← Book details Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 36

Sashe 4

Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya mike zaune da fadin." Idan kika matsanta min wallahi zan ha naki ni nace kije zan baki idan na fito sanin kanki ne bana san takurawa."

Ta yi jim tana kallonsa kafin ta gyada kai da fadin." Na kawo maka abincinka ne.?

Sai da ya mula tukkuna ya ce."Aa ki bawa Jamila da Shahida suka 'kara ni na koshi."

Ba tare da tace komai ba ta juya ta fita, koda ta fito daga dakin a maimakon tayi abinda yace kai tsaye kicin din ta nufa ta dauko abincin nasa tasa a gabanta ta dinga ci sai kace jaka, Walida dake sud'e hannu tace."Talatu d'an k'ara min wallahi ban koshi ba."

Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kai loma bakinta, yarinyar dake mara kunya ce ta yatsine fuska da fadin." Talatu ki dai ci a hankali kada ki 'kware wannan loma haka."

Bud'e baki tayi za tayi magana aikuwa ta shaki shinkafa ta hanci tari ya sar'ke ta ta dinga yi hawaye na zuba, yarinyar ta tashi ta bar gurin ba tare data debo mata ruwa ba.

Shahida da Jamila haka sukaci abincin ba tare da sun 'koshi ba, suka fito domin wanke hannu nan suka ga Talatu tayi wurjajan ido yayi jawur har yanzu da sauran tarin amma saboda zulama bata daina cin abincin ba.

Shahida ta banka mata harara ta wuce dama duk sanda tazo gidan abinda ke shiga tsakaninsu kenan harar juna, sai taso take gaishe da ita, Hadiza ta fito daga d'aki Talatu tace."Kinga 'yar iskar yarinyar nan saboda ban zuba mata abinci ba take hararata.

Hadiza tace."Take harararki kamar sa'arki." Tace."Au! keda baki ta'ba gani ba? ai a duk san da zata zo gidan nan hararace take shiga tsakaninmu."

Bagazan! bagazan ta nufi inda take ta juyo da ita suka fuskanci juna, murya ta d'aga da fadin." Don Uwarki mahaifiyarmu sa'arki ce?"

Jamila tace."Hadiza neman fitina bashi da amfani me kuma tayi miki?

Ta juya tana yi mata bayani yayin da ita kuma Shahida ta juya inda Talatu ke zaune ta dinga watsa mata muguwar harara tunda ta lura da abinda bata so to ta daura d'amarar 'bata mata rai.

Talatu ta rike ha'ba da fad'in.'' Ni kike harara don Ubanki! ta dauke kanta tana jan tsaki tare da niyyar barin gurin.

Hadiza ta fizgo kafad'arta tana nema ta kai mata duka, sai ta rike mata hannu cikin yanayin maganarta tace."Hadiza ki kiyaye ni wallahi ni nafi karfin ki dake ni."

Ta fizge hannunta tana d'ura mata ashar!! Ya fito d'aga daki da yanayin bacci a tare dashi ya ce." Baku da hankali ne? sukayi shuru ya kalli Shahida da fadin." Me yasa duk lokacin da ki kazo gidan nan sai anyi rigima dake?

Ido ta zuba masa, yaja tsaki da fadin." Ana magana kin tsare mutune da ido kizo ki tafi inda ki kafi wayo."

Da yake da 'karfi yake maganar duk taji komai sai tace." Ai na dawo gidan ubana da zama."

Talatu ta zabura! ta mike tsaye da fadin." A'ina.? Babu tsoro tace." A nan."

Jikinsa ya mutu ya ce."Kinyi mata laifi ko?Fashewa tayi da kuka ta durkushe a gurin!.

Talatu cikin masifa ta ce."Wallahi ko kukan jini za kiyi baki da gurin kwanciya a gidan nan aikin banza kawai."

Ya kalleta da fadin." Kin san dai 'yata ce ko?"

A fusace! Tace."Na sani amma wallahi ba zan zauna da ita ba."

Ya girgiza kai da fadin.'' Duk lokacin da nayi ra'ayi 'yata zata dawo hannuna da zama."

Tana numfarfashi! tace."Ni kuma a ranar zan tattara kayana na bar maka gidanka domin kuwa ba zanyi kishi da uwarta nazo nayi da ita ba.

Murya ya d'aga gurin kiran sunanta, ta d'ago kai tana kallonsa fuskarta gaje-gaje da hawaye,

Ya ce."Tashi muje ki fad'a min laifin da ki kayi mata."

Ta mike tana share hawaye tabi bayansa zuwa dakinsa, kallon banza Talatu ta bisu dashi tayi k'wafa tana girgiza kanta.

Duk abinda ya faru ta sheda masa tana kuka, ya ce."Kiyi hakuri kinyi sara a bakin ga'ba matsalar Baba Asabe kudi za'a biyata kud'inta"
Cikin izzah! da nuna isa yayi maganar kamar wanda yake da burin biyanta kud'in dawainiyar da tayi masa daga farko har 'karshe.

Yasa babbar rigarsa da fadin." Tashi mu tafi." Ta mike da sauri ta fito, shima ya fito yana kokarin kulle kofa tazo ta ta rike k'ugu tare da jan tunga a gabansa.

Hannu yasa cikin aljihu ya zaro sabbin 'yan dubu-dubu uku ya watsa mata.

Ta tsuguna tana tsincewa da fad'in." A banza dai duk abinda za kayi ni na rufa maka asiri."

Ya gyara zaman hularsa ya kama hanyar fita ba tare da ya tanka mata ba.

Ta kalli Jamila dake kan rijiya a zaune ta ce." 'Yar uwata na tafi na gode da zumunci."

Jamila tana murmushi tace."To Aunty Shahida ki gaishe da Baba Asabe da kyau."

