← Book details Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta rakata har bakin ƙofa, ta koma cikin gida kai tsaye ta nufi part ɗin Hajja, mahaifiyar AA Turaki.
Tun kafin ta shiga ciki sosai, kamshin turaren dakin da shaukinsa ya ratsa hancinta, amma duddah haka bai rage mata tsoro da fargaba ba.

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Ta shiga dakin cikin ladabi, ta zauna a gaban Hajja wacce ke zaune kan kujera tana jan tasbihin ta.

Hajja ce : ta dago kai da wani ƙyalli cikin idon ta tace “ Ramlart, kin dawo Lafiya?, ya jikin naki.”

Cike da kunyar kanta Ramlart tace: “Eh Hajja...jiki da sauki nagode da addu’arku.”

Hajja ta aje tasbihinta, ta gyara zama kamar mai son fad'ar wani abu.

“Na yi shiru ne ban ce komai ba tun da kike asibiti, Amma yanzu dole ne na fada, Wannan halin da kika jefa kanki da ɗanmu a ciki, ba abu ne da zan iya rufe ido a kai ba.”

Ramlart ta saki ajiyar zuciya, ta sauke kai ƙasa.

Hajja taci gaba da cewa: “Shan maganin zubar da ciki? Auren shekaru biyar babu haihuwa, yanzu kuma sai ki jefa kanki cikin barna? Kin san irin raunin da kika jefa ɗanmu ciki kuwa?”

Ramlart ta dafe ƙirjinta da hannayenta biyu, hawaye na zubo mata, akan kuncinta tace.

“Hajja… wallahi nayi nadama ,Na tuba… bazan sake ba, ki yafe mini , sharrin shaidan ne.”

Sai da Hajja ta kalle ta na tsayin lokaci kafin ta ɗan sauke muryar ta kasa tace.

“Toh idan da gaske kike, ki nuna hakan da kyakkyawan hali, ba da baki kawai ba, Saboda abin da kika aikata na iya hanaki samun haihuwa har abada.”

Ramlart ta share hawayenta, ta juya da ƙyar, ta fice daga part ɗin cike da kunya da danne danne.

Bayan ta fito daga bangaren Hajja, Ramlart ta shige part ɗinta cike da rudani da tashin hankali, Jikinta ya yi sanyi zuciyarta na bugawa da karfi.
Kalaman Hajja sun daki kunnenta fiye da yadda take tsammani.
Cike da tsoro da matsin lamba, ta janyo wayarta daga cikin jakarta, ta danna lambar kawarta Zuly,tana dağa wa.
cikin rawar murya ramlart tace:
Hello... Zuly… please ki same ni a chat yanzu yanzu… wani abu ya na shirin faruwa… we are in trouble!

ZULY ce tace:
Lafiya? Me ya faru kuma?

Wani irin tsaki, ramlart ta sake ,hawaye na kokarin zubo mata tace:
An gane Zuly! Wallahi Hajja ta yi min zancen pills… kuma daga ni cewa tana da hujjojin da ke nuna ina sha.
Bata bayyana komai ba sosai, amma na gane cewa suna zargin na!
cikin firgici Zuly tace:
What?! Ta yaya? Waye ya tona mana asiri?

Cikin tashin hankali RAMLART tace :
Ban sani ba! Amma naga alamar Dr. Farida ce ta sanar da AA Turaki, shi kuma tabbas ya gaya wa mahaifiyarsa, kin san shi Mama's boy ne, Kuma yanzu wallahi na shiga uku… bansan yadda zan fita ba.

zama tayi a bakin gado, ta rungume pillow, zuciyarta na tafasa.

ZULY ne tace:
Calm down babe... ki nutsu. Sai mu nemi wata hanya, kema kinyi ganganci da kika yarda aka kaiki family hospital,ke da zakije private hospital inda muka saba zuwa ,haba ramlart saikace ba Wise ba .
Yanzu dai Ki ci gaba da nuna nadamar ki a gaban idon su.
Ki dinga nuna kamar kin chanja. Sannan... sai mu shirya sabon matakin da ya dace ,Wannan ba karshen komai bane, sai dai mafarin lamarin.

