← Book details Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 36

Sashe 2

Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda alamun yana bata hakuri.

Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya.

Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa!

_NA YI AMFANI DA SALO BIYU GURIN RUBUTA WANNAN LABARI, INA FATAN MASU KARATU ZA SU FAHIMTA_

*BINTA UMAR ABBALE*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
Ku yi join don samun dama karanta littafin na d'aya.

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
Na
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO...
_____

_Fatan Alheri ga marubuta Amanar Binta💯🥰_

*Hasinatu (Autar Manya)*
*Sadiya Rimi*
*Binta Garba Saleh*
*Matar ya sayyadi*
*Real Esha*
*Jamy 'Yar kankia*
*Fatima Sunasi Rabi'u*
*Dr Ms Agadaz*
*Ummu Mahir*
*Jasmine*
*Zee Kumurya*
*Shamsiyya Manga*
*Autar Marubuta*
*Indo Aisha*
*Maman Teddy*
*Zahraty Takwara*
*xayyishatu Humaira*

*3&4*
Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a.
Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu.

Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa.

Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta.
Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?"
Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake kansa.

Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?"

Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi."

Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai! Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru.

Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga ne?"

Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba.

Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada mata.

Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace."

Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau."

Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san kansa ba."

Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina.

Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali.

Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da kaina na duba kudina yau koni ko shi duk haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai
"

Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.''

Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da mayafi.

Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin neman gira a rasa ido ni dai na fada miki.

"Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana 'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare a tare.

Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai tayi har ta k'araso inda take, "Don ubanki abinda ki kayi min kenan? ta fad'a tana kokarin kai mata duka! tasa hannu ta kare tana kallonta da idanuwanta da suka taru da ruwan hawaye. cikin masifa ta ce."Tashi muje gurin mahaukacin daya sace min kudina."

Cikin k'okarin kare kanta ta bude baki za tayi magana.......ta buga mata tsawa! wacce ta sanya babu shiri ta mike tabi bayanta tana me cigaba da aibata ubanta wanda bai san abinda yake faruwa ba.

Har suka isa bakin titin tana surutai! jama'arta sai tambayarta suke abinda ke faruwa tana tafe tana basu amsa wasu dariya kawai suke su wuce wasu kuwa bin bayanta suke domin kashe kwarkwatar idonsu.

Yana tsaye da wata jarka a hannunsa da alama gurin yake so ya bari, katamau! ta rike hannunta suka 'karasa gurin da yake.

Tsira musu ido yayi yana kallo. ta kalleshi da niyyar yi masa tijara! dafin idanuwansa ya sanya jikinta mutuwa sai ta gaza furta komai kawai tayi 'kasa da kanta.

Kallon yarinyar ya yi suka hada ido da ido, sai tayi gaggawar saukar da nata idon sakamakon mutuwa da jikinta ya yi a cikin k'wayar idonshi akwai wani sirri wanda shi kanshi bai san yana dashi ba.
Can 'kasan ma'koshi ya ce." Menene ko za ku duba kudin ne?"

Kai kawai ta iya d'agawa har yanzu kanta na kasa ta kasa kallonshi, Baba Asabe tayi namijin kokari gurin Fad'in." Kaga Malam dakata! ba mu yarda da cewa kai mahaukaci bane kazo cikin wannan unguwa ne da mummunar manufa don haka kud'ina dubu arba'in da hudu daka sace wallahi sai ka fito dasu ko kuma ka kwana a police station."

Ya zuba mata kyawawan idanuwansa masu cike da kwarjini.
Dalladi dake bayansu a tsaye yace."Uwar towo wannan magana ki barta kawai ko kin ta'ba ganin anyi sharia da mahaukaci ni na tabbata da cewa Baban-baba ba zai sace miki kudi ba, to yayi me da su? mutumin da ba shi da hankali idan kuma baki yarda ba sai ki dauki mataki amma ina mai tabbatar miki da cewa wahala zaki sha domin kuwa duk inda za ki je babu wanda zai saurareki.

Ta girgiza kai nifa ba zan yarda ba wallahi." Yace."Shikkenan sai kiyi abinda za kiyi." Gurin ya bari bayan ya gama maganarsa, sai kawai ta hankad'a yarinyar kusa dashi da fad'in "Maza shiga k'arkashin motar ki duba min kud'ina idan zai kashe ki da duka bai dameni ba."

Ba tare da wata fargaba ba ta shige k'arkashin motar ta fara dube-dube duk da tasan kudin basa gurin.

Kallonsa tayi da fad'in." 'Yan sanda zan dauko maka yanzu ai gamu ga police station haukanka na 'karya ne" Cikin sauri ta bar gurin.

Yana tsaye ya rungume kirjinsa da hannuwansa idanuwansa a kanta a lokacin da take karkashin tsohowar motar tana dube-dube.

Jikinta ya jik'e da gumi ta fito daga 'kasan motar da 'karfi tace."Baba banga 'kudin b........Had'a ido sukayi yana kallonta jiki a sanyaye tace."Babu kudin a gurin." Kai ya gyad'a mata. sai ta matsa ta bashi guri ganin yana kokarin ture ta, ya shiga ya zauna tare da rungume gwiwarsa still idanuwansa na tsaye a kanta.

Baba Asabe Cike da kwarin gwiwa ta isa station din duk ta zayyane musu abinda yake faruwa.
Koda sukaji abinda take tafe dashi sai suka shashantar da maganar saboda sun riga sun san sharia da mahaukaci sai wanda ya shirya bayan haka kuma duk tsayin watannin da mahaukacin yayi a unguwar ba'a ta'ba kawo musu shi da sunan ya aikata mummunan aiki ba. saboda haka sai suka sallameta tare da kafa mata hujja da cewa ko don gaba ta daina cewa za ta yi sharia da mahaukaci domin kuwa al'kalami ya sauka daga kan duk wani mai matsalar k'wakwalwa.

Jiki a sanyaye ta fito daga station din ranta duk a bace! tana tafe tana zancan zucci da irin hukuncin da za tayi wa yarinyar.

Ita kuwa Shahida tana nan tsaye a gurin gabanta sai faduwa yake ta san halin Baba Asabe akan kudi babu shakka yau sai buzunta.

A jikinta take jin yana kallonta amma tsabar fargaba ta kasa juyawa ta kalleshi ta fahimci a cikin haukan nasa harda kallo a ciki to idan ba haka ba menene abin kallo a tare da ita.

Ya jima yana kallonta kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya hannunshi yasa ya ja gefan hijab dinta.

Cikin wani irin yanayi ta juya suka hada ido. muryarsa ya daga sosai da fadin." Wacece ita?"

Zuciyarta ta karye hawayen da take ta tattalinsu suka su'bce. A raunane tace."Kakata ce."

"Ina iyayenki?" ya fad'a still idonsa na kanta, kai ta sunkuyar jin tana shirin fashewa da kuka, ya sake maimaita maganarsa.

Murya na rawa ta ce." Mahaifiyata ta mutu Babana kuma yana can unguwar Ja'in da matarsa da sauran 'yan uwana."
Chapter 2 · 0% Book details