← Book details Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jama'ar dake tsaye a gurin suka shiga mamakin al'amarin, Baba tace."Kun dai ji da kunnuwanku abunda take fada, Shin kuna da tabbacin Jamilu auranta zaiyi ko kuma yaudararta yazo yayi sanin kanku ne kafin yazo gurinta ya yaudari 'yan mata da yawa a cikin unguwar nan to me zai sanya ina ganin kashi da rana na taka auran Jamilu bashi da fa'ida tunda shi bashi da hali uwa uba kuma bashi da sana'a"

D'aya daga cikinsu mai suna Huwaila tace."Ki yi hakuri ki barwa Allah al'amarin domin kuwa shi aure nufi ne na Allah kuma naji kina maganar Jamilu bashi da sana'a Aa yana da sana'a domin shago guda ne dashi a kasuwar wambai kawai dai aure ne be yi ba ya tsaya shiririta amma ki bari ni nayi miki alkwarin zuwa gidansu domin mu tattauna da mahaifiyarsa idan da gaske yake to ya fito ayi magana idan yana yaudaran yaran mutane to mu ba zai yaudare mu ba."

Baba Asabe ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Huwaila Na gode Allah ya jishshemu alkairi." Huwaila ta amsa da ameen kafin ta rungume Mariya tana rarrashinta.

Koda Huwaila ta samu mahaifiyar Jamilu da maganar kai tsaye tace ita sam bata ma san da maganar ba, amma idan ya dawo zata tambayeshi duk yanda ake ciki zata zo har gida tayi mata bayani.

Bayan sunyi maganar da mahaifiyarsa ya nuna mata shi sam be san da wata Mariya ba ballantana ya je neman auranta saboda haka ta daina yarda da jita jitan mutane akansa aure nufi ne na Allah idan lokacinsa yayi to ko yana so ko baya so sai yayi.
Sai jikinta ya mutu tace."Anya Jamilu ba zaka nemi maganin baki ba kuwa na fahimci cewar mutanan unguwar nan sun sanya maka ido."
Dariya kawai yayi ya shashantar da maganar.

Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin ya zauna yayi dogon tunani akan al'amarin a zahirin gaskiya Mariya bata da wani kyawun azo a gani amma kyawun jikinta yana mutukar rud'arsa yana masifar son cikakkiyar mace amma kuma yana so ya dawo gida yaga kyakykyawar fuska nayi masa sannu da zuwa.
Murmushi yayi lokacin da ya tuna ai Ubangiji Allah ya hallata masa auran mace fiye da d'aya saboda haka zai auri Mariya saboda kyawun jikinta nan gaba kuma idan ya samu fara kyakykyawa sai ya aura ya samu ta shiga cikin taron jama'a wacce zai sanya a gaban mota yana zagaya gari da ita.

Ya shedawa mahaifiyarsa shawarar da ya yanke kan cewa taje ta shedawa Huwaila cewa Eh tabbas da gaske yake zai auri Mariya domin ma yanzu ma shirye-shiryen kawo kudin aure yake.

Farin ciki ya lullubeta aikuwa ba taja dogon lokaci ba taje ta shedawa Huwaila halin da ake ciki Huwaila cike da farin ciki ta yafa mayafi domin zuwa ta shedawa Baba Asabe abinda yake wakana.

Baba Asabe addua kawai tayi ta barwa Allah amma daga can 'bangaran 'yan uwan Malam Almu an dan samu matsala domin sun so su hana faruwar al'amarin mussaman da sukayi binkice suka tabbatar da munanan halin Jamilu wanda ya zama abun gudu ga ko wane managarcin mutum.
Jamilu yana ganin haka sai ya shiga musu facaka da kudi lokaci guda ya toshe musu baki.
Kuma ba'aja dogon lokaci ba akayi komai a ka gama. amarya ta tare a gidanta dake unguwar ja'in.

Jamilu ya ga fa'idar auran Mariya domin daga sanda aka daura auransa da ita k'ofofin samu suka bude daga gareshi Allah ya albarkaci kasuwancinsa, a maimakon ya nutsu ya yi abinda zai taimaki rayuwarsa ai sai kawai ya hau shiririta da shirme, burni yake sosai ya sayi sabuwar mota kana kuma duk bayan wata biyu yake fitar da tufafinsa ya zuba wasu takalma da huluna gami da agogona kamar hauka a dakinsa, turare kam be yarda da mai arha ba mai tsada yake fesawa, Mariya tana ganin ikon Allah domin duk irin shawarar da take bashi baya dauka idan ta matsanta masa sai ya rufeta da fada da fadin kudinta ne ko nasa! Haka ta naji tana kallo ta zuba masa ido sai dai labarin duk abinda yake aikatawa a gari yana dawowa kunnanta tana da labarin yanda yake kashewa matan bariki kudi.

Sosai al'amarin yake cin ranta gashi har sunyi shekara da aure amma babu labarin haihuwa ta fahimci kuma shi sam abun bai dameshi ba harkar gabansa kawai yake.

Ta sameshi da maganar tana so ita dashi suje asibiti a dubasu domin a tabbatar musu da lafiyarsu.

Yayi funfurus! ya ce shi babu inda za shi lafiyarsa lau don haka kada ta 'kara yi masa maganar zuwa asibiti.

A ranar taci kuka ta koshi kuma yanzu ta fara nadamar auranta dashi dama wannan badakalar mahaifiyarta take guje mata, yanzu da kunya ta tunkareta da maganar domin kuwa tun farko itace ta za'bi auransa dole tayi hakurin zama da mugun halinsa.