Ajiyar Zuciya ramlart ta sauke tace..
"Zuly wlh bansan ya akayi ba kawai dai na tashi na tsinci kaina national hospital tare da Aunty hauwa, yanzu dai ba wannan ba, kin san kuwa Hajja tana kok'arin shiga sabgata kuma na lura itace matsalata a cikin gidannan, tsohuwar tana bani ciwon kai wlh."

Cike da zafin rai ZULY tace:
Sai mu fitar da ita gaba ɗaya. Wannan game ne yanzu... kuma dole mu ci.

RAMLART ce ta shaki iska sannan tace:
Na yarda dake Zuly… amma wallahi bana jin dadin wannan zaman da nakeyi a gidan nan, ke dai kin riga da kinsan komai, kyansa da dukiyar sa nake so,Idan mahaifiyar sa ta cigaba da shiga rayuwar mu… zan iya rasa komai.
Kin san da cewa bayan kin kawo mini pills din ,bayan tafiyarki nayi amfani da su ,kamar dai yadda aka saba, kwatsam sai ciwon ciki ya turnuke ni ,tsabar wahala ban san lokacin da nakira aunty hauwa ba a waya ,shine fa tazo ta kai ni a sibitin,kin san in ba haka ba da asirin mu bazai tab'a tonuwa ba.
Ke dai karki samu damuwa kawata da zaran mun had'u komai zai dawo dai dai, cewar zuly.

Ramlart ta kashe wayar a hankali, ta jingina da jikin kujera tana kallon bango, zuciyarta na shirya mata sabon makirci mai cike da hadari...

💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫

✍️Mrs Alkali

Page 5️⃣

Bayan sallar isha’i, da misalin karfe 9:30pm Dare ya lullube garin, iska mai sanyi na kadawa ta window.

A hankali Ramlart ta turo kofar dakin ,Tana sanye da doguwar riga ta satin mai launin shudi, da santsi, Fuskarta cike da nadama da tsoro a lokaci guda.
AA Turaki yana tsaye a gaban mirror yana cire agogon hannunsa, d'an bai jima da shigowa gidan ba,ido ya zuba mata yana kallonta ta cikin madubi.

A hankali RAMLART tace.
"Na shigo ciki, Honey?"
ba tare da waiwaya ya kalle ta ba yace:
"Kin shiga ai tuni... tun da kika yanke hukunci da kanki kina shan magungunan da zasu zubar miki da ciki ba tare da shawara ba."

A hankali kamar wata munafuka, Ramlart ta karaso kusa da shi, ta tsaya daidai bayan sa, ta sa hannayen biyu ta rungume shi tabaya, ta kontar da kanta a bayan sa tare da lumshe idon ta tana kokarin dakatar da sauk'an hawayenta.

Cikin Muryar kuka tace.
"Dan Allah kayi hakuri. Ba haka nake so ba... kawai tsoro ne... kuma shawarar kawata ce."

Cikin nitsuwa ya juyo cike da izzah, kyawawan Idonsa ya zuba mata, wan da ya sa tafara diriri cewa .
Kamar wanda bazai ce komai ba a bazata taji saukar Muryar sa.

"Shawarar kawarki ce? Kina da miji, amma har kawarki ce ke tsara miki rayuwar auranki? Wannan ba ƙaramin gazawa bane Ramlart."

Shiru ne ya biyo baya, Ramlart ta sunkuyar da kai Ƙasa alamar ta yi nadama.

cikin kakkausan murya yace:
"Wani irin tsoro ne ya hana ki son haihuwa? A ina kika ajiye tsoron Allah? Kina sane da irin sharrin da zubar da ciki ke da shi? Kina sane da cewa Allah ya haramta hakan?"

Ramlart ta fashe da kuka tare da cewa.

"Wallahi ban san zai kai haka ba. Nayi kuskure... dan Allah kayi hakuri..."

Kai tsaye yake kallonta:
"Ba fushi nake da ke don na rasa ciki ba, Ramlart.
Fushi nake da zuciyarki mara tsoro da biyayya ga Ubangiji.
Abin da na ke nema ba kawai haihuwa ba ce , ina neman mace mai daraja, mai tsoron Allah da sanin hakkin aurenta."

