← Book details Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Mafarin Lamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Aslam yakama hannun kanwarsa suka shige cikin gidan, shi kuma Samir yafita dan jiransu a mota, ya sunkuyar da kansa akan sitiyari yafad'a kogin tunani, Isah ne yafito ya bubbuga masa glass d'in motar ya d'ago da kansa da sauri ya kalleshi, Isah yace keep calm my friend, gasu Aslam nakawo maka, muna jiran takaddar Aysher pls koda text msg ne ta waya kayi mata mun hutar dakai zuwa. Cikin sanyin murya Samir yace"haba Isah kaifa babba ne, kaida zaka dai-daita al-amarin kuma kaine mai ruwa da tsakin ayi sakin?", murmushin takaici Isah yayi kafin yace"ashe kasan da hakan baka dubi girma naba kake dukan k'anwata da azabtar da ita a gaban yaran cikin ta", girgiza kai Isah yayi kafin yakara cewa"Aslam shekarun shi 6 yanzu, Afnan 3½ but yanzu da suka shigo cikin gida cewa sukeyi Momy kitaso mutafi, Abba bazai sake dukan ki ba da zagin ki, kinga ai yadaina tunda muka dawo gidan 'yan gayu, toh Samir tayaya zaka goge wannna hoton a zuciyar yaranku for God sake?, jeka kawai akwai Allah amman wallahi saika saki Aysher." Yana gama fad'in haka yasakai yabar gurin, cikin sanyin jiki Samir ya saka yaranshi a mota yajasu sai Kaduna.

A gida komai ya cakud'ema Samir aikin Office ga hidiman yara, lallai yasara Matar shi Aysher, ashe ba karamin aiki takeyi ba a gidan, shiyake musu wanka break fast, lunch da dinner kuma saidai suyi take away, yara sun dawo marayun dole idan kagansu dole su baka tausayi, Samir yana bama kanshi kwarin gwiwar cewa wannan week end din idan yatafi kano tun friday sai sunday zai dawo shida matar sa, yakira wayarta yafi a kirga baya zuwa da'alamar ta canja layine saboda shi, Ohhh shikam Kabir yakaishi yabaro da muguwar shawarar daya dinga bashi.

Haka al'amuran suka cigaba da tafiya har zuwa ranar juma'a, sai da Samir yajira aka taso 'yan school kafin yashiryasu yadauki hanya zuwa kano, kaitsaye gidan su Aysher yafara tsayawa yatura yaran tare da fad'a musu cewar zaizo anjima shida Baba Mu'azu (Kanin Mahaifinsa).

Aysher taji dad'in ganin yaranta, nan kakar su tafara nan da nan dasu, Maryam ma 'yan matan ABU anzo hutu, dawowanta tak'ara zuwa yayar tata tana sake tuno mata wasu abubuwan data manta dasu wanda akayi agaban ta, kalmar mai *_MAI FARAF K'AFA_* sosai yake 6atawa Aysher ranta idan harta tuno dashi.

Da daddare Baba Mu'azu yazo tare da Samir, Baban Aysher suka fara sallama dashi, bayan yafito tare da dogon gaishe2, Baba Mu'azu yafad'i dalilin zuwan nasu" wato Mal. Muhammadu yaron nan Samir tazo gurina tare da sanar min irin aika-aikar dayayi hak'ik'a ni kaina banso zuwa ba saida yad'aukomin Mahaifiyar sa, dan Allah ayi hakuri adubi zuri'an da Allah yafara basu, Uwata ta koma d'akin ta dan Allah."

Shiru Baba yayi dan yana bala'in jin kunyar Mal.Mu'azu amman hakan bazaisa a fasa hora Samir ba dan haka yafara bama Mu'azu labarin irin gashin ayar da Samir yayima Aysher harda kiranta da yake _MAI FARAR K'AFA_, duka da zagin cin mutumci, sau biyu ina zuwa har gida nayi masa nasiha ashe baya shigarsa, baifasa ba dan haka ni babu abinda zace anan kuyi hak'uri. Shiru Mal Mu'azu yayi kafin yace"Naji takaicin wannan lamari, naji haushi uwata tanada gaskiya wallahi danasan hakane da ban zoba, ni kunya duk ta kamani, sai kaje kanemo abokan naka da suke baka shawara suzo maka bikon matar ka, ba ruwana."
Cikin 6acin rai yayima Alh.Muhammad sallama yatafi kotakan Samir baibi ba.

