← Book details Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba nufi na ba kenan Abban Aslam, Allah ne mai shiryar da bayinsa amman tayiwu kaine sanadiyar hakan." Aysher ta fad'a cikin sanyin murya.

Shiru Samir yayi yakasa cewa komai, nan dai Aysher taci gaba da bashi shawarwari tare da kwantar masa da hankali har saida yasamu nutsuwa. Kafin ya dubi Aysher yace"ke yaushe zakiyi auren toh? Tunda yaukam nak'ara tabbatarwa da cewa bakya sona, bazaki iya komawa aure na ba."

Dariya Aysher tayi kafin tace"Kacika rigima Abban Aslam yaushe-yaushe nafara karatu? Wata biyu kenan fa amman kanayimin maganar aure, saina gama karatu, bismilla ga abinci." Tak'arasa fad'a tare da jawo farantin da Mama ta shiryo abinci a ciki. Kad'an Samir yaci abincin, yakalli Aysher cikin tu6une fuska yace"Sulty zantafi dare yayi, gasu Aslam zasuyi one week, sai kutaho tare dasu lokacin bikin zandawo gobe kafin na wuce."
Murmushi Aysher tayi ganin yadda Samir yake magana kamar dole tace"bakomai sai kazo din, Allah yakaimu lafiya ka kularmin da kanka."
Mik'ewa Samir yayi tare da k'ara d'aure fuska yace"Ina ruwanki da ni da zakice na kula da kaina, sai da safe."

Ficewa yayi a gaggauce, baijira cewar Aysher ba.
"Abban Aslam rigima." Aysher tafad'a tare da mik'ewa bayan ta tattare kayan abincin dake falon.

```******```
Kabir yana d'aya daga cikin wad'anda suke zuga Samir kan amincewa da auren Yaseera, dan tsakani da Allah Samir ya yadda da Kabir d'ari bisa d'ari.

Kabir yana lissafe da ranar da iddar Aysher zata cika, dan haka tana cika ya garzaya gidan tunda yaje gidansu Aysher sau uku yana aika yaro ayi mishi sallama da ita, yaron sai ya dawo da amsar cewa"tace koma waye yayi hakuri, ba zata samu damar zuwa ba." Zuwanshi uku ana bashi wannan amsar dan haka ya hak'ura tare da k'arama Aysher lokaci, cikin zuciyarsa ya d'aura aniyyar cewa bazaije bikin Samir Kaduna ba tunda yasan Aysher dole taje.

Yaseera na hango kwance akan makeken gadonta, takira Johnson a waya suna magana cikin harshen turanci tace"Haba Jonh nace maka karka damu, idan nayi wannan auren zanzo na aureka, nifa kawai inaso naji yadda guy d'in yake ne, dan haka nakeso na aure shi, kota wane hali saina koya masa shan kayan maye."

Shiru Jonhson yayi kafin kuma daga bisani yace"okay ina jiranki promise? (alk'awari)."

"I promise u my love (Nayi maka alk'awari masoyina)."

Shirye-shiryen biki ya kankama sosai gidan Alh. Auwal mataimaki suke shiri,, Yaseera amarya dakanta take yima kanta shiri tasha wancan, ta matsa wancan, haka dai. Bangaren Samir babuwani shiri dayakeyi tunda uban ango ya hutar dashi kayan lefe, dan haka ya zuba ido shidai kawai sadaki yake jira ranar tayi yaje ya bayar, Mama tanata shiri danma Samir ya dakatar da ita gayyato jama'a.

Alh. Auwal mataimaki da kansa yakira Samir ya shaida masa waliman da abokansa suka shiryama ango da amarya tare da rokon alfarman Samir yataimaka yaje, hakanan Samir ya amsa badan yaso ba.
Ana gobe d'aurin aure Aysher ta sauka a garin zari'a badon ranta yaso zuwa ba, sai dan takura mata da Samir yayi, a gidan wani kawunta ta sauka dake zaune a kaduna anguwar sarki ta sauka ita da yaranta.

A kuma ranar ne za'ayi walimar da Alh. Auwal ya shaidama Samir, dan haka Samir baisamu had'uwa dasu Aysher ba a wannan ranar.