Tace." Za taji da kyau." Hadiza tace."Banzaye kawai wannan munafurcin naku babu inda zashi." babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Shahida tabi bayan mahaifinsu ita kuma Jamila ta shige daki tana jiyo irin zagin da sukewa Shahida tamkar maguzawa!
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO...
_____

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
Kuyi join domin samun damar karanta littafi na daya.

*Marubuta*
_Nimcy luv (Sarauta)_
_Hassana Bamalli_ _(OmApanan)_
_Sa'adatuBintuAbdullahi_
Ina godiya 'kwarai💯

Kyautar feji zuwa ga:
_*Ummul-Khairi Shaik*_ _*Muhammad (Kairatu)*_
Binta tana godiya da k'auna tare da k'warin gwiwa🥰

*7&8*
Jamilu Ya hujaj! mutum ne mai fara'a da wasa da dariya shiyasa yake da jama'a yara da manya duk inda ya gifta za ka ji ana fadin "Ya Hujaj! Shi kuma ya dinga washe baki kenan yana dariya idan da kudi a jikinsa ko nawa ne sai sun k'are domin bai iya gwaninta ba kyautar dubu biyar a gurinsa ba abu ne mai wahala ba, mutuk'ar yana da kudi to na bajinta ne amma fa gidanshi sai godiyar Allah domin da k'yar! yake bayar da kudin awo watarana matar gidan itace take cefane da yake tana awarar siyarwa shiyasa suke raba daidai.
Da yawa mutane suna mamakin yanda yake sanya manyan sutturu da bajinta a waje amma 'ya'yanshi suna yawo babu sutturar arziki babu makaranta mai kyau, uwa uba kuma matarsa na sana'ar siyar da awara wannan dalilin ya sanya wasu ke zaginsa suna ganin arzikinsa ya tashi a banza tunda ya kasa sauke nauyin iyalinsa sai dai ya fita yana neman suna a gurin jama'ar gari.

A zahiri sana'ar sa wacce kowa ya san shi ida ita sayar da takalma a cikin kasuwar wambai shago guda ne dashi yake bada sarin takalma na roba dana fata amma irin wanda akeyi a cikin kasuwar bayan wannan sana'ar tashi akwai wata wacce ya jima yanayi a 'boye kuma itace take kawo masa ma'kudan kudin da yake facaka dasu.

Yau zaka gan shi da sabuwar mota amma idan aka kwana biyu sai gan shi cikin a daidaita sahu ko kuma a kafa yana tafiya idan ka tambayeshi sai kawai yace motarsa tana gareji ta samu matsala 'karya kamar kudin guzuri a gurinsa, wannan dalilin ya sanya jama'a suke d'aukarsa a matsayin mai rariyar hannu ko kuma d'an bariki har yanzu babu wanda ya hasaso irin sana'ar dake sanya abubuwan hannunsa suke salwancewa.

Ko a cikin a daidaita sahun ma sai jan 'yar tashi yake da wasa yana tsokanarta wai lallai sai ta fada masa sunan saurayinta.

Ita dai Shahida murmushi kawai take tana mamakin halayyar mahaifin nata, kwata-kwata baya jin nauyi da kunya idan yana wasu abubuwan.

Da yake yamma tayi ya sanya titin ya cunkushe da ababan hawa bayan jama'ar dake kai kawo a gurin. Duk wanda yake cikin garin *KANO* ya san cewa titin *JAKARA* yana bukatar gyara daga mahukunta, amma anyi shakulatun 'bangaro dashi duk da irin gudumawar da matasan unguwar ke bayarwa a lokocin za'be amma ko wane d'an takara daga zarar ya samu abunda yake so sai ya manta da wad'anda suka sha masa wahala. mai adaidaita sahun yace."Alhaji ko zaku sauka anan ne yamma tayi gashi gowslow nan yaki sauki.
Yace."Aa akwai sauran tafiya kayi hakuri ka shiga damu ciki, Yace."To shikkenan amma zaka 'kara min wani abu." Yace."Babu damuwa."

Da karfi! tace."Subahanallahi." hankalinsu ya dawo kanta kokarin fita take daga babur din ya rike hannunta yana tambayarta, ta nu na masa shi wanda yake can tsallaken titi wani mai babur ya kusa buge shi jama'a har sun taru a kansa.

Hawaye ta share tana fadin." Allah ya kiyaye da tuni mai babur ya buge shi Allah sarki Baban- baba."

Yace."Ke wai baki da hankali ne kike magana ke kadai.

Mai babur din yace."Alhaji baka lura bane ai mummanan al'amari ne ya kusa faruwa akan wancan mahaukacin dake tsallaken titin can.''

Yaja tsaki da fadin." Ni ai ban lura wallahi ba kaji yanda hankalina ya tashi ba ke ina ruwanki da mahaukaci Shahida."
Yana kallonta yake maganar.

Hawaye ta share da fadin." Haka kawai nake tausayinsa." Tsuke fuska yayi da fadin." Malama shige mota mu tafi bana son shashancin banza a garin tausayi ake cutarku wancan mutumin da ka gani ba mahaukaci bane akwai manufarsa.

Ta share hawaye da fadin." Eh Baba nima bana masa daukar mahaukaci tunda wani sa'in duk abu na masu hankali yana aikatawa rashin galihun da yake cike ne yake damuna, da za'a samu wasu masu imani da tausayi su taimaka masa da abin yi Abbah ka duba fa kaga kayan jikinsa duk daud'a duk sun yage fuskarsa bakikirin takalmin kafarsa ya sud'e ya tsinke kullum karkashin mota yake kwana rana zafi iska ruwa babu wanda ya damu dashi da ci da shan sa."
Chapter 4 · 0% Book details