← Book details Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 20

Sashe 12

Majanuni Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ya rigata magana da fadin" Wannan ba hujja bace Shahida, na san abinda kike tunani, amma bari kiji wani abu, ko kin fi haka rauni ko nakasu! wallahi zan aureki, domin ni bana bukatar kyau! ko wata d'aukaka! tarbiya nake buk'ata da amana, kuma na samu da yardar Allah, saboda haka kisa a ranki cewa; ni naki ne har abada kuma uban 'ya'yanki."

Kallonshi nayi, tare da girgiza kaina, domin ni abinda nake dubawa daban da tunaninsa.

Ta ce" Nima hankalina ya kwanta da yarinyar nan Alhaji Habu, saboda haka kayi k'ok'arin rarrashinta domin ta samu nutsuwa."

Ya ce." Insha Allahu Hajiya."

Ta kalleni tare da cewa" Shahida ni zan tafi amma don Allah kada ki bijirewa auranan, kiyi hakuri ki zauna tare damu kinji ko"

Tausayi ta bani sosai! na ce" To shikkenan Hajiya nima na gode sosai"

To tunda ya fita bai sake shigowa ba sai bayan isha'i, ya shigo ya same ni kan dadduma na idar da sallah, ina addu'a.

Zama yayi kusa dani tare da d'aga hannunsa sama yana fadin" Allah ka mallaka min zuciyar matata ka bamu zuria masu albarka.

Ina jinsa yana ta addu'oi, nima ina yin nawa, na shafa a fuskata, shima shima ya shafa, ya kalle ni da murmushi na mussaman a fuskarsa, babu yabo babu fallasa na gaishe shi, ya amsa a lokacin da yake 'kok'arin rike hannuna. da sauri na janye, na tashi na bar shi a gurin.

Beyi zuciya ba, ya sake zuwa kusa dani ya zauna tare da rungumo ni jikinsa, kawai sai na fashe da kuka! ina ture shi! " Ka matsa daga kusa dani"

Ya ce" Me yasa zan matsa bayan ke din halalina ce''

"Ni ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba, domin baka cikin tsari na" Na fad'a tare da cire hannunsa da d'ora a saman cinyata.

Ido ya zuba min da alamun damuwa a tare dashi ya ce" Menene abinda ba kya so a tare dani?"

Shuru nayi masa, ya ce" Kada fa ki butulcewa Allah Shahida."

Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Nafiso na auri daidai da ni, mai rauni da rangwamin gata.

Ya ce"Sai kuma Allah ya baki Saddiku a matsayin miji shin ya za kiyi kenan? da yanayi na 'bacin rai yayi maganar.

Tashi nayi na shiga d'aki na kwanta tare da tsirawa rufin d'akin ido! hawaye masu zafi suke zuba, shin ya zanyi ne? na san Ubangiji ya gama yi min komai da ya mallaka min babban mutumin mai daraja irin wannan, amma a jikina nake jin kamar akwai abinda zai faru mara dad'i dangane da auransa.

Shigowarsa d'akin yasa nayi saurin goge hawayena, ya ce" Kina yi min asarar hawayenki wanda ya fi gold tsada a gurina, bari kiji wallahi duk abinda za kiyi ba zan rabu dake ba, domin ni naga matar aure.

Kallonsa nayi a lokacin da yake maganar, nan naga tsagwaron sona a cikin k'wayoyin idanuwansa.

Ya ce" Yini guda duk kin rasa sukuni! kinyi rama ta ba gaira ba dalili, kowane bawa fa, da kaddararsa, ke taki k'addarar auran dattijo wato Saddiku, kuma kin shigo hannunsa kenan, domin ba zan iya rayuwa babu ke ba.

Na ce" Aikuwa ba zaka samu nutsuwar da kake bukata ba, tunda dai ni bana 'kaunarka, tausayinka kawai nake ji, kuma ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba.

Murmushi yayi kafin ya ce" To tunda akwai tausayi ni na tabbata da akwai k'auna, amma mu je zuwa dai tunda kin fad'i haka.

Juya masa baya nayi tare da rintse idona! sai kawai na jishi a kusa dani, yana k'okarin rungume ni! na ture shi da karfi! na tashi zaune tare da matsawa 'kuryar gado!

Kallo na yayi na minti biyu kafin ya ce" Kin san dai hukuncin matar da take 'kauracewa mijinta ko?"

Gabana ya fad'i! da jin maganarsa.

Cikin rawar murya na ce" To me kake nufi?"

Murmushi yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa ya ce." Bana nufin komai sai alheri, ko zan kar'bi hakkina ba yanzu ba sai zuciyarki ta aminta dani, amma yanzu ina so ki bani hankali domin cigaba da warware miki abinda ya faru da rayuwata wanda baki sani ba, ina so na baki labarin d'aukakata da kuma cigaban labarin zaman aure na da matata ta biyu.

Jin haka yasa na kalle shi da fad'in" Ya sunanta?"

"Zinaru" yafad'a yana kallon fuskata. baki na ta'be da fad'in" Yunwa nake ji yanzu" sauka yayi daga gadon, ya kama hanyar fita ba tare da yace min komai ba, nima na bishi da kallo tare da nazari da tunanin abubuwa da yawa a tare da ni, da shi.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 80&81
Kafin nayi magana sai ga ta fito, kamar wacce take la'be, ta tsaya 'kerere! a kan mu, ta nuna Hajiya da yatsa tare da fad'in'' To magulmaciya tsohuwa mai zuwa lahira da 'ko'kon dambu, duk na ji abinda ki ke fad'a masa sharri za kiyi min Allah ya isa tsakani na dake." tana wata irin girgiza irin ta rashin mutunci take maganar.

