← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce"Ai baki biyo hanya ba, wallahi da kin fad'a min cikin mutunci ni mai iya saya miki ne, amma tunda ta wannan hanyar ki ka biyo shikkenan, gobe da wurwuri ki je ki kar'bo min kud'ina idan ba haka ba, ni dake ke ne"

Zubewa tayi a kasan dakin tana kuka, ni kuma nasa rigata na fita domin sayo sabulun wanka.

Sai da ta kar'bo min kud'ina sannan na 'kyaleta ta sha'ki iska.

Kwana biyar da faruwar al'amarin, na dawo gida naga babu kujeru a falo. na tambayeta suna ina? kai tsaye tace ta sayar dasu, domin ta sharewa kanta hawaye! tunda dai nata ne.
na ce to shikkenan, mutukar kuwa ta fita zuwa gurin bikin nan, a bakin auranta.

Ko a jikinta, biki na zuwa ta dinga zurga-zurga duk ina kallonta ban ce mata komai ba, sai da suka gama bikin tukkuna, da safe ta kwaso wanki za tayi, da zan fita na bata takarda saki, nace" wannan ita ce shedar sakin da nayi mata idan ta manta to na tuna cewa muddun ta fita da niyyar zuwa gidan biki 'kawarta a bakin auranta.

Kuka sosai ta dinga yi tana bani hakuri, ban ko saurareta ba nasa 'kafata na fita daga gidan.

Wannan abun dana aikata sai da nayi nadama! domin shine silar kwanciyar mamana 'bacin rai da tashin hankali ya janyo mata mutuwar 'barin jiki! kuka sosai nayi da idanuwana ganin mahaifiyata magashiyan rai a hannun Allah, nayi tur! da auran Fatima da kuma 'bakar zuciyata, duk da nasan duk abinda nake yi akan gaskiyata nake domin na kare darajar aure na.

Har Mamana ta gama zama a asibiti babu wanda ya taka kafa ya je domin dubata, gabad'aya 'yan uwan mahaifina da ita kanta Hajiyar sun dauki laifi sun d'ora mata cewa; da umarninta nake aikata komai, saboda haka babu su babu ita.

Nayi nadama sosai! kuma na zubar da hawayena ganin yanda 'bacin rai da damuwa suka haifarwa da Ummana matsala, 'bari guda na jikinta ya daina aiki, sai an taimaka mata! haka Sadiya take kula da ita, ni kuma ina yi da jikina da aljihuna, kuma nayi mata alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba, sosai tayi min fad'a ta kuma nuna min kuskuran abinda na aikata, cewa saurin saki ba shi da fa'ida ko don gaba kada na sake, tunda yanzu saura igiya daya to nayi kokarin ri'ke ta da kyau muddun raina! har cikin raina nayi nadama na kuma yi mata al'kawari cewa duk abinda Fatima za ta aikata ba zan 'kara daukar matakin sakinta ba. tana daga kwance ta dinga yi min kyawawan addu'o ina amsawa da "Ameen"

****
Bayan wasu
'yan wattani da
faruwar al'amarin. zamana da Fatima babu yabo babu fallasa, idan rikicin ya ratso mu nayi sosai! kuma ina ladabtar da ita yanda ya kamata don bana daukar wargi, amma ban sake yun'kurin sakinta ba duk irin 'bacin ran da zata sanya ni a ciki ina hakuri, don ko da naga magungunan planning (tsarin iyali) cikin kayanta, ban yi mamaki ba, saboda na san zata aikata abinda ya fi haka, kawai sai na d'auke! maganin na zuba a cikin masai! (shaddah) da yake bata da gaskiya ba ta tambayeni ba, sai dai kawai naga tana ta dube-dube a dakin.

A tsakankanin lokacin nake ta shirye-shiryen aurar da Sadiya domin tuntuni aka sanya ranar auran ana d'agawa, saboda yanayi na rayuwa komai ni nake na hidimar auran, cikin 'yan uwan mahaifina babu wanda ya tambayeni me nake shiryawa.

Na samu na had'a kudi dubu dari da saba'in wanda zan sayi kayan aikin da zan had'a mata gado da kujeru, da yake duk na iya komai, tunda sana'ar gidanmu ce, bisa tsautsayi na shiga da kudin gida, ashe Fatima taga lokacin dana d'aga kasan gado na ajiye kud'in! wallahi a daran na shiga wanka ta kwashe kudin, kwabo bata bari ba, tana zaune a falo na fito daga wanka na same ta, na ce" Ke kuma zaman me ki ke baki kwanta ba"

A sanyaye ta ce" Yanzu Ummana ta kira ni a waya bata da lafiya sun tafi ma asibiti! kasan tana da ciwon suga to shine ya tashi a daran nan.

Cikin alhini na ce" Allah sarki! addua za kiyi mata Allah ya bata lafiya."

Ta amsa da ameen kafin ta ce"Don Allah ka bari na je tunda dare beyi ba kaji kuma babu nisa a tsakaninmu"

Ganin yanda take had'ani da Allah da annabi yasa jikina ya mutu! na ce ta tashi taje Allah ya sawwak'e! aikuwa da saurin gaske tasa hijabi ta kama hanya fita.

Har 'karfe goma sha biyu da rabi bata dawo ba, hakan yasa na rufe gidan, domin zuciyata ta aiyyana min cewa a can zata kwana.

Har ga Allah ban kawo komai a raina ba, domin sai sauri nake na shirya na fita don gabatar da uzurirrikan dake gabana, ciki kuwa harda zuwa gidansu Fatima domin duba jikin mahaifiyarta

Sai dai me ina d'aga kasan gado da niyyar d'aukar kud'i na ga wayam! hankali ya tashi ainun! na sauke katifar gabad'aya tare da karagar gadon wai ko sun fad'a 'kasa! sai dai duk iyakar dubawar da nayi ban ga komai ba sai tarkace da 'kura!

