← Book details Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba.

Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba.

A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?"

Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.?

Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo."

Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka."

Shuru yayi bai ce komai ba.

Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu."

Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin.

Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya.

'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata!

Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka!
Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.?

Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta.

****
"Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj.

Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa."

Ta ce." To za'a fada masa.

Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya.

Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar.
*BINTU*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya*

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*27&28*
Ha'ki'ka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwad'ayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sa ni, Hujaj cikin rashin k'ima da rashin arziki ya nufi gidansa da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an k'wamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin 'kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne su ka yi arangama da mak'ocinsa mai suna Malam Habu yana nannad'e tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, ya yi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai.

Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da ma'kocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya d'auke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari ma'kocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu.

Fitowar ta kenan daga d'aki da buta a hannunta za ta kama ruwa. ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba.

Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu?"

Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa.

Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata.

Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita.

"Wai ana sallama da mai gidan."
Wani ne yaro ne yake magana a gidan.

Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne?

Luf yayi a d'akin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadi'n." Ka ce gashi nan zuwa."

Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin.

Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko?"

Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi."

Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta.

Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya samu Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah."

Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ?"

Yayi shuru bai ce masa komai ba.

Ya girgiza kansa yana hura 'katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni."

Cike da burga da rashin gaskiya ya d'aga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi k'arfin haka."

Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na mai'ko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi idan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali."

Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa mak'ocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj d'aya na k'okarin d'aura masa ankwa a hannu.

"Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.''

Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun mak'aryaci ne, saboda haka hukuma ce zata raba ni dashi."

Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba.

Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da k'ima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari.

Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis da shi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya."

Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba.

Wai a kace labarin duniya ba ya 'buya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar.

Shahida kam d'aki ta shiga ta ci kukanta ta k'oshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani.

***
"Ranka ya dad'e iyakar ha'kuri nayi kawai abinda na ke so ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani."

Officer ya ce." Saminu kaje ku yi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto."

Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure na ke so nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin ma'karyaci ne na daina yarda da maganarsa."
Chapter 15 · 0% Book details