Alh. Muhammad ma tashi yayi yashige gidan yabar Samir a zaune tagumi yayi shi kadai yasan abinda yakeji cikin heart dinsa.
[11/26, 10:29 AM] Zeetty: Haka Samir yagama hutun karshen makonsa yakoma batare dayasamu had'in kan Aysher ba, har abokansa yakawo mata Aysher tayi musu tass (haka masu sunan suke akwai hakuri, amman fushin su bakyau).

A haka dai har aka shafe wata guda batare da Aysher ta sauko daga dokin nak'in data hauba, tarantse bazata koma ba, dole Samir yad'auko Mahaifiyar sa yakomar da ita kaduna saboda kula da yara.

Ranar wata Asabar Samir yashirya kamar kullum amman wannan karon da takaddar sakin Aysher mai d'auke da saki 1, yatafi kano tare da alwashin zaiyi ma Aysher saki d'aya ko zata sauko su mayar da auren su, idan harta huce kuka yayi sosai kafin ya rubuta saki d'ayan, sosai yakeson Sulty, amman kaddara da son zuciya gashi yarabasu.

Koda yaje batare daya ja dogon lokaci ba yasake bama Aysher hakuri, amman tace tanakan bakanta dan haka yad'auko takadda idon sa sanye da bak'in glass bazaka gane yanayin dayake ciki ba, ya mikawa Aysher farin envalope d'in tare da check na kud'i, kafin yadaure saboda kukan zuciyar da yakeyi ya durk'usa yana cewa" Sulty kigafarceni, ina fatan zaki huce very soon nazo mu mayar da auren mu, ki zauna da yaranki, ga kud'i kirike a hanunki zan aiko miki da motar ki dana siya miki, ki taimaka ki bani sabon number ki koba komai zamuyi zumunci albarkacin su Aslam, ki d'aukeni yaya abokin shawaranki pls."

Cikin sanyin jiki Aysher takarba ta saka masa number tana mika masa wayar tabar falon da sauri saboda wani kuka daya taso mata.

Samir ma ikon Allah ne kawai ya mayar dashi gida kaduna, kamar amafarki yasaki Sulty shi.

Muje zuwa dan yanzu za'afara chakwakiyar.

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

©Zeetty

PAGE 13-14

Cikin sanyin jiki Samir yajawo motar sa tare da barin k'ofar gidan, wayar abokin sa Kabir yakira yake shaida masa cewar yaufa ya saki Sulty, wani ihu Kabir yasaki tare da cewa"Like seriously abokina?", shiru Samir yayi yakasa bashi amsa dan yana tunanin wannan farin cikin da Kabir yakeyi kuma na menene?.

"Hello! Samir kanajina kuwa, da gaske kasaki Aysher?."

"Eh Kabir zanyi maka wasa ne da wannan zancen da ko a mafarki banyi tunanin faruwar shi ba?."

"Kayi hak'uri abokina kad'auki hakan a matsayin jarrabawa, kaidaga hutu ma ya sameka, karabu da jangwam, kaidai Allah baka wadda tafita kawai." Cewar Kabir.

Samir yayi wani huci tare da fesar da iska mai zafi, kamar Kabir yana kallon sa yace"Har'abadah bazan samu kamar Aysher ba, dagaske nayi rashin da bazan ta6a mayarwa ba, nidai fatana tasamu mu dai-daita kafin ta kammala iddar ta mu maida auren mu, bari dai zankira ka idan nasauka zan wuce kaduna ina hanya."

"Okay saika kira Allah tsare."

Wani ihu Kabir yasaki, tare da cewa "Alhamdulillahi yau burina yacika, zan samu gwarzuwan zuciyata, shege harda wani cewa zaka maida ita kafin ta gama idda, ai duk yadda yaza'ayi saina zuge ka baka mayar da ita ba, har sai tagama idda lokacin kuwa tazamo allura cikin ruwa, barin harzarta zuwa na fara kaima mahaifinta gaisuwa, yasan da zamana tun wuri." Zancen da Kabir yakeyi kenan shi kad'ai yana zaune a fine time restaurant, ya mik'e dan barin gurin.