[12/10, 5:06 PM] Samir ya isa wajen da Alh. Auwal ya fad'a masa domin yin walimar bikinsa da abokansa suka shirya ba don ransa yaso ba, tare suka tafi da wani abokin aikinsa mutum d'aya wato Ahmad, amma abinda ya fara gani ne a gurin ya bashi mamaki, waje ya cika da 'yan mata da samari a takaice dai party aka shirya, kuma sabanin yanda ya zata zaiga manyan mutane sai yaga qawayen Yaseera. Haka dai ya zauna ba dan yana so ba kawai dan ya isa wajen ne, haka akayi party ba yabo ba fallasa, Ansha kayan shaye shaye a wajen, shima Samir haka aka bashi wine ya kwankwada ba tare da yana da masa niyar akwai alocohol (giya) a ciki ba........

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*
*_We are here to educate, motivate, and entertain you reader's._*

*INA JINKU A ZUCIYATA*
*_Beauty Queen_*
*_Mmn Noor_*
*_My madaya_*

*Alfahari nakeyi daku sosai.*
*_Zauren littattafan hausa_*
*_Duniyar marubuta_*
*_Mace mutum group_*
©Zeetty

PAGE 24-25

Sai wajen 12:00am aka gama dinner wanda suka kirashi da sunan walima, irin bad'alar da sukayi a gurin baki bazai iya fad'arsa ba. Ahmad abokin Samir shima dayake dan duniya ne, yana d'an kora ruwan giyar dan haka yasha abinsa son ransa, haka Ahmad yakama Samir zuwa gurin mota dan lokacin Samir baya cikin haiyacinsa, Amarya taso sutafi tare da Samir amman Johnson dayazo mata biki yahanata zuwa a cewar sa yakama musu hotel suje su kwana dan yima juna bankwana kafin lokacin nasu bikin (subhanallah! Kunji wani lalacewa Allah shirya mana zuri'a).

Aysher bata samu halattar gurin walimar ba kamar yadda Samir ya gaiyaceta, dan batason zuwa taga Samir da wata a matsayin matar da zai aura (kishi), dan haka kawai ta zauna a gidan kawunta inda ta sauka kenan, kiran wayar Samir ta dingayi bayan anyi sallar magriba, dan taji yaushe zaitafi walimar amman shiru ba'a d'auka ba har wajen isha, Aysher duk ta damu a ganinta ko Samir yayi fushi ne dan tak'i zuwa gurin walimar auren sa. Dan haka ta dinga kira akan cewa yayi mata kwatancen gurin walimar amman shiru har zuwa k'arefe 11pm (na dare) tanata kira bai d'auki wayar ba, dan haka Aysher ta hak'ura da kira ranta a 6ace"meyasa Abban Aslam baizaiyi mata uzuri ba (tunanin da Aysher takeyi kenan cikin zuciyarta)."
Rashin sani! Dan kuwa Samir tunda zaishiga masallaci sallah magriba yasa wayar a silent saboda zafinkan maganar zuwa gurin walimar nan ya manta bai cire ba, dan haka duk kiran da Aysher takeyi masa baisani ba, bai kuma d'auko wayar ya duba ba har zuwa lokacin da ya isa gurin walimar ya kora ruwan kwalba (giya) cikin rashin sani.

Kai tsaye gidan Samir, Ahmad ya nufa da shi bai direshi a ko'ina ba saida yakamashi har cikin falo ya shigar dashi kafin ya juya dan zuwa nashi gidan.
_Mama bata gidan, tana gidan wasu 'yan uwanta dake cikin anguwar kawo, saboda gyare-gyare da Alh. Auwal mataimaki (Uban amarya) yasa aka sakeyima gidan tare da sabon fenti dan zuwan amarya._

Samir a falon ya baje, bacci yayi gaba dashi, bashi yatashi farkawa ba sai wajen asuba, mamaki yadingayi yadda akayi yadawo gida can kuma yafa tunanin abinda yafaru dashi da kuma abinda yayi na k'arshe a gurin party nan, cak tunanin sa ya tsaya sanda ya tuno da cewar ashe fa wine Ahmad yazuba masa a kofi shida Yaseera suka sha a lokaci guda bayan yaciyar da ita cake itama ta ciyar dashi.