Na zube kasan d'akin kaina na wani irin juyawa! tabbas ba kowane ya d'auki kudin nan ba sai Fatima domin na riga na san halinta ciki da waje, amma ya akayi ta san na ajiye kudi a k'asan gadonta, tunda lokacin tana kicin tana aiki.

Da 'kyar na rarrafa na fita zuciyata cike da damuwa da tunanin faruwar al'amarin.

Sai da na samu saukin aiki tukkuna na kira wayarta nake tambayarta, duk da ina da tabbacin ita ta dauki kudin, amma sai na tsinci kaina da tambayarya, kawai sai ta fashe da kuka da fad'in" Kullum idan na nemi abu na rasa a gidan sai na dinga zarginta, ina d'ora mata sata, alhalin ita bata kwana a gidan ba, gaskiya ita ta gaji da wannan abu.

Kashe wayar kawai nayi na rabu da ita, domin dai gabad'aya kaina ya k'ulle na rasa irin tunanin da zanyi.

Ko da na shedawa mahaifiyata halin da ake ciki, ta ce nayi hakuri kada na sake maganar, abunda ya samu ayi haka.

Na ce"Mama yanzu haka za a kai yarinyar nan gidanta babu gado? hakan kamar bai da ce ba, kuma kin ga daga b'angaran mu ake samun matsala! a kowane lokaci bai kamata a sake d'aga bikin nan ba"

Ta ce" Ba za a d'aga ba insha Allahu. za a yi abinda ya sawwa'ka idan ya so da kud'in sadakinta sai a saya mata katifa, ni kuma da 'yan uwana za mu had'u mu saya mata labulaye da kayan kicin, zanin gado da sauran abubuwan bukata"

Na ce" Amma Mama ba haka naso ba wallahi, kuma ina da tabbacin cewa Fatima ce ta d'auki kudin nan.

Ta ce" Tunda na ce ka bar maganar to kada ka sake tayar da ita.

Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Shikkenan Umma Allah yasa mu dace." Ta amsa da "Ameen ya Allah.

To a takaice dai haka aka aurar da Sadiya babu gado ballanatana kujeru, hakan yayi wa zuciyata ciwo sosai da sosai, amma na kudire a raina cewa; duk sanda na samu faraga zan sharewa yarinyar hawaye.

Sosai na shiga takatsantsan! da Fatima bana yarda na shigo da kudi gidan, ballanatana ta gani ta d'auka, amma ban d'auki matakin komai a kanta ba, kawai na zuba mata idona, cikin zuciyata nake mata adduar shirya a gurin Allah.

Cikin watannin da suka gabata, gabad'aya ta sauya hallita lokaci guda tayi wata irin 'kiba da haske na d'aukar magana, fatar jikinta tayi luwai! bayan manya-manyan sutturun da take sanyawa, haka zan dawo gidan na samu tayi abinci mai rai da lafiya, bayan kayan d'aki da ta sanja sabbi irin na company, abin ya dame ni sosai! na zaunar da ita ina tuhumar ta, ta ce" Business suke da Jamila.

Na ce "Wane irin business ne wannan da yake kawo muku wannan mahaukatan kudi haka? kuma bana raba ki da Jamila ba?"

Ta ce" Order kayan kicin mu kayi daga india, kuma babu yanda za a yi na rabu da Jamila domin abokiyar rufin asiri na ce."

Na ce" To naji a ina ki ka samu kud'i? har ki ka fara kasuwanci?"

Shuru tayi. Na ce" Yanzu kin tabbatar da zargin da nake miki ko?"

Ta'be baki tayi ta ce" To meye ai gashi nan, ni da kai muna cikin jin dad'i! lokaci guda rayuwarmu ta sauya, amma da ka tattare kud'i zakaje kayi gwaninta"

Takaice ya rufe lullubeni, na ce" Saboda na rufawa 'kanwata asiri shine gwaninta, Fatima anya kuwa kina da hankali?"

D'auke kanta tayi tana surutai! zuciyata tayi zafi sosai! amma sai na daure ban yi mata komai ba na tashi na bata gurin, zuwa nayi na kwanta domin samun nutsuwa, kwana biyu sam bana jin dadin jikina, ciwon kai mai tsanani da jiri, dole dai ko ina so ko bana so naje asibiti likita ya duba ni.

Likita ya tabbatar min da cewa jinina ya hau sosai! dole ne kuma na kiyaye shiga damuwa da gujewa duk abinda zai janyo min 'bacin rai! kuma na dinga samun isashen bacci!

Banyi mamaki ba, domin na san halin da nake ciki zan iya kasancewa a jerin masu 'karancin lafiya, na tabbatar da cewa; hakan baya rasa nasaba da tashin hankalin da Fatima take jefe rayuwata a ciki.

Akan magani aka d'ora ni, na dawo gida ina bin ka'ida, amma na san hakan bashi ne maslaha ba, samun lafiyata yana da ala'ka da Fatima.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 75&76

To ko da taga ina shan magani, bata tambaye ni dalili ba, sai rama nake a tsaitsaye, babu abinda ya dameta, sai narka 'kiba take tana gogewa tare da tu'ammali da sutturu na alfarma, babu wanda zai ga Fatima a lokacin ya ce ita d'in matata ce domin tafi kama da matan hamshakan masu kudi sosai abin yake damuna tare da cin rai! don haka sai na samu iyayenta da maganar, kan cewa su binkici a ina take samun kud'i, domin abinda take yayi yawa.
Chapter 8 · 0% Book details