← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai na tashi hai'kan! da neman kud'i, duk abinda za'ayi da jiki k'arfi ina zuwa na yi mutukar zan samu abinda asiri na zai rufu, ni ne wanki da guga! gyaran takalma, aikin gini, dako cikin kasuwanni, gefe guda kuma ina yin gyaran babura da siyar da fetur a bakin titi, asiri na kuwa ya rufu, domin na d'aukewa mahaifiyata da k'anwata nauyin komai, don ba naso suyi kukan maraici! shiyasa nake fita nema ba dare ba rana.

Ganin haka yasa Hajiya dawowa gidan, a cewarta ai suma suna da hakki a kaina, duk neman da nake uwata nake wahaltawa, sai ta dawo gidan ta share d'aki ta zauna, tsirfar yau daban ta gobe daban, gashi ita kuma mamana bata da hayaniya! kuma bata son tashin hankali, shiyasa duk abinda Hajiyan tayi mata sai ta kawar da kanta, amma abin yana damunta mutu'ka, ni ma abin yana yi min ciwo, ranar da na samu zama a gidan, zan shiga har dakinta na zauna domin na nusar da ita cewa abinda take ba daidai bane, sai kawai ta fashe min da kuka ta lauya zancen da cewa; don naga 'kasa ta rufe idon mahaifina shiyasa nake nuna mata cewa mamana tafi ta girma a guri na, ganin haka yasa kawai na rabu da ita sai dai na daina sakar mata fuska, ko wasa take min bana saurararta nake shigewa na tafi harkokina, sai ta rarrafo ta fito tsakar gida ta zauna ta dinga habaici! wanda yake damun zuciyar mamana! bata kaunar tashin hankali da damuwa, haka za suyi ta kuka ita da Sadiya a daki abin na damun ransu.

Cikin ikon Allah da wannan buge-buge da nake na samu na sayi fili, sai dai tunda Hajiya ta ji labari, ta dame ni kan lallai sai na fito da matar aure tunda ina samun kudi, nayi kokarin nusar da ita cewa; kudin da nake samu na rufin asiri ne, zanyi aure amma ba yanzu ba.

Ta 'ki yarda da maganata, kawai ta kira Baba Auta ta fara sheda masa halin da ake ciki, 'kiri-'kiri na ga hassada a cikin idonsa, jin cewa na sayi fili har na soma gini, ya dinga fad'a mara dalili wai akan me duk abunda zanyi ba zan nemi shawararsa ba, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa.

Ya ce." Shikkenan Allah ya sanya alheri, maganar aure kuwa dole mu yi maka ka fito da mata, idan kuma baka da ita to na baka Fatima."

Gabana ya fadi! na kalle shi da mamaki a tare da ni na ce." Wace Fatima?"

Ya ce"Ta waje na mana ko kana ganin kafi karfin ka aureta ne?"

Na ce." Gaskiya bana ra'ayinta Baba auta babu maganar rufa-rufa a tsakaninmu, Fatima 'yarka ce amma kasan bata da kamun kai ko?"

Ya ce." Magana zaka fada min a gaban ido na?"

Na ce" Ba haka bane na jaddada maka abinda ka sani ne, ni d'in ba mace bane, ballanatana ayi min irin auran da bana ra'ayi, a kyale ni da kaina zan duba matar da ta cancata.

Sai kawai ta fashe! da kuka da fadin" Saddiku wannan sharrin na mahaifiyarka ne, domin ita take zama ta kitsa maka komai, amma ina laifin wanda yayi maka kyauta, Fatima dai 'yar uwarka ce duk lalacewarta ba zaka sanja ta ba.

Ya ce." Ki rabu dashi Hajiya tunda shi bashi da mutunci, a gaban idona yake cin fuskata, to shikkenan tunda kace baka sonta sai ka fito da wacce ka keso." yana gama maganarsa ya tashi fuuuu! ya fita.

Nima tashi nayi na bar gurin raina a 'bace! gaskiya ba zan lamunci wannan kama karyan ba. domin dai yarinyar kowa ya san halinta, sam bata da nutsuwa da tarbiya ga shegen kula maza da sauraran abubuwan da basu dace ba, a wannan zamanin kowane uba yana so ya za'bawa 'ya'yansa uwa ta gari, to akan me yana ganin kashi da rana ya taka, ba zai yuwu ba.

Ko da na shedawa mamana halin da ake ciki, sai ta ce tunda abun ya riga ya zama haka to nayi gaggawar fito da matar da nake so na aura, domin a ganinta hakan zai sanya su janye maganar Fatima.

Na shiga tsaka mai wuya a lokacin, domin kuwa tunda na girma na kai munzali na samartaka ban ta'ba kula wata budurwa ba, ba don bani da bukata ba, a'a asali ma ni mutum ne mai yawan sha'awa, shiyasa sa'i da lokaci nake azimi domin tseratar da kaina.

Ina son aure sosai, to amma ina cizawa! domin na riga na san aura a yanzu dole sai ka shirya, nauyi biyu ne zai hau kaina dana iyalina da na mahaifiyata da 'yar uwata.

Amma tilas tasa na yankewa kaina shawara domin gujewa auran Fatima wacce babu ita a cikin tsarin rayuwata

Na je na samu mahaifiyata da maganar Na'ima 'yar 'kaninta ce Baba Salihu, yarinyar tana da tarbiya sosai da kunya, wannan shine abinda ya ja ra'ayi na akanta har na ji ina sha'awar auranta.

