← Book details Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 10

Sashe 6

Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin gabjejiyar muryar ta tace"haba D-lovely inayi maka magana kayi shiru why, Dad yace zamuyi aure nan da 2 weeks dan haka i can't wait to see dat day, saboda sosai kayimin dan haka zan shayar dakai zumar da baka ta6a shan irin sa ba, me kace.?"

Shiru yayi mamaki yana sake rufe shi, jiyayi ta kawo masa wani irin runguma da sauri ya mik'e daga gurin, yana fad'in"subhanallah Yaseera meye haka, kanki d'aya kuwa?."

"Toh D-lovely inason na nuna maka yadda nake sonka ne, karka bani kunya mana kanayin abu kamar ba wayayye ba, meyasa kazo mud'anyi romancing before katafi, karage zafi."

"A'a nikam natafi sai na sake dawowa, daga ganin ki bakya cikin hayyacin ki."

Yaseera tace"Okay D-lovely sai kadawo d'in, tashi d'aya naji na kamu da wani irin soyayyar ka gami da zazzafar sha'awar ka, nifa yanzu codien na sha kwalba d'aya kawai D-lovely kaga ai bansha da yawa ba."

"Uhmmm baki sha ba kam, sai nazo bye."

Samir bai jira cewar ta ba yafice a falon da gudu, dan ganin tana shirin kawo masa wani runguman.

Da daddare yakira Aysher a waya, tana d'auka yafara magana wanda daga jinsa tasan yana cikin damuwa yace"Sulty kinga abinda kika jawomin ko?, wai yau da 'yar codien nayi gamo matar da zan aure, totally batayimin ba k'afuwan ta kamar marad'in acca, jiki kamar sanda, baki ga abinda tayimin ba daga zuwa na (kwashe labarin abinda yafaru a gamuwar sa da Yaseera yayi, yafad'ama Aysher)."

Tausayinsa sosai ne yakama Aysher bayan yagama bata labari a hankali tace"kayi hak'uri kawai Abban Aslam kataimaka masa waje gyara masa tarbiyarta kamar yadda yanema Allah zai dafa maka, in sha Allah zaka samu lada."

Cikin murya mai rauni Samir yace"daman nasan haka zakice, bazaki ta6a jin haushin hakan ba, bakomai nagode wallahi da ace ban amince masa ba tun farko, wallahi da na fasa, shiyasa yayimin dabaran cewa sai na fara amince masa kafin naganta, saboda yasan halin 'yar tasa bakomai sai da safe."
Diff ya kashe wayar baijira cewar Aysher ba.

Muje zuwa.....

MAMAN HANAN
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/6, 12:43 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

©Zeetty

🍀🍀🍀 *SABODA ABOTA* 🍀🍀🍀
Na
Fatimah Muhammad (Ummancy)
*_Hak'ik'a na jinjinama wannan hazik'ar marubuciyar tamu, wanda tayi mana bayani akan yadda mu'amala yake kasancewa tsakanin Mace da Namiji, Matan aure masu zuwa gurin aiki, dan Allah kuyi amfani da darasin da kuka karanta cikin littafin Ummancy, Up up Fatima, sai munjiki a sabon littafin ki Allah k'ara basira._*

PAGE 19-20
A wannan daren Aysher kasa rintsawa tayi, dan haka ta d'auro Allah tafara jero nafila dan neman za6in Allah tsakanin ta da Samir.

Washe gari bayan Samir yagama breakfast kafin yatafi office yake shaidawa mahaifiyar shi maganar Yaseera 'yar gidan ogan shi, sai dai ya 6oye mata mugayen d'abi'unta da kuma dalilin dayasa mai gidan shi yabashi auren ta.

Sosai taji dad'in maganar dan itama rashin mata kusa da d'an nata yana damunta, dan haka tashiga jero addu'o'i tare da sanyama lamarin Alheri.
Shi dai Samir fuska ya k'ara had'awa, ko amsa addu'ar nata bayayi, ya kai duban sa kan yaranshi yace"Aslam da Afra ku shirya tunda kuna hutu idan nadawo daga office mu wuce kano."

