← Book details Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 15

Sashe 11

Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka ya rika janta zuwa VIP section, inda aka kawata shi da curtains masu haske da d'aukar hankali ,nan fa ya shiga romancing din ta cike da kwarewa, a haka ramlart ta fita daga cikin haiyacin ta, har ya samu nasara ya biya bukatar sa, da ita, Bayan mintuna kadan, ramlart ta fito daga wajen gashinta sun dan bazu, murmushi take cike da gamsuwa.
Ramlart tana shirye-shiryen tafiya, tana gyara dan kwalin ta da d'an lullubin veil din ta, Gayen yana tsaye yana kallon ta da murmushi, yana da confidence irin na wanda yasan ta kan bariki, Wurin shiru ne, fitilar lounge din na launin ruwan hoda da blue suna ba da haske na musamman , wanda yake kara musu shauqi.

A hankali yake matsowa kusa da ita, yana kallon ta cike da shauki , yace.
"Kin cancanci fiye da haka, Ramlart… amma na bar miki wani abu a matsayin tunawa da wannan daren."

Ya ciro wata bundle na kudin kasashen waje – euro da dollars – ya saka a hannunta, sannan yace .

"Ga wannan… just for your time and your shine."
Ramlart ta karba, tana murmushi tana kallon sa da murmushin da ta saba amfani da shi wajen nuna farin ciki da yaudara.

Cikin d'an basarwa ramlart tace.
"Wannan fa ?."

Ya dauko wata karamar card mai sheki, ya mika mata. Akan card din: sunansa, lambar waya, da adireshin email ne.

Kallon ramlart yayi yace.
"Sunana Majeed Ibrahim Jatau, kuma mahaifina shine Honourable Senator Ibrahim Jatau – sanannen dan siyasa a kasar nan."

Ramlart ta zaro ido waje, sai kuma ta saki murmushi cike da farin ciki da burin sabuwar hanyar daukaka da ta zo mata a cikin sauki.

Tace.
"Oh wow… nice to meet you, Majeed."

MAJEED ne ya Dan matso kusa da ita.
"Kuma wannan – card ɗin nan – ya bude miki kowanne kofa idan kina bukatar wani abu let me know."
Yana gama fada'r haka Ya lumshe ido yana sumbatar goshin kafin yace.
"Let’s say this is not goodbye… it’s just the beginning."

Ya juya cikin class, na yara marassa jin magana, ya bud'e mota ya shiga. Ramlart ta tsaya tana kallon bayan motar na barin wajen, tana lumshe ido cike da tunani da wani sabon tunani a cikin ranta.

Zuly na jiran ta a gefe tana mata dariya.

“Na faɗa miki... wannan shine maganin ciwon tunani, amma kinbi zaki kashe kanki a banza akan wani da namiji.”

RAMLART ce ta busa iska a bakin ta tare da cewa .
“Hmmm, ai yanzu naji sauƙi. Let’s go... kafin wancan mutumin ya tashi ya san bana cikin gidan.”

Haka al'ameen ya yi driving d'in su, Suna isa bakin gate na gidan, Ramlart Ta gyara shigar ta, ta feshe jikin ta da turare sannan ta ɗan dafa hannun ta a jikin k'ofar motan.

ZULY ce ta sheke da Wani irin dariya tace.
“Ki tabbatar baki bar wani alamar da zata nuna cewa kin fita, club.”

RAMLART ce ta juyo tana kallon Zuly tace.
“Don’t worry. Nasan gidan nan fiye da yadda su ke tunani. Allah ya saka da alheri Zuly.”

ZULY ce ta daga gira tana dariya tace.
“Alherin club ko? Hahaha... Mun kusa cin nasara, bestie.”

Ramlart ta yi sallama da su, ta rufe kofar mota sannan ta ratsa ta bayan wani bangon ginin gidan inda take da wata sirrin hanya ta musamman da take shiga daga baya ba tare da an lura da ita ba, ta yi wuff ta shige ciki, A hankali, ta shiga gidan cikin nutsuwa tana duba gefe da gefen ta domin tabbatar da cewa kowa yana bacci, babu wanda ya ganta.

A dai-dai lokacin, ake kiran sallan asuba ya fara tashi daga masallacin anguwa dana cikin gidan AA Turaki, Gidan na cikin shiru, haka Ramlart ta kutsa kanta zuwa part ɗinta tana mai sauke ajiyar zuciya, dayiwa Allah godiya, naganin babu wani mahluqi da ya ganta.
Bayan shigan ramlart Cikin dakin ta, ta cire veil da takalman ta high heels dinta sannan ta zauna akan gado tana kallon kyautar kudaden da Majeed ya bata da card ɗinsa.
Wani murmushin jin dadi ne ya subuce a saman fiskarta a hankali ta furta.
“Senator’s son… hmm. Ramlart, kin soma samun hanyar da zata sa ki mallaki duniya, yadda kike so.”

Batare da ta gabatar da sallan asuba ba ta kwanta. Ba da jimawa ba, barci mai nauyi ya dauke ta.

💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫

✍️Mrs Alkali

Page 1️⃣1️⃣

Da gari yawaye, Ramlart na kwance akan gado tana kallon katin da Majeed ya bata. Ta duba sunansa a jikin katin: “Majeed Ibrahim Jatau– Son of Senator Ibrahim jatau, CEO MJ Holdings”. A gefe, an nannade wasu daloli da euros cikin wata leda mai kyau, ta sanya hannu ta d'auke su.