Haka ta cigaba da hakuri yau fari goma baki don ma dai yana kokari ta fannin ci da sha daba don haka ba da ba zata ganu ba.

Tana kokarin warware matsalarta sai wata ta matsalar ta shigo domin kuwa mijin nata aure ya rakito ashe tuntuni har an kai kudi dasa rana bata sani ba sai ana saura kwana biyu daurin aure yazo ya ajiye mata leda viva da kayan fadar kishiya a ciki.

A ranar kwanan kuka tayi ta kudiri aniyar gari na waye wa zata tafi gidansu domin kuwa ba zata iya ganin wannan ba'kin cikin ba.

Yana d'akinsa yana shirin fita kasuwa ta fita daga gidan, koda ya fito yaga bata nan be wani damu ba dama yayi tsammanin faruwar haka, aure zai yi babu wanda ya isa ya hana shi.

Baba Asabe ta rufe idonta tace sam! bata yarda ba don haka tayi maza ta tashi ta koma dakinta ai duk wanda ya sayi rariya ya san zata zubda ruwa don haka ita bata da gurin kwana.

Haka nan tana ji tana gani ta koma gidan Jamilu koda ya dawo ya sameta a gidan, a maimakon ya rarrasheta ai sai ya tsiri gaba da ita ya dai nai mata magana har aka daura auran baya kulata.
Ta sake shiga halin ni 'yasu ta ko'ina babu sassauci sai ta mayar da hankalinta gurin ibadah da ro'kon sauk:i daga rabbis-samawati.

Jamilu da amaryarsa suka dinga sheka amarci ayi wanka tare aci abinci a tare sannan kullum da daddare idan ya dawo daga kasuwa ya sata a gaban mota su tafi su zaga gari ko ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba.

Amarya Hafsa ta dinga jiji da kai a gidan tana zubar da habaici ita ga matar da akeso, ita kuwa Mariya ta tattara komai ta barwa Allah ta zuba musu ido.

Aikuwa tafiyar ba tayi nisa ba amarya ta samu ciki, yana fahimtar haka sai yaje ya samo mata maganin zubar da ciki ya tsaya a kanta sai da tasha. A daran ranan cikin ya zube. Taci kuka ta koshi domin ita taso ta haihu ko don tayi wa Mariya gadara da hujja.

Koda ya fahimci amaryarsa tana da saurin da'ukar ciki sai ya daina kusantarta kai tsaye sai yasa kwaroron roba(condem) sannan yake auratayya da ita, Hafsa amarya ranta ya b'aci mutuka sai ta daina amincewa dashi, aikuwa be ji kunyar ci mata mutunci ba domin tsakar gida ya fito ya dinga zazzaga mata tujara da fadin." Dama lalurace tasa ya aureta ba wani gamsar dashi take ba ta dubi matarsa Mariya cikakkiyar macace me zai yi da ita idan ba kaddara ba.
Hafsa ta dinga kuka tana mamakin halin d:a namiji.
Ita kuwa Mariya ba tayi mamaki ba domin ta san abunda yafi haka zai iya aikatawa ita tafi kowa sanin halinsa

Tun daga ranar ya mak'ale mata ya dinga rarrashinta da kalamai masu dadi har da fadin kaddarace ta sa shi aure amma me zaiyi da wata bayan yana da ita.

Ita dai jinsa kawai take ta san ba komai yakewa dadin baki ba sai ni'imar da Allah yayi mata duk daran duniya baya iya hakuri sai ya kusanceta.

Tsayin wata biyar haka rayuwar take tafiya Jamilu ya watsar da amaryarsa kamar bashi ya ajiyeta ba, sai kawai ta tunkareshi domin taji matsayinta, ya kalleta sama da kasa kafin yaja mugun tsaki ya ce."Wallahi ban san dalilin da yasa na aureki ba dubeki don Allah guntuwa dake hanci k'ato in banda farar fata baki da komai."

Hafsa ta fusata! ta daga masa hannu da fadin." Kaga ya isa haka ka fada min matsayina a gidanka dama ai kafin na aureka sai da aka fada min halinka amma tsautsayi yasa na aureka.

Ya sosa gemunsa yana mata wani irin kallo ya ce."Kwad'ayin abun duniya ne yasa kika aure ni ai tun kafin naje neman auranki na gane ke din mayyar kudi ce shiyasa na rud'eki dasu kuma na samu nasara, saboda haka yanzu baki da wani amfani a gurina kije na sakeki saki biyu."

Hawaye suka k'wace mata ta ce."Sai Allah ya saka min wallahi kuma abunda kayi min sai anyi wa 'yarka."

Ko a jikinsa ya rubuta mata saki a takarda ya bata harda kudi dubu biyar akan takardar, a fusace! ta watsa masa kudinsa ta fita daga d'akin tana kukan bakin ciki.

*TAFIYAR TANA DA TSAYI😃*

Ku karanta littafin a sannu a hankali, amma kada ku manta na fada muku cewa nayi amfani da salo biyu gurin rubuta littafin, sai a nan gaba za ku fahimta

*BINTA UMAR ABBALE*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi Join domin samun damar karanta littafi na daya

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*13&14*
Ya hujaj! bayan ya rabu da amaryarsa da wata uku sai ya hango wata 'yar dumur-dumur! mai cikar kirji fara tas da ita amma ba ta cika kyau a fuska ba dan Mariya ma ta fita kyawun fuska, to da yake yana da kudi a hannu bai sha wahala gurin siye zuciyar Talatu ba, dama ubanta talaka ne basu da komai koda yaje neman auranta basu wani tsananta binkice ba suka dauki 'yarsu suka bashi.
Chapter 8 · 0% Book details