Ihun murna yaran suka shigayi da tsalle suna fad'in "yeeh! Yau zamuga Momy da Mama."
Cikin ran Samir tausayin yaran sa ne yasake kamashi, _Aysher hakkina nida yaran nan idan yatashi tambayarki bazakiji dad'i ba._ (Samir ke fad'in haka cikin zuciyarshi).

Mama ce ta katse mishi tunanin shi da cewa"Samir tafiyar dare zakayi da yara k'anana haka?."

Ya bata amsa yana tafiya bayan yad'auki briefcase d'inshi"a'a Mama yau bani da aiki sosai, dawuri zandawo mutafi kema idan zakije saiki shirya mutafi tare."

"Ai kuwa zanje, ka saukeni Garin Malam, daga nan saina sanar musu da biki."

"A'a Mama dan Allah karkiyi wani gayya tunda bana farko bane, uban amaryan da kanshi yace babu wani taron biki (yafad'i hakane saboda bayason azo aga kalar amaryan tashi, abinka da surutun mutanan k'auye 'yan garinmu lol)."

Mama tace"toh saika dawo dai Allah tsare."

"Amin." Ya amsa tare da ficewa daga falon.

``` *******```
Samir sun shiga cikin garin kano ana kiran sallah magriba, domin saida ya fara tsayawa a hanya ya sauke Mama a garin Malam (wani d'an k'auye ne farkon shiga kano, kafin a k'arasa kura).

Su Aslam yatura cikin gidan Kakan ninsa (gidan su Aysher), shi kuma yayi saurin d'aura alwala domin shiga masallacin dake k'ofar gidan su Aysher, ya samu jam'in sallar magriba da akeyi.

Da gudu yaran suka shiga gidan, suka tarar Aysher da Mama suna Sallah, dan haka neman guri sukayi a falon suka zauna, Mama ce tafara idar wa dan haka kallon su tayi tana murmurshi tace"A'a maigida takobi, saukar yaushe a garin namu?." Gaisheta Aslam yafarayi kafin yace mata"yanzu mukazo Daddy ne ya kawomu."
Mama ta mayar da kallonta kan Afra tace"kishiyata ko gaisuwa baby? Sai kumburo baki kikeyi."

Afra cikin shagwa6a tace"ba kink'i kulani ba, sai Aslam kike kulawa shikenan ai bari Momy ta idar da sallah nasan zata kulani."

Baki Mama ta rik'e tana fad'in "ohh ni na shigesu, toh kiyi hak'uri kinji kishiya."

Dariya Aysher taketayi musu yaran sunbata mamaki, rabon da tagansu wata biyu kenan, sun k'ara girma sosai.

"Aslam da Afra drama kenan, kunzo zaku takura Mamana da surutu ko?." Cewar Aysher

Aslam ne yafara gaisheta kafin Afra, k'arasawa jikin Aysher sukayi suka kwanta, lokaci d'aya suka sauke ajiyar zuciya. Aslam ne yafara magana da cewa"Momy anbamu hutu, Dady yace zamuyi sati d'aya anan kafin yadawo yatafi damu, wai bikin shi saura sati biyu Momy zakizo?, yauwa Momy meye ake nufi da *gida idan babu mace kango ne?."*

Ajiyar zuciya Aysher tayi kafin tace"Ohh Aslam surutu da tambaya, toh wanne zan fara amsa maka a ciki?, waye yake cewa gida idan babu mace kango ne?."

Cikin sauri Aslam yace"Daddy ne mana kullum sai yayita fad'an haka, bayan yad'auko hoton mu da akayi mana babba ranar da muka koma kaduna yanata kallo, Momy har kuka Dady yakeyi."

"Shiii ya isa haka, zan fad'a maka abinda ake nufi da kalmar amman saika k'ara girma, kuma zanzo bikin Dady."

Mama dai tana gefe ta zuba musu ido, bata sako musu baki ba, cikin zuciyarta fad'i takeyi _yaran Aysher Allah ya sako musu dabara da wayau, Allah dai ya raya._

Wayar Aysher ne yake kuwwar neman a gaji, alamar kira yana shigowa tana dubawa taga Samir ne dan haka tayi hanzarin d'auka.

"Hello."

"Kizo ina falon Baba." Abinda ya fad'a kenan baijira cewarta ba ya katse kiran.