Cikin nitsuwa Ya juya, ya zauna a gefen gado, Ramlart ta biyo shi tare da durƙusawa a gaban sa cikin kuka tace.

"Na tuba... wallahi bazan sake ba..."

ya dauki lokaci kafin ya kalleta, kamar mai karantar yanayin ta, gently yace.

"Allah ya sa ki tuba daga zuciyar ki, Amma ina so ki sani... ki kiyaye sake faruwar hakan a karo na biyu."

Yana gama fada'r hakan ya mike, ya shiga bandaki.
Ramlart ta tashi daga durƙushewar da tayi a ƙasa, tana kok'arin share hawayen ta, gefen gadon ta samu ta zauna tana ta kok'arin danne zuciyar ta.

Baiyi tsammanin har yanzu tana cikin ɗakin ba, ya fito daga bathroom yana shafe lallausan gashin kansa da towel, yana sanye da dogon robe mai launin fari, ruwa na diga daga gashinsa.
Fuskarsa na nuna alamun gajiya da rashin walwala.
Ramlart, wacce ke tsaye kusa da gado , ta nufo shi da murmushi da iyeyi a d'auke a fuskarta.

Cikin muryar raɗa-raɗa tace:
"Honey... dan Allah kayi hakuri. Na gane kuskurena, Ka gafarce ni…"

Tsayawa yayi cak, Ya kura mata idon sa masu kara birkita mata lissafi, Wata irin ƙunya da bacin rai na bayyana a saman fuskarsa, Bai ce mata komai ba, ya wuce ta gefenta yana dan girgiza kai.

Cike da iyeyi ta sake matsowa kusa, dashi ta ɗora hannunta a kafadarsa.

cikin sanyin murya tace:
"Wallahi, ina kaunarka, Duk abinda nayi saboda tsoro ne…"

Cike da takaici, ya fizge kafadarsa, cikin kakkausan Murya yace .

"Don Allah ki fita daga daki na kafin na rasa haƙuri na! Ki fita Ramlart!"

tsayawa tayi, idonta na cikowa da hawaye, amma kafin ta iya ƙara wata magana, ya tura ta da hannunsa har ta ja da baya kad'an.
Bai bata lokaci ba, ya karasa bakin ƙofa, ya bud'e kofar, ya nuna hanyar da yatsar sa da karfi yace.

"Get out!!"

Wani irin kuka mai rauni, Ramlart ta sake tare da ficewa da sauri, tana share hawayen ta.
rufe kofar ɗakin yayi da ƙarfi sannan ya juyo, ya tsaya na dan lokaci kamar yana tunanin wani abu.

Cikin nitsuwa Ya karasa gaban wardrobe ya ɗauko pajamas dinsa masu taushi, ya shirya jikinsa cikin natsuwa kamar babu abinda ya faru.
Daga nan ya nufi gado, ya shimfiɗa kansa kan babban pillow mai santsi, ya rufe idonsa cikin natsuwa.

Kamar wanda ya rasa nutsuwar sa, ya juyo gefe guda yana kallon bangon dakin.
A zuciyarsa yana tunani, rayuwar sa maiciki da kaddarah.

Ramlart da guduTa fado saman gadonta da karfi, ta juyo ta kwanta tare da kifa cikin ta a kan gadon, daya hannunta na rike da wayarta.
Tana fitar da numfashi da sauri, idanunta sun kada da sunyi jawur da hawaye .

cikin takaicin abunda AA Turaki ya mata tace
"Haba na shiga uku... Kamar ni Ramlart ya ke korata daga dakin sa? Ni matar auren sa!"

Cike da bacin rai Ta kamo wayarta, ta shiga contact ta danna sunan Zulya a cikin lambobin ta.
Bayan kiran ya shiga, tana Jin Zuly ta dağa tafara magana kawai cikin kunar zuciya.

"Zuly! Wallahi na gaji! Ni Turaki ya kora daga dakin sa kamar wata ‘yar aiki!"

ZULY ce tace .
"What?! Haba mana! Me kikayi masa har ya kai ga hakan?"
Chapter 6 · 0% Book details