Tayi shuru tana nazarin al'amarin kafin ta ce." *D'an gaske* da yake sunan da take kira na dashi kenan, sakamakon sunan mahaifinta ne, ta cigaba da cewa" ina gudun abinda zai biyo bayan al'amarin, domin bana son tashin hankali, kuma ban mance da wasiyyar mahaifinka ba, kan cewa lallai na kula da mahaifiyarsa ka da tayi kuka damu, muyi kokarin ganin mun rabu da ita lafiya, wannan dalilin yasa duk abinda Hajiya take min a gidan nan, bana d'aga kai na kalleta, domin zama na amana da mutunta juna nayi da mijina, duk da mahaifiyata bata yare, ya zama dole na girmama tasa, saboda haka ban hana ka nemi auran Na'ima ba, amma ka je ka shedawa 'yan uwan mahaifinka domin mu ji hukuncin da za su yanke.

Hajiya tayi tsalle ta dire tace bata amince ba, wato naje na had'a baki da uwata ta dauki 'yar kaninta ta bani, na guji 'yar uwata Fatima, to bada yawunsu ba, muddun nace dole sai na auri Na'ima sai dai na sanja iyaye, gabad'aya suka had'e bakinsu, Kawu Audu dashi Baba Auta din, babu wanda ya fahimce ni.

Mamana ta umarce ni cewa na janye maganar auran Na'ima na amince da auran Fatima domin samun kwanciyar hankali, amma zata tsananta da yi min addua insha Allahu ba zan lalace ba.

Jin haka yasa na amince ba don raina yaso ba, sai don samun zaman lafiyarmu bakid'aya. amma sam Fatima bata daga cikin tsarin matan da nake so na aura.

'Bangaran wacce ake dambawar don ita, ko da ta samu labarin abinda yake faruwa, sam bata nuna damuwa ba, domin ta jima da sona a cikin zuciyarta, duk da bata furta min ba, amma duk alamomi sun bayyana, idan zamu had'u a ko'ina ne sai tayi min magana irin ta rashin kamun kai, "Wallahi kana burgeni, ina son namiji dogo giant (ingarma) wanda na san ya cika cif, zai gamsar da ni a shimfida, ire-iren wannan maganganun banzan take min a duk sanda za mu had'u, sai nayi mata jan ido sannan! na nuna mata cewa; ni nafi k'arfinta, amma hakan baya hana ta sake zuwar min da maganganun banza makamanta wannan. a duk sanda zamu had'u a wani guri

Tunda ake maganar auran ban taka k'afa na je gurin yarinyar ba, komai suke ina kallonsu ne kawai, nayi iyakar abunda zan iya na lefe da sauran abubuwan bukata na aure.

Sai ga ta tazo ta same ni a gurin aiki na tare da 'kawarta, kallo daya nayi musu na kawar da kaina domin raina ya 'baci da ganin sutturar dake jikinsu, komai a bayyane.

''Magana na zo nayi da kai" tafada a lokacin da take tsaye a kaina.

Na kalleta tare da fadin."Me yake tafe dake?" kai tsaye ta ce."Kudin 'kunshi da kitso nake bukata.

Dubu uku na bata amma na gargade ta kan cewa; kada ta kuskura ta zo min gida da gashin doki, domin gwanar 'karin gashi ce da tara farce, ga uban bilicin da take, duk ta lalata fatarta!

Ta'be bakinta tayi ta ja hannun 'kawarta suka tafi, tana maganganu kasa-kasa wanda na san dani take.

'Daki da rumfa kawai na samu na kammala, na dan kwaskware! dai-dai gwargwado. amma kicin da band'aki da sauran aiki, dan babu fulasta ballanatana rufi, haka nan na hakura, saboda yanda wahala tayi yawa, ga bikin ya matso komai ya kacame! babu mataimaki sai Allah.

To tunda aka d'aura auran, ban wani saki jikina da ita ba, na dai sanya mata ido ne kawai ina nazari a kanta.

Duk wani hakkinta da ya rataya a wuya na, ina kokarin ganin na sauke shi, amma kuma ban ta'ba had'a shimfida da ita ba, a falo nake kwanciyata ita kuma a cikin uwar daki, haka nan, za tayi shigar fitar da tsaraici a gabana tayi ta juyawa, amma cikin ikon Allah ba ta iya jan ra'ayi na zuwa gare ta.

Sai kawai ta je ta fad'awa Hajiya cewa; bani da lafiya domin tunda akayi auranmu wata hud'u ban ta'ba kwanciya da ita ba.

Hajiya ta samu abin yi ta je har d'akin mamana ta rufe ta da fad'a, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cin mutumci iri-iri abin mamaki! Fatima har tana sanya baki, anan ne Sadiya ta gaza hakuri ta fara mayar da martani, Hajiya ta gaura mata mari tana fadin" Wato za ta goyi da bayan uwarta kenan! to shikkenan zata sanya kafar wando daya dasu gabad'aya!

Sai da nazo gidan Sadiya ke sheda min abinda ya faru, sosai raina ya 'baci! idan Hajiya ta ci zarafin mamana na rabu da ita to babu shakka Fatima ba zata wanye lafiya ba, domin bani da hakuri a kan mahaifiyata da nake jinta a cikin ko'kon raina!

Sosai ta ga 'bacin raina akan abinda tayi, na ce kuma lallai in tana bukatar zama dani to ta je ta bata hakuri, idan ta'ki wallahi sai na sake ta. wannan shine hukuncin dana yanke mata.

'Kwana d'aya biyu shuru ba tabi umarnina ba, a cikin kwana na ukun, na rubuta mata saki daya a takarda na ce lallai kafin na dawo ta fice min daga gida.
Chapter 4 · 0% Book details