Sashe 32
Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba.
Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta.
Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi.
Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu.
Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne.
Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan.
Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escorts dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! "Wannan ai shahararran attajirin nan ne da ake nuna fuskarsa a tibi." sake kallonsa tayi a karo na biyu cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara ya nad'a farin rawani a saman hular. as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an.
Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya k'araso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta.
Bai amsa ba sai dai ya yi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa.
Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya.
Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi ciyayi! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske.
A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta.
Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata.
A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta,
Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba.
Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya."
Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta .
Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba."
Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa."
Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya.
Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya."
Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata.
Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?"
Girgiza kanta tayi ta ce." A'a babu komai, sai dai ki zauna ki d'ebe min kewa ai na ji dad'in zuwanki gidan nan saboda zaman kad'aici yana damuna, Shukura kuma ba gwanar zaman falo ba kullum tana daki da waya a hannu."
Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin maganganunta, to shin maigidan bashi da aure ne? ko kuma ba a gidan yake zaune ba? bata da mai bata amsa sai kawai tayi shuru, tare da tsirawa tv ido kallon kawai take amma ba sosai take jin abinda ake fad'a ba.
Cikin riga da wando na bacci ta fito daga d'akinta. ganinta a zaune yasa tayi turus! tana kallonta babu annuri a fuskarta ta kalleta da fadin." Hajiya wannan wacece kuma?" ta fada tana nuna ta da yatsa.
Tana shirin bata amsa ya shigo, duk sai su kayi shiru suna kallonsa, a nutse ya zauna kan kujera yana kallon Shukuran dake tsaya da alamun rashin gaskiya a tattare da ita.
"Kin yi sallah?" tambayar da ya yi mata kenan.
Sai ta hau diri-diri kafin ta ce." Daddy bani da tsarki ai."
Shuru yayi be ce komai ba, da shagwaba ta ce" Daddy don Allah ka bari na je gidan bikin nan, kamar hakan bai dace ba tunda Aunty Samira 'kanwar mommy ce kuma kai ma 'kanwarka ce ka taimaka Daddy don Allah." ta 'karasa maganar tana karyar da kai.
Shuru yayi bai ce uffan ba, ta kalleta da fadin." Hajiya kisa baki don Allah"
Kallonsa tayi da fad'in.'' Alhaji Habu ina nema mata alfarma." Yanda ta fad'i maganar cikin 'kaskantar da kai ya bashi dariya!
Ya ce" Na amince amma ba don halinta ba, kuma ban yarda da kwana ba, aje a dawo."
Tsalle ta buga da fad'in." Daddy na gode Allah ya 'kara girma."
Duk abinda suke tana takure a gurin tana kallonsu, sai dai ba sosai take jin abinda suke tattaunawa ba. ita gabad'aya zaman sa a gurin shi ya 'kara firgitata! ta kasa gane wane yanayi take ciki, haka kawai mutumin yake cika mata ido.
Hajiya ta nuna ta da yatsa da fadin." Yallabai wannan ita ce amaryar Sule fa, wallahi da farko na dauka irin masu zuwa neman taimako ne, sai da ta gabatar min da kanta tukkuna na tuna amma ga dukkan alamu tana da matsalar rashin ji kurma ce"
Kallon da yake mata ne yasa duk ta tsargu! ta kasa 'kwakwkwaran motsi.
A hankali ya kalli Hajiyan da fadin." Ya sunanta?"
"Shahida sunanta, ai na ce na samu abokiyar hira duk da cewa ba ta ji sosai hakan bai zai hana ta d'ebe min kewa ba."
Ya ce." 'Kwarai kuwa nima wannan ne dalilin da yasa na bashi guri a gidan nan, na ce ya zauna saboda ki samu walwala.
Ta ce." Maganar auranka dai shuru Alhaji kullum sai kace kana kan hanya.'' Shukura da sauri ta ce." Hajiya ai daddy ba sabon aure zai yi ba, Mommyna zai dawo da ita.''
Wani irin kallo yayi mata kafin ya mi'ke ba tare da ya ce musu komai ba ya haura samansa.
Hajiya ta ce." Shukura mahaifinki ya tsani ayi masa maganar Fatima mutukar kina so ki ga b'acin ransa to ki ambaci sunanta, wannan k'iyayyar tayi yawa."
A sanyaye ta ce."Wai Hajiya me ya faru ne? na lura daddy ya tsane ta sosai kuma yana da ri'ko! kome tayi masa ai sai yayi hakuri tunda na shiga tsakani, sannan da dangantaka a tsakaninsu."
Ta ce." Shukura labarin yana da tsayi sosai! amma babu shakka Fatima ta yi abubuwa da yawa marasa kyau a can baya! wanda ba su da amfani, saboda haka tayar da al'amarin yana nufin 'bacin ran mu gabad'aya.
A sanyaye ta ce." Shikkenan to Allah ya kyauta." ta amsa da "Ameen ya rabbi."
Shahida na zaune tana satar kallonsu, yanayin fuskokinsu da yanda suke magana a hankali cikin rashin walwala yasa ta gane cewa lallai abinda suke tattaunawa ba mai dad'i bane.
****
To kwana d'aya biyu har ta saba! kullum idan ta tashi za ta gyara gurinta, kafin tayi wanka ta shirya jikinta tsaf! sai ta karya kummalo ta nufi cikin gidan a can take yini tare da hajiya, idan lokacin shiga kicin yayi ta je ta taimakawa masu aiki, sosai Hajiya take jin dadin zama da ita, wannan dalilin yasa ta umarce ta cewa duk abinda take bukata kada tayi 'kwauron baki ta tambaye ta, anan take cin abinci rana da dare. sai tayi sallar isha'i take tafiya gurinta, sai dai abinda yake damunta yanda Shukura ke 'kyamarta! hantara! kyara! wataran harda zagi! kuma kullum ita ke zuwa ta gyara mata d'akinta ta wanke mata bandaki da sauransu, amma bata ta'ba godiya ba, wannan abu yana damunta sosai!
Kasancewar ta samu caji a wayarta yasa ta tura masa text na gaisuwa da kalaman soyayya! tana jiran amsarsa, shuru bai bata amsa ba, jikinta ya 'kara yin sanyi gabad'aya bata da wani kuzari, yau kwanansa tara da tafiya babu wata magana da ta ta'ba shiga tsakaninsu ta hanyar sadarwa.