← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin ya'ke nayi na ce." Ni kam ba ni da abinda cewa domin har yanzu ina kokwanto akan ka."

Shiru yayi na minti uku kafin ya kalle ni da fad'in"Ta shi mu je na nuna miki wani abu wanda zai sake tabbatar miki da gaskiya ta."

Ban yi jayayya da shi ba, na tashi kamar yanda ya umarce ni, sai ya ri'ke hannuna muka fita harabar gidan...
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 84&85
Ni dai bin sa nake duk in da ya ajiye 'kafarsa nan nake ajiye tawa, har muka isa wata 'kofa dake wani d'an korido, tsoro na ji ganin gurin yayi duhu da yawa! na ja na tsaya ina 'kokarin cire hannuna dake cikin nasa. a nutse ya kalle ni da fad'in" Menene?" na ce" Wannan d'akin fa?" murmushi yayi kafin ya ce." 'Dakina ne, da nake ajiye muhimman abubuwa, kada ki ji komai ba zan cutar dake ba."

Nayi shuru ina kallonsa tare da tunanin wani abu a cikin raina. na ji mutane na fad'in yawanci masu kud'in da sukayi shura a duniya suna da wani 'boyayyan sirri wanda suke aikatawa na sa'bon Allah! haka kawai zuciya bata amince da shi ba, duba da yanayin gurin da ya kawo ni, wani irin d'aki a cikin ciyayi! da wata doguwar 'kofa zururu! gabana na fad'uwa! na ce" Ni dai ba zan shiga ba."

Kallona yayi da mamaki a tare da shi ya ce." Saboda me? ko har yanzu ba ki amince da ni ba?"

Baki na ta'be da fad'in" A'a kawai ina zargin d'akin ne watak'ila ba abin arzi'ki ne a ciki ba"

Yanayinsa ne ya sauya don na fad'in wannan maganar, jikinsa duk yayi sanyi kawai sai ya tsira min ido! ya d'an ban tausayi, amma ban nuna a zahiri ba, sai kawai ma na tafi na bar shi a tsaye a gurin.

Sosai ransa ya 'baci da abinda yarinyar take masa, gabad'aya ya rasa gane abinda take nufi, yanayin kallon da take masa shi kad'ai ke damunsa, ya riga ya gama sanya ta a cikin ransa, domin wani irin so yake mata wanda ba zai fasaltu ba, amma yana ganin sai ya sha wahala kafin ya samu kanta, don ganin irin kallon da take masa kamar wanda yayi mata gagarimun laifi.

Bai sake tunkarar inda take ba sai wajejan goma da rabi na dare ya shiga gurun da take cikin kayan bacci masu taushi, yana 'kamshin azababben turaransa.

Salamarsa kawai na amsa na sunkuyar da kaina don ban yi tsammanin zai shigo ba shiyasa na zauna da vest tare da siket wanda ya tsaya iya gwiwa! da sauri na d'auki dankwalina na yafa a jikina na d'an ture plate din da na ci abinci gefe na had'e jikina guri guda.

Zama yayi yana fuskanta ta, yayin da 'kamshin turaransa ya addabeni yana neman ya kashe min jiki. ganin yanda ya tsura min ido yasa duk na tsargu! sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce." Haka ki ke zaune a cikin duhu?" shima ya fad'i maganar ne kawai saboda ya ji dad'in bakinsa, waye ya ajiye ta a duhun idan bashi ba.

Shuru kawai nayi masa saboda raina ne ma ya 'baci da maganar tasa, wacce tayi kama da ta rainin hankali. Shirun nawa shi ya bashi amsa da kuma yanayin fuskata don 'kiris ya rage na fashe da kuka!

"Babu gaisuwa ko?" Ya fad'a yana haske ni da fitilar wayarsa.

Hannu nasa na kare fuskata, babu fara'a na ce" Ina wuni?"

Ya amsa babu yabo babu fallasa kafin ya d'ora da fad'in." Kin ci abinci?"

Kaina na d'aga masa.

Falon yayi shuru na 'yan mintina kafin ya sake wata maganar da ta sanya nayi saurin kallonsa.

Ya ce." 'Kwarai kuwa ina da bu'katar matata a wannan daran, ai nayi ma 'kokari kusan watanni uku ina kallonki ban yi komai ba, kada ki manta a cikin labarina na sheda miki cewa; ina da yawan bu'kata! saboda haka sai ki shirya domin ina so ki zama jaruma! mai d'aukar d'awainiyata."

Kuka ne ya 'kwace! min da sauri na ce" Ni wallahi ban shirya wannan al'amari da kai ba, domin dai ni ba kai nake so ba, saboda haka ka ajiye wannan maganar ni kawai ka dauke ni ka mayar wa da iyayena"

Murmushi yayi mai ciwo kafin ya ce." Ai kin shigo hannun Saddiku dattijon nan mai furfura! babu rabuwa a tsakanina dake yarinya sai dai mutuwa."

Tashi nayi da gudu na shige d'aki na kwanta a kan gado ina kuka! ni gaskiya ba zan iya bashi kaina ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma ban shirya zaman aure dashi ba.

Gadon ya hayo ya janyo ni jikinsa yana so ya rungume ni ina turjewa tare da fizge-fizge! sai kawai yasa min 'karfi ya matse ni tsam! a jikinsa yana ta jijjigani tare da shafa gashin kaina! rarrashina yake tamkar 'yar goye yana ta fad'a min kalaman soyayya a cikin kunnena har ya samu nasarar kashe min jiki ta hanyar fad'in" Da wasa yake babu abunda zai yi min. jin haka yasa nayi shuru, tare da gyara kwanciyata a jikinsa.