[12/6, 1:08 PM] Zeetty: Ta shiga falon da sallama, ya amsa mata kafin tanemi guri ta zauna, ta fara gaisheshi ya amsa babu yabo babu fallasa.
Falon yad'auki shirun wasu 'yan mintuna shiru bawanda yayi magana, Samir ne yagaji da shirun dan haka yayi gyaran murya kafin yafara magana da cewa"Sulty ina cikin damuwa, nayi dana sanin ka6ar wannan aure na Yaseera yarinyar gaba d'aya bata da hali, muryan ta kamar na Maza lamarin nata sam babu sha'awa, Sulty duk kece kika janyomin *Mafarin lamarin* da'ace angani da mata Oga bazai ta6a yimin tayin auren 'yar sa ba."

Aysher ta bud'i baki zatayi magana wayar Samir yafara kuwwa alamar kira yana shigo masa, ya duba number da ake kira yaga bak'uwar Number ce dan haka ya share yak'i d'auka, ba'a hak'ura ba aka sake kira, Aysher tace"kad'auka kagani mana ko waye."

Dan haka Samir ya danna yad'auka amman yak'i magana. Daga d'aya 6angaren yaji ana magan. "Hello! D-lovely kana jina Amaryace Seera Baby."

Na shiga uku! Kalmar da Samir ya fad'a kenan tare da katse kiran, yakalli Aysher yace"Sulty itace fa, nikam wannan yarinyar wace irin mayya ce haka, a ina ta samu number na?, danni bani na bata ba da hannu....." Wani kiran ne yasake shigowa Aysher tace"kad'auka kaji abinda zata ce maka dan mu gama magama dare yanayi (ta fad'a cikin alamun kishi)."

Samir ya d'auka bayan yasa maganar yadda Aysher zata iya jin abinda Yaseera take fad'a.
"Hello! D-lovely wai baka jina ne, toh daman zan fita zuwa club ne shine Dad yace saina tambayi izinin ka, amman fa baisan cewa club zanje ba dan Allah karka fad'a masa, shine Dad d'in yabani Number ka, toh ya kake gani naje?, zan na samo abin ta6awa ne wata k'ila ma nayi sa'ar samun cocein (hodar iblis), dan na kwana biyu bansha ba tunda Dad yasa aka kwashemin kayan maye na a gida, shiyasa nakeso ayi auren nan nasan bazaka takurani ba ko D-lovely?. Wata rana ma zan baka kasha, zan koya maka shiga duniyar sahara kajika a sama-sama......."

Diff Samir yakatse wayar yadafe kansa da hannu.
Yakalli Aysher hawaye yake fitarwa mai ciwo yace"Sulty i'm finished! Natashi daga aiki nikam, kinji tsinanniya zata koyamin yadda akeshan kayan maye, Sulty shin ko baki yafemin bane?, hak'k'inki yafara tambayata tunkafin aje ko ina, barin je nikam auren nan nafasa saidai sanadiyyar haka a koreni daga aiki."

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/10, 4:46 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

©Zeetty

_Na sadaukar da wannan page d'in gareku, Maimunat Idris Sani Beli da Fauziyya D. Sulaimain, Ubangiji ya kara basira sosai nake biye daku._

PAGE 22-23
Mik'ewa Samir yayi da niyyar barin d'akin, Aysher tayi saurin shan gabansa tare da cewa"Abban Aslam kakwantar da hankalinka, babu abinda yafi k'arfin ubangiji so u have to calm down ur mind pls dawo kazauna muyi shawara. A sanyaye Samir ya dawo ya zauna akan kujera, ruwa mai sanyi Aysher tafara bashi yasha lokaci d'aya yasauke kofin tare da ajiyar zuciya.

Aysher ta kalleshi cikin sanyin muryarta tace"Abban Aslam ka kwantar da hankalinka, kaucewa wannan aure ba k'aramar matsala bace tunda kariga ka amsa da bakinka banason kazama k'aramin mutum mai magana biyu, tayiwu Allah ya nufeka da wannan auren ne ta dalilin haka Yaseera ta shiryu......."
A fusace Samir yace"Ni zan shiryar da ita, wannan kangararriyar yarinyar?."
Chapter 6 · 0% Book details