Wani irin shewa RAMLART tayi tace.
“CEO... kuma ɗan Senator... Hmmm! Wannan kam dama ce da ba zan bari ta wuce ni ba. In na rasa soyayyar ka, tabbas zanso nayi gogayyah da kai a wajen tara dukiya.”

Tana gama fada'r haka ta miƙe, ta nufi mirror tana kallon kanta. Tana murmushi da gamsuwa da kyan jikinta, wayar ta ta dauka Ta latsa layin Zuly, cikin magagin bacci zuly ta d'auki wayar.

RAMLART ne ta ce da Zuly ...
“Zuly... This guy is different. Yana da kudi, yana da matsayi, kuma yasan yadda ake treating mace. Ya bani cash da card... Can you imagine? Card!”

Dariya ZULY tayi tace..
“Toh fa! Kin ga kuwa muna kama hanyan, zama billionaires Yanzu sai ki dinga kula sosai, ki ƙara burgeshi – you never know, maybe kin samu sabon rayuwa daga can, kinga kema zaki shiga cikin jerin manyan, matan da za'a dinga gogayyah da su a kasar nan, kinga gara ki tsaya da kafafun ki kema.”

RAMLART ce tace
“Wallahi! Pha Ni dai yanzu zan dinga zama on standby. Daga Turaki sai Majeed. Duniya daɗi, kinga na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya.”

Tana fad'ar haka Ta kashe wayar tana dariya, sannan ta nannaɗe katin da kudaden, ta saka a cikin drawer dinta na sirri. Ta haye gado tana murmushi cike da farin cikin irin kamun da tayi.

GWARİNPA ESTATE

Yamma ce sakaliya mai cike da Wani irin iska mai d'auke da sanyi, Dr. Farida ce ta dawo gida cikin gajiya amma fuskarta na dauke da murmushi mai kwantar da zuciyar ,mai kallon ta, Tana daure da hijabi fari mai laushi, ta shiga falon gidan hannun ta na d'auke da jakar ta.

DADA ce ta fito daga daki
" Lale maraba da likita bokan turai, sannu da zuwa ya masu jinyan."

DR. FARIDA ce ta zauna a kusa da ita tace..
"Alhamdulillah Dada, wallahi naji dadin ganin Hajja ta samu sauki. Tayi responding da kyau sosai, kuma cikakken hanzari ne yasa ba ta shiga koma baya ba."

Murmurmushi DADA tayi tace..
"Allah yayi miki albarka, Allah ya kara kare ki daga sharrin masu sharri."

Ameen dada'amm cewar Dr Farida.

Ameer ne ya shigo cikin falon, yana dariya fiskar sa dauke da walwala yace.

"Ummi na, please… kice zamu fita yau! Kinga jiya Na gama exams, kuma yau Saturday ne!"

DR. FARIDA ce ta kalleshi da gajiya d'auke a saman fiskan ta amma hakan baisa murmushin saman fiskarta bacewa ba.
"Ameer ka bari gobe mana… Dada na gaji sosai."

AMEER ne ya hada hannuwansa alamar yana roƙon ta yace .
"Wallahi na yi alkawari da friend dina Ahmed! Dan Allah Ummi, koda minti talatin ne."

DADA ce ta kalli Dr Farida tace.
"To ki yi hakuri, ki kaishi mana, Bawan Allah yana jin dadin fita dake sai dai baki da lokacin sa."

Dr. Farida ta mike, ta nufi dakin ta domin canza kaya. Bayan lokaci kadan ta fito cikin simple gown mai launin blue sky, hijabi ta d'aura a akai wanda hakan ba karamin fito da ainihin kyanta yayi ba.

Murmurmushi DR. FARIDA tayi tace..
"To mu tafi… Amma wallahi minti talatin d'in kawai."

Haka sukayi bankwana da Dada sannan suka fita. Ameer ya bude mata motar, suka shiga ,Suka nufi wajen shan ice cream da fiskar su d'auke da dariya Nishad'i suna Dan taba hira tsakanin uwa da ɗa.

MAITAMA PARK

Ameer na shan ice cream cike da annashuwa yayin da Dr. Farida ke dan shakatawa a gefenta tana kallon sa tana murmushi.
wayarta ce ta fara ringing – emergency call daga hospital.

DR. FARIDA ta kalli sunan da ke kan screen din, ta d'an daure fuskar ta dan batayi tsammani ba.
"Ohh… My God."

AMEER ne yace
"Who’s calling Ummi?"

A hankali DR. FARIDA tace:
"Hospital ne, emergency ne. Amma…"

Cike da farin cikin jin hakan AMEER yace .
"Zamu je?! Zamu je asibitin da kike aiki?! Yessss!"

*Ta d'an kalle sa da mamakin yan da taga yana murna, sannan ta girgiza kai da dariya a saman fiskarta tace.

"To shikenan. Amma ka yimini alƙawari, bazaka sani headache ba, zaka nitsu bana son fitinah."

AMEER ne yace.
"Yes ummi nayi Alkawari!"
Haka ta shiga Motar ta ta juya da sauri, ta d'auki hanyar da zata kaisu hospital, duk da cewa ba haka Dr. Farida ta tsara ranar ta ba. Amma ya zatayi, haka taci gaba da driving d'in su, shi dai Ameer sai murna yakeