Sashe 2
Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta dinga girgiza kanta tana auziyya a cikin ranta, wasu hawaye masu d'umi! ne suka shiga sauka a kumatunta, dama duk wani kwane-kwane da yake ta riga ta fahimci abinda yake bukata kenan da ita, ko ga yanayin kallon da yake mata a duk lokacin da suka had'u! ai talauci ba hauka bane, tana ganin ko me zai mallaka mata ba zata amince da bukatarsa ba.
Ganin tayi shuru kawai tana kallonsa da hawaye a fuskarta, sai ya tashi jikinsa na rawa! ya 'kan'kameta yana shashshafa bayanta sai kisses yake mata har ya samu nasarar cire mata dankwalin kanta yana hargitsa mata gashi wanda ta wanke ta d'aure shi da ribbon.
Wani 'karfi ne ya zo mata a lokacin, ta ture shi tare da kurma uban ihu! ta sa hannuwanta duk biyun aka tana kiran sunan Allah! kuka take tukuru! dan ganin yanda yanayin sa ya sauya gabad'aya! ya rikirkice! yana nema ya kwantar da ita a saman kujera tana duddukansa ta ko'ina! kuma ba ta fasa kurma ihu ba tana kiran Allah ya kawo mata dauki.
K'arfi ya sa mata sosai ya ri'ke ta da kyau! don ganin ihun da take yana nema ya tarwatsa 'kwanyarsa! ya matse ta a jikin bango! sannan ya had'e bakinsa da nata! gam! ya ri'ke ya hana ta ihu! a lokacin da bakinsu ya had'u ji tayi kamar an bubbuga mata 'tabarya a k'afafunta sai kyarma take tana ta so ta k'wace bakinta abin ya fassakara, ya ri'ke harshenta da kyau! so yake kawai ta samu nutsuwa!
Sanyi jikinta yayi sai uban hawayen da yake gararanba a saman fuskarta, wanda shima tasa fuskar duk ta ji'ke da ruwan hawaye, ba kuka yake ba amma tsabar tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin ya sanya kwayoyin idanuwansa mugun ja! ita da shi suka dinga rawar jiki ita dai na tsananin tashin hankali da fargaba ne, shi kuwa na tsantsar sha'awa ne da bukatuwa zuwa wani abu da yayi shekara da shekaru bai samu ba.
Sai da ya tabbatar ta nutsu jikinta ya mutu sannan ya cire bakinsa daga nata, ya dan ja baya tare da zuba hannuwansa cikin aljihu yana yi mata wani irin kallo na tausayi da mugun so!
Ta zube 'kasan 'kafafunsa tare da ri'ke daya ta ce" Don darajar Allah da Annabi ka da ka aikata fasadi dani, kada ka janyo mana fushin ubangiji! zina babu kyau! mussaman ga masu aure hukunci mai tsanani Ubangiji ya tanadar ga masu aikata wannan lamari, wallahi tunda nake ban ta'ba zina ba, kuma bana fata na fara da kai, bana bukatar komai daga gare ka, ni na yarda na cigaba da zama matalauciya mai rangwamin gata, shin wai ma me za kayi da ni? duk ga mata nan a gari kyawawa masu aji da kyawun jiki, mai za kayi da iri na nakassashiya mara gata, kana da kudi ka je ka nemi irinka amma ni don girman Allah ka fita daga cikin rayuwata.
Cikin tsantsar tashin hankali da kuka matsananci take wannan maganganu.
Amma ko a fuska bai nuna sadudarsa ba ya cire k'afarsa tare da komawa kan kujera ya zauna yana kallonta babu alamun sassauci a tare da shi ya ce.'' Wannan shine karo na farko dana bukaci wani abu a gurin wata 'ya mace ta yi min gardama! kamar ni, na nemi da ki bani kan ki, amma ki cika min kunne da ihu! har kina kai min duka da cizo da yakushi! wai shin meye a ciki ne? na farko dai wannan lamari idan ya faru tsakanina dake ne, babu wanda ya ji ko ya gani, amma duk kin tashi hankalinki a banza a wofi wanda ni kuma duk abinda za kiyi ba zan janye kudiri na ba, dole sai na kwanta dake domin zuciya da gangar jikina suna bukatar hakan, saboda haka zan baki kwana uku ki je kiyi tunani, amma ki zo min da abinda zan gamsu, tunda na fada miki ni dai ba zan iya hakuri dake ba. cikin jaddada aniyarsa ya kai karshen maganar.
Hannu tasa ta goge ruwan hawayen da yake zuba ta ce." Wai kai baka tsoron Allah? ba ka tsoron ranar da zaka tsaya a gabansa, ranar tonan asiri, ranar da kudi da mulki ba za suyi tasiri ba, a ranar ne Allah zai nuna wa jama'a waye kai cikinsu kuwa harda mutanan da suke ganin girma da mutuncinka, a gidan duniya, kowa yana ganin girmanka, dalilin taimako da sadaukarwar da kake da dukiyarka, a zahiri kai mutumin kirki ne, amma kuma wani 'bangaran ka samu nakasu! saboda miyagun halayen da kake aikatawa irin wanda Allah ya haramta.
A cikin al'kur'ani mai girma Ubangiji subahanahu-wata'ala ya umarce ku da ku aura daga d'aya zuwa biyu da abinda yayi sama, mutukar kuna da iko kuma za kuyi adalci." Ta d'an sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa; Allah yayi maka komai na daga jin dadin duniya ya wadataka da arziki da rai da lafiya da ji da gani bai tauye ka ba, to mai zai sanya ka butulce masa? kana da dukiyar da zaka auri mata hud'u ka ajiye a gidanka domin raya sunnar ma'aiki salallahu alaiyi wassalam, amma kana zubar da 'kima da mutuncinka, ka sani cewa duk abinda ka yi a kan dan wani sai anyi da naka, saboda haka ka ji tsoron Allah ka daina bibiyar rayuwata."