Cikin wata murya na ji maganarsa a kunne na. ya ce. "Me yasa ki ke tunani mara kyau a kaina?"

Shiru nayi ban bashi amsa ba. Ya cigaba da cewa; ba zan gaji da fad'a miki cewa ni ba zan cutar dake ba, kuma duk abinda ya faru, akwai dalili wanda na sheda miki, amma ban yi tunanin haka daga gare ki ba don Allah kiyi hakuri mu zauna domin mu raya sunnar ma'aiki tare."

Jin yanda yake had'a ni da Allah yasa jikina ya mutu! na ce" Ni fa muddin kana so na zauna da kai domin yin rayuwar aure sai ka kasance yanda na sanka a farko, domin ni fi bukatarka a haka."

Ya ce." Hakan ba zai yuwu ba, ki so zahiri na, shine abinda na fi buk'ata, amma wancan da ki ke so duk gaibu ne, shiri ne, nayi domin cimma wata manufa kuma Alhamdulillhi na samu nasara, amma ba zan zauna cikin yagaggun kaya da 'kazanta ba, wannan zai janyo min wani abu daban."

Na ce" Ni kam na fi bu'katar ka a haka, tunda kana ganin hakan ba zai yuwu ba shikkenan."

Murmushi kawai yayi bai sake magana ba. ganin haka yasa na tashi daga jikinsa na matsa can 'karshen gado! na ja bargo na rufe jikina.

Bacci ne mai nauyi ya d'auke ni, ko da na tashi da asubah! baya d'akin, ban damu ba, kawai na tashi na shiga band'aki da tunani mai yawa a cikin raina.

Sai da na shirya tsaf sannan na nufi cikin gidan don gaishe da Hajiya.
Da sallama a bakina na shiga falon, Hajiya da Shukura suna zaune a gurin cin abinci. na 'karasa a nutse na tsuguna har kasa na gaishe ta, ta amsa da fara'a mai yawa a fuskarta.

Cikin wani irin yanayi mara dad'i Shukura ta gaishe ni kamar anyi mata dole. nima na amsa babu yabo babu fallasa.

Hajiya ta ce" Ki zauna ki karya kummalo mana.

Na ce" Hajiya na ci abinci a guri na kafin na fito.

"Allah sarki." Ta fad'a kafin ta d'ora da fad'in." Mijin naki ai tun asubah ya tafi can garin mu jibia da yake duk 'karshen wata yana zuwa, ina fatan kunyi sallama da juna?"

Da sauri na ce" Eh Hajiya ya fad'a min, Allah ya dawo dashi lafiya"

Ta amsa da "Ameen ya Allah."

Tsaye na mi'ke tare da fad'in" Hajiya zan koma guri na sai an jima.

Ta ce"To shikkenan mu jima da yawa."

Tana fita Shukura ta kalli Hajiya da fad'in "Wai Daddy ya rasa wacce zai aura sai kurma! wallahi Hajiya abin yayi min ciwo sosai! tuntuni Mommyna take so ya dawo da ita ya'ki ya je ya kwaso wannan k'azamar."

Hajiya ta ce" Ke dai ki iya bakin ki Shukura bana son tashin hankali don Allah. domin abin farin ciki ne a guri na da Allah yasa yayi auran ina raye, maganar babarki kuma ki ajiye ta, a gefe domin da zai dawo da ita da tuntuni anyi an gama, saboda haka ki d'auki matar babanki a matsayin uwarki, kin fi kowa sanin halin mahaifinki, don haka kada ki ga kuna sa'anni da yarinyar nan, ki raina ta, duk 'kan'kantar ta uwarki ce, tunda tana auran mahaifinki."

Kawai sai ta buga tevur d'in cin abinci tare da fad'in" ba zai yuwu ba wallahi." hanyar d'akinta ta shiga tana surutai! Hajiya tabi ta da kallon mamaki!

"Mommy kina da labarin Daddyna yayi aure kuwa?" ta fad'a cikin ba'kin ciki da takaici!

Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Aure? yaushe yayi babu labari?"

Nan duk ta kwashe komai ta sheda mata.

Ta ce" Amma gaskiya 'Dan-gaske ya ba ni kunya, duk diddigin nasa anan ya tsaya? auran kurma wacce take da nakasu, mtsww! kada ki damu idan na dawo zan zo gidan, ai ko yana so ko baya so sai ya mayar dani d'aki na, ko kuma na hana shi kwanciyar hankali da matar tasa.

Ta ce."Mommy ni na rasa wace irin zuciya ce da Daddy, ke fa 'yar uwarsa ce, yana kallon yanda ki ke katangala! kiyi nan kiyi can, duk saboda shi amma ya 'ki ya saurareki, gaskiya Momy kiyi wani abu akai, domin ba zan iya bud'e idona na kalli kucakar yarinyar can a matsayin matar mahaifina ba, wai har Hajiya tana fad'in" Dole sai nayi mata biyayya"

Hajiya Fatima ta ja tsaki tare da cewa; ki rabu da Hajiya Saude tuntuni na fahimci cewa; ba ta son lefinsa, saboda yana da kud'i! babu yanda ban yi da ita ba, akan tasa baki ya mayar dani, amma ta'ki, saboda haka idan na dawo daga dubai, a gidan zan sauka duk sai na rikirkita musu lissafi tunda abin ya kasance haka."
Chapter 15 · 0% Book details