Dole ne na hanzar ta zuwa gidan su Aysher yanzu danyi mata jaje, daman bata san ina daga cikin abokan Samir ba, shiyasa nak'i zuwa bata hak'uri karta ganeni, tsarina ya lalace (Kabir ke fad'in haka cikin zuciyar sa).

```******```
Aysher kuwa tana shiga falon Mahaifiyar ta da takaddar sakin a hannun ta, neman guri tayi tazauna kafin tafara kuka mara sauti.
Umma batayi yunk'urin hanata ba, saida tayi mai isar ta tayi shiru dan kanta, kafin Umma tayi magana"atoh daman shi mutuwar aure ai ciwo ne dashi, banda haka wane irin baki ne da nasiha banyi miki ba?, amman keda Yayan ku da Mahaifinki kuka kafe akan maganar shegen taurin kai irin naki kamar mutanen farko, tare da goyon bayan su, kiyimin shiru gaki ga gidan na." Tana gama fad'in haka tamik'e tabar falon.

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/1, 8:28 AM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*

_Happy Maulud to all 'Darika muslim Brother's & Sister's around the world._

*Ina maka murnan zagayowan watan haihuwarka AHMAD YAKASAI, Allah k'aro shekaru masu albarka.*

_Kucigaba da kasancewa dani domin fuskantar sak'ona danakeson isarwa a wannan labarin, lamarin sosai yana faruwa kamar yadda wata tayimin magana ta Pc kamar haka:-_

*+23480534553.....*
_Assalam Maman Hanan sunana Maman Ayman, dan Allah kici gaba da labarin MAFARIN LAMARI jinshi nakeyi kamar labarina kike bayarwa, sai dai akwai dan banbanci, amman wlh yadda Samir yakecema Aysher mai farar kafa haka mijina da danginsa inaso naji yadda karshen labarin zaizama,muna tare dake ubangiji yakara miki basira, inayinki sosai burina wata rana nazo naganki marubuciyar DABI'A da Mafarin lamarin labaru masu taba zuciya nagode, kiyi saving number na dan Allah, sunana Maman Ayman._

*AMSA*
_Wslm! Nagode Maman Ayman Allah bar zumunci, naji dad'in addu'arki, zanyi saving number ki, In sha Allah idan nagama rubutawa zanyi miki wasu tambayoyi idan badamuwa, Nagode. Maman Hanan ce_

©Zeetty

PAGE 15-16

Bayan Sallah magriba Kabir yazo k'ofar gidan su Aysher, ya faka motar sa a gefe yakulle motar yafito, kai tsaye gurin Mahaifin Aysher ya dosa yayi masa sallama ya amsa, ya durk'usa har k'asa ya gaidashi ya amsa fuska a sake, can Alh. Muhammad yace"Sai dai bangane waye ba.?"

Sosa kai Kabir yayi da mukullin motar sa kafin yasake duk'ar dakai alamar mara gaskiya yace"Baba gaskiya baka sanni ba, nadai zone zan wuce natsaya mugaisa, zantafi a huta lafiya." Yak'arasa fad'a bayan yamik'e dan barin gurin.
Mamakine sosai yakama Alh. Muhammad amman saiya saki fara'a yadinga shima Kabir albarka, sosai Kabir yaji dad'i dan haka yace in sha Allahu zandinga zuwa muna gaisawa Baba idan nazo anguwar nan.

Bakomai yaro nagode sai kazo d'in.

Mota Kabir yakoma yashige zuciyarsa cike da murnan tarkon sa na farko ya d'anu (ma'ana yafara samun sa'a).

Sosai Alh.Muhammad ya kwantar wa da Aysher hankali, dan duk yadda taso da mutuwar auren bayan anyi mata kuma lamarin ya bugeta sosai. A hankali kuma komai ya wuce mata, ta maida hankali wajen kammala iddar ta, gefe guda kuma Isah yafara mata chuku-chukun samun makarantar School of Nursing dake Aminu kano teaching Hospital.
Chapter 4 · 0% Book details