Kai Samir yadafe tare da ambatar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! A fili a hankali yad'aga hannuwansa sama yana fara cewa"astagfirillah ya Allah natuba, Allah karka kamani da laifin da na aikata cikin rashin sani, Allah ya isa tsakanina dake Yaseera bazan ta6a yafe miki ba tun kafin kije gidana burinki yafara cika a kaina, kinfara bani ruwan maye nasha na kwana batare danasan a wani hali nake cikiba, hak'ik'a zaki yabawa aya zak'inta randa kika shigo gidana." Abinda Samir yake ta fad'a kenan cikin zuciyarsa kafin daga bisani yatashi yaje yad'auro alwala yafara Sallah nafilfili tare da rok'on gafarar ubangiji.

*************
Yaseera kuwa kwana sukayi suna aikata bad'ala ita da Johnson, dakyar tasamu ta lalla6eshi yabarta ta tafi dan k'arfe 11:00am za'a d'aura aurenta da Samir (kunji lalacewa Iyayenta kuma basu binciki ina take ba).

A haka ta lalla6a ta tafi gidan mahaifinta dake Anguwar dosa, lokacin anfara cika 'yan d'aurin aure, a haka tayi horn mai gadi ya bud'e mata gate ta kutsa ka motar cikin gidan.

Bawanda ya tambayi daga inda tadawo, a haka har lokacin d'aurin aure yayi babu ango sai abokansa da kawun sa (waliyyin Samir), abokansa suka d'inga kiransa a waya shiru wayar a kashe a haka har aka d'aura auren babu ango babu labarinsa.

Samir dai yana sane da lokacin da za'a d'aura masa aure, yayi kuma alk'awarin cewa bazai halatta ba dan haka nema yakashe wayar sa tunda ya dinga kiran wayar Aysher tak'i d'auka dan tayi fushi "wayyo Sulty meyasa bazaki d'auki wayata na fad'a miki matsalata ba, na sha giya na kwana cikin maye." Samir ya fad'a a fili hawaye yana zubowa daga fuskar sa,gyara zama yayi, yayi kwanciyar sa saboda har yanzu abar bata sakeshi ba (ni kuwa nace rashin sabo).

Sai bayan yayi azahar sannan yashirya lokacin yafarajin dai-dai, dan haka bai saurari gidansu Amarya ba kai tsaye gidan da Aysher ta sauka ya nufa.

Sallama yasa akayi masa da ita, batayi niyyar fitowa ba amman dan batason matar kawunta ta gane akwai matsala tsakanin su yasata tura masa yaransa da sak'on cewar gatanan fitowa. Fitowar Aysher yayi dai-dai da sauke wani nannauyar numfashi sa Samir yayi, kwalliya tayi mai sauk'i dayake Aysher mai kyau ce dan haka tayi kyau d'in ba k'arya, fuska a had'e ta k'araso gurin sa tafara gaidashi ya amsa yana wadata fuskarsa da murmushi tare da cewa"kaina bisa wuya my Sulty, nasan nayi laifi amman ki tsaya kiji dalilina kimin uzuri pls."
Aysher ta cuno baki tare da cewa"Abban Aslam me zance, tunda daga fara hidimar biki kamanta damu jiya sau nawa ina kiran wayarka shiru ba'adauka ba."

Samir yace"yi hak'uri Sulty, kaina bisa wuya wayar tawa tun da zanyi sallah magriba nasa a silent na manta." Daga nan Samir ya kwashe irin aika-aikar da Yaseera tayi masa a gurin party wanda suka kira da sunan walima yak'arasa fad'a yana zubar hawaye yace"Sulty yanzu ace matar da zan aura tunkafin akawota gida na tafara d'uramin kayan maye, gaba-gaba bansan abinda zata aikatamin ba, nikam in sha Allahu tunda sun d'aura ko ruwan gidanta bazan yadda nasha ba Allah ya isa bazan yafe ba."
Dariyane yakama Aysher ganin yadda Samir ya dage yana fad'a iyaka gaskiyar sa, amman ta kanne ta dinga kwantar masa da hankali har ya sauko ya d'aukesu a motar sa dan zuwa gidan danginsa dake kawo inda anan ake hidimar bikin nasa.
Chapter 7 · 0% Book details