A maimakon jikinsa ya mutu da nasihar ta, sai kawai ta ga yana murmushi tare da wasa da gemunsa kamar wacce tayi abin dariya sai kallonta yake yana murmushi, tsayin mintina uku kafin ya ce" Na gode da nasiha malama, amma ina sheda miki cewe; ina nan akan bakana, ba zan janye kudiri na ba, dole zaki bani kanki ko kina so ko ba kya so, ki je kiyi shawara na baki kwana uku kamar yanda na fad'a miki da farko." Ya na gama maganarsa ya tashi ya haye sama ya bar ta zaune a gurin cikin tsantsar damuwa da tashin hankali.
A tsakanin kwanakin sosai ta mayar da hankalinta gurin karatun al'kurani mai girma tare da shedawa Allah damuwarta, a yanzu dai ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko, dalili babu wanda za ta je ta fada masa damuwarta saboda wayar da take hannunta ma tun ranar da su kayi magana da Saliha ya 'kwace! har ya tafi bai bata ba.
Tana dai zaune a gidan tare da mi'ka lamuranta ga Allah.
Yau ne cikar kwanakin da ya gindaya mata.
Tayi ta k'o'karin danne damuwarta amma hakan bai samu ba, sai da Hajiya Saude ta fahimci damuwa a tattare da ita a lokacin da ta shiga domin gaishe ta.
Ta kalle ta, kafin ta ce." Shahida cikin kwana biyun nan ina ganin damuwa a tare dake ko da akwai wani abu da mu ke miki?"
Ta ji kamar ta fad'a mata abubuwan da suke faruwa, sai kuma wata zuciyar ta tsawatar mata saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, watakila idan ta tona maganar ita ce zata kwana a ciki, domin babu wanda zai yarda da ita.
Ta girgiza kai da fadin." Hajiya babu komai kawai dai bana jin dadin jiki na ne."
Tayi murmurshi kafin ta ce" Wai cikin naki wata nawa ne?"
Da sauri ta ce." Hajiya bani da ciki fa."
"Ke haba dai 'yar nan, to wannan laulaye-laulayen da ki ke na menene?"
Shuru tayi ba tace komai ba.
Shukura ta fito daga d'akinta ta shirya tsaf sai kamshin turare take, ta nemi kujera ta zauna hankalinta a kan wayarta ciki bada Umarni ta ce." Ke Shahida ki shiga dakina ki gyara min sannan kuma ki wanke toilet."
Hajiya Ta ce." Ai yau sai dai kiyi da kan ki ba ta da lafiya"
Wani irin kallo tayi wa Shahidan tana ta'be baki da fad'in." Hajiya gaskiya ba zan iya wani abu ba yanzu na riga nayi wanka ai d'akin nawa babu wani datti sosai! kawai ta tashi ta je tayi dama aikin ta ne"
Ta ce." A'a ki sa Marka mai aiki tayi miki mana ita wannan d'in ki kyale ta rana daya dai da huta."
Tana k'okarin magana ya k'araso gurin, duk sai su kayi shuru, suna kallonsa amma banda Shahida kanta yana 'kasa domin tunda taji 'kamshin turaransa ya cika gurin, hankalinta ya tashi, gabanta in banda fad'uwa babu abinda yake.
Ya ce." Hajiya maganar me ku ke ne? zuwa na gurin kun yi shuru sai kace wani mala'ika"
Murmushi ta yi kafin ta sheda masa maganar da suke.
Ya harari Shukuran kafin ya ce." Ke aikin me ki ke da ba zaki gyara abinda ki ka 'bata ba."
Tayi shuru ba tace komai ba.
Ya ce." Kada ki kuskura ki sake sanya ta aiki, ke kika 'bata kuma ke zaki gyara abinki."
A sanyaye ta ce."To Daddy."
Jin haka yasa ta tashi da niyyar tafiya gurinta ta d'an risina da fadin." Hajiya a tashi lafiya zan ni koma guri na."
Ta ce." To sannu, ubangiji Allah ya baki lafiya amma yana da kyau! kuje asibiti likita ya dubaki sosai laulayin yayi yawa gashi kin ce baki da ciki.''
Murmushi kawai tayi ta juya tare da kallon gefen da yake zaune, bata yarda ta kalle shi ba ta ce."Alhaji a tashi lafiya."
Shima ba tare da ya kalle ta ba ya amsa hankalinshi a kan wayarsa.
A gaggauce ta fita tana cigaba da neman tsarin Ubangiji akan mummunan al'amarin da yake bibiyar rayuwarta.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 65&66
Lamarin dai babu dad'i domin wani lokacin idan tsanani yayi yawa sai mutum ya gwammace mutuwarsa akan rayuwar da yake, sai dai kuma hausawa suka ce idan aski yazo gaban goshi to ya fi zafi! hakane kowane bawa akwai irin tasa kaddarar wanda babu wanda ya isa ya goge ta, to ita kam tana tunanin wannan ce kaddararta wanda ta tazo da kafafunta ta sameta har inda take, babu shakka wannan mutumin ya zame mata jaraba da kuma kaddara, ba kowa ne sila ba sai Mijinta wato wanda ta kwallafa rai a kansa take ganin shi din mai kaunarta ne, ashe kallon kitse takewa rogo, mutum ne shi azzalimi mayaudari, ta amince masa ya cutar da ita.