likitana duk nayi masa bayani abinda ke da akwai, ya bani tabbacin cewa; idan ana bu'katar gurin ya zama normal sai an 'kara wani abun, shine na ce ko zaki bari nayi wani yanzu ko da sau d'aya ne.

"Bangane ba." Na fad'a gabana na duk uku-uku! don gabad'aya hankalina ya tashi jin abinda ya ke fad'a.

Sai ya fashe da dariya yana kallona. Ganin haka yasa na juya masa baya domin na fahimci tsokanata yake.

Da sauran dariyar a tare da shi ya ri'ke hannuna da fad'in" Da wasa nake miki my love ba zan miki komai ba sai gurin ya warke in sha Allahu."

Ba tare da na juyo ba na ce" Ka tabbata?"

Shiru yayi be bani amsa ba.

Shukura ta shigo da'kin da sallama a bakinta. shi ne ya amsa, ni kam kunya tasa na rufe idona, ina 'kokarin 'kwace hannuna dake cikin nasa, ya ri'ke da kyau!

'Bangaran Shukura kuwa ganin ta, kwance lakadan a gadon mahaifinta, sai wani bakin ciki ya turnu'ke ta, ga shi kuma a zaune ya kusa da ita hannunsa cikin nata, kamar ta kurma ihu! saboda takaici.

A sanyaye ta ajiye kwandon abincin dake hannunta, ta ce"Daddy ina kwana?"

Ya amsa cikin kulawa yana nazarin fuskarta domin ya hango damuwa a tare da ita.

Sai da ta daure zuciyarta sannan ta ce" Antina ina kwana."

Ba tare dana kalle ta ba na amsa da "Lafiya lau." daga haka ban ce komai ba, amma cike nake da mamaki ya akayi yarinyar ta sauko har take gaishe ni.

Ta ce"Daddy Hajiya ta ce na kawo muku abin karin kummalo idan anti ba za ta iya saukowa 'kasa ba"

Hankalinsa gabad'aya yana kaina ya bata amsa da cewar" To babu laifi hakan."

Hanyar fita ta nufa jikinta duk a sanyaye. sai kuma ta kasa daurewa ta tsaya tana kallonsa kafin ta ce"Daddy ya maganar da mu kayi da kai kwana biyu da ya wuce?"

Ya ce." Wace magana kuma?" domin shi ya manta ma sunyi wata magana.

Ta ce" Akan dawowar Mommyna d'akinta da kuma al'kawarin da kayi min."

Tsawa! ya buga mata tare da nuna mata hanyar fita. " Wuce ki bani guri shashashar banza."

Da saurin gaske ta bud'e k'ofar ta fita tana sgare hawaye.

Na kalleshi sai na ga duk babu walwala a tare dashi.

Na ce" Ya za ayi ka kore ta har kana yi mata tsawa! kada fa ka janyo min 'bakin jini, Shukura 'yar ka ce bai kamata kayi haka ba."

Babu fara'a a tattare dashi ya ce." Ke a ganinki abinda tayi ya da ce?"

Ido na tsira masa da fad'in." Magana kayi da ita har kayi mata al'kawari lefi ne don ta sake tuntu'barka da maganar.

Ya ce." A'a ni ban yi mata al'kawarin dawo da mamanta ba, ta dame ni da maganar sai na ce mata zan duba na gani."

Dama abinda nake so na ji kenan daga bakinsa.

Sai kawai nayi shiru raina gabad'aya ya 'baci! ban san me yasa ba haka kawai nake jin kishin matan da yayi tarayya dasu duk da cewa a yanzu basa tare, amma haushinsu nake ji sosai!

Shiru d'akin yayi na 'yan mintina, kafin ya kalle da cewa" Ki tashi ki ci abinci ga farfesu Hajiya tayi miki." Yana 'kokarin bud'e fulas din yake magana.

Motsi ban yi ba ballanatana yasa ran zan sauko na ci wani abu.

Ya gaji da maganarsa ya had'a shayi da kansa ya karya ya sha, kafin ya zuba farfesun ya dangwala da biredi.

Cikin bacci da ya fara fizgata na ji shi yana laluben hannuna dake cikin bargo, ya saka min wasu takardu.

"Tashi zaune za muyi magana."
Yafad'a babu wasa a muryarsa.

Sai da na mula tukkuna na tashi zaune. har yanzu na kasa sakin fuskata, duk na damu jin maganar dawo da uwar gidansa.

Cikin nazari ya ce " Duk kin sauya fuska saboda wani dalili mara tushe! kada fa ki damu, na riga na shafe babin Fatima a rayuwata, domin da zan dawo da ita to da tun kafin na aure ki na dawo da ita, don haka ki samu nutsuwa.

Daurewa nayi na ce'' Waye ya fad'a maka na damu? kaina ne fa yake min ciwo ba wani abu ba.

Murmushi kawai yayi tare da fad'in ''Ai na gane ana 'kaunata yanzu tunda na ga kishi 'karara a cikin idonki."

Shashantar da maganar nayi ta hanyar fad'in" Wannan takardun fa?"

Ya ce" Naki ne."

Na tsira masa ido domin yayi min 'karin bayani.

Ya fuskance ni sosai kafin ya ce." Kasancewar na samu abu mai muhimmanci a gurinki yasa nayi miki wannan kyautar. takardu biyu ne a hannunki, akwai na gidan mai da kuma na rumfar kasuwa dake kwari, yanzu haka ana cigaba da hada-hada na kasuwanci a kowane sassa, abinda aka samu duk ya zama mallakinki, ina miki fatan alheri.

Na kalle shi da mamaki mai yawa a tare dani, na ce"Saboda kawai ka samu budurci a tare dani zaka bani gidan mai sukutum! nayi me da shi to?"

Sai ya 'bata fuska da fad'in" Ba wai ba ne a gurina, kuma budurcinki ya cancanta da komai. domin zan iya tattare duk abinda na mallaka a duniya na baki saboda farin cikin da ki ka sanya ni a ciki, saboda haka ki dauki al'amarin da muhimanci, ki kuma sa a ranki cewa; kin bani abu mai daraja wanda bani da abinda zan biya ki dashi.

Gabad'aya jikina yayi sanyi da kalamsa. kawai na ri'ke takardun tare da zuba masa ido, ni dai ban ga abinda zanyi da gidan mai ba, ina lefin rumfar kasuwar.

Kira ne ya shigo wayarsa ya d'auka! nan na ji yana fad'in" In sha Allahu gobe zan shigo kano d'in sai a san yanda za a yi.

Na ce" Don Allah mu tafi tare."

Girgiza kansa yayi da fad'in" Za ki je amma ba yanzu ba sai kinyi nauyi.

Sai na rasa inda maganarsa ta nufa, sai nayi nauyi kamar yaya?

Ya katse tunani na ta hanyar fad'in." Kina bu'katar zama a wannan sashen ko za ki koma naki domin na riga na gama shirya miki komai."

Girgiza kai nayi da cewa" A'a gwara nan d'in."

Ajiyar zuciya ya sauke da tare da cewa "Shikkenan abinda ki ka za'ba shine za'bi na."
Chapter 20 · 0% Book details