Sashe 36
Majanuni Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe.
Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai.
Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo."
"Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari.
'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima.
Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana.
Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske.
Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin haushin abinda yayi mata jiya.
Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa.
Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya.
Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita.
Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi.
Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa.
A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?"
Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba.
Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi.
Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa.
Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa.
Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin.
Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba.
Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama."
Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai!
Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba.
"Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido!
A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta.
Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta.
Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba.
Ya ce." Ya hannun naki?"
"Da sauki." tafada a ta'kaice!
Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata.
Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?"
Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta.
Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci."
A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba.
Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai.
Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci."
Ta kalleshi da tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai
Fita tayi daga tsakanin kujerun.
Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba.
Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na.
Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali.
Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba.
Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na.
Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa.
Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba.
Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa.
A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta.
Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita.
Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin.
Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take.