← Book details Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 36

Sashe 17

Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa.
Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar.

****
Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye.

Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa.

Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa.

*Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*31&32*
"Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar.

Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita.

"Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa!

Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan!

Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali.

Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse?

Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata k'arfin iko na a kan 'ya ta."

Ta ce." Me take nufi to?

Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana."

Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke."

Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa.

Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa.

Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya."

Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!"

Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki."

Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan."

Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta."

Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi."

Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.''

Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa.

Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata.

Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici!

Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba."

Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu."

Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba.

Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan.

Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa.

Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba.

Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!

Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta."

Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu.

Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.''

Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?"

Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku!

"Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun.

'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?"

Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.?

Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci."

Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau."

Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa.

Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu.

Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke......

*****
Chapter 17 · 0% Book details