Kaina ya d'aure mutu'ka! na kalli Hajiya dake zaune idanuwanta sun ciko da ruwan hawaye sakamakon cin mutuncin da Zinaru ke mata, zuciyata ta cika da tausayinta, na kalle ta har yanzu tana tsaye a kan mu babu alamun risina a tare da ita, raina a 'bace na tashi tare da tsinka mata mari a fuskarta, cikin takaici da bak'in cikin abinda ta aikata na ce" Hajiyar tawa ki ke kira da magulmaciya saboda baki da mutunci."

"To idan ba magulmaciya ba mai zai sanya ta zaunar da kai tana shirya maka magana wallahi duk abinda ta fad'a sharri tayi min" Ta karasa maganar cikin k'okarin kare kanta.

Na ce" Wallahi ki iya bakin ki, muddun kina bukatar zama da ni to dole ne sai kin daraja Hajiyata mutu'kar kuwa ba haka ba, to zamu sa kafar wando daya dake.

"To sai me ? tafad'a tana buga cinya kafin ta cigaba da cewa; kai bari ka ji wallahi ba zan zauna kana taka ni ba, al halin na san da dukiyar d'an uwana kake fankama, akan me? wannan tsohuwar zata sanya min ido a gida har tana fada maka cewa; ina fita yawo to 'karya take munafuka ce"

Jikina na tsuma! na sake kai mata wani marin, ta kauce ban same ta ba, Hajiya ta tashi ta rirri'ke ni tana hana ni dukanta, ganin haka yasa tayi mana kallon banza tare da jan dogon tsaki! ta shiga daki ta bugo kofar da karfin gaske!

Zubewa nayi kan kujera tare da dafe kaina zuciyata in ban da zafi babu abinda take, Hajiya ita ta dinga tausar zuciyata har na samu sukunin tafiya ofis, amma duk da haka da 'bacin rai na yini, har sai da abokina Alhaji Faruk ya fahimci ina da damuwa. ya matsanta min sai na sanar dashi halin da ake ciki.

Ya ce" Ban yi mamakin faruwar wannan abu ba, domin dama can yarinyar bata da mutunci, sai dai shawarar da zan baka shine ka kula sosai, kuma ka sanya matakan tsaro a cikin gidanka, gudun kada ta je ta dauko wani ciwo ta kawo maka gida, ko kuma ta d'auko cikin wani ta kawo maka.

Na ce" Aboki na wallahi ni duk a tunanina yarinyar nan, ta shiryu ta daina duk wasu halaye marasa kyau! wannan dalilin ne ma ya sanya na saki jikina da ita har nake mu'amular aure da ita, ashe yaudarata take, tana ha'inta ta.

"Kayi hakuri abokina kaddara kowa da irin tasa amma ni kaina ina jajanta maka auran Zinaru, sai dai nayi maka alkawari insha Allahu, zan sanya ka cikin addu'ata, Allah ya kawo maka mafita.

Jikina a sanyaye na amsa da "ameen suma ameen abokina.

Gabad'aya daina shiga sabgar ta nayi, sannan kuma na saka matakan tsaro sosai a gidan, duk a k'okarin na ganin na kare martabar aurena.

Hakan da nayi sai ya sanya ta cikin damuwa mai tsanani, ashe kullum idan na fita zuwa take har d'akin Hajiya ta ci mata mutunci iya son ranta, watarana dai Shukura ta kasa daurewa ta mayar mata da martani, tunda a lokacin yarinyar tana da shekara goma sha biyu, ta fara sanin ciwon kanta.

Aikuwa kamar jira take, sai ta zari wayar redio ta kama yarinyar ta dinga dukanta kamar wacce Allah ya aiko, Hajiya tayi-tayi ta 'kwace yarinyar daga hannunta ta kasa, k'arshe ma ta dinga had'awa da ita tana duka.

Sosai ta farfasawa yarinyar jiki, da wayar redio, amma abin mamaki! ina dawowa gidan ta same ni tana kuka tare da fadin" Shukura tayi mata rashin kunya har da zagi, na tambayeta dalili sai ta fara kame-kame, ganin haka yasa na ce ta je zan d'auki mataki akan hakan.

Lokacin da Hajiya take yi min bayanin abinda ya faru. sai ta fito ta zauna duk abinda Hajiyar ta fad'a sai tace 'karya ne ba haka bane, na kalle ta da tsananin b'acin rai a tare dani na ce" Zinaru idan na sake jin maganarki sai ranki ya 'baci." shuru tayi tana zabgawa Hajiyar Harara.

Hajiya ta gama yi min bayanin duk abinda ya faru, raina ya 'baci sosai tunda na fahimci cewa babu laifin tsaye bare na zaune ta kama yarinyar da duka har sai da shatin waya ya fito a jikinta, na ce" Wallahi Zinaru, duk sanda ki ka sake dukan yarinyar nan sai na rama mata, domin ita d'in ba jakarki ba ce, da zaki kama duka sai kace an aiko ki, ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe.

'Budar bakinta sai ta ce" A wai! to ai 'yar taka ba cikakkiya bace, domin ita da shegiya ba su da maraba, duk ina da labarin komai, tsohuwar matarka ta je yawo can saudia ta d'auko cikin shege, ta haife ta kawo maka, saboda kai shakatafe ne kazo kana murna, wannan yarinyar duk ina da labarin komai a kanta"

Hajiya ta fashe da kuka tana fadin" Ki ji tsoron Allah Zinaru, ki bi duniya a sannu."

Tsaki ta ja mana kafin ta tashi ta shige daki ta bar mu cikin damuwa da tashin hankali.
Chapter 12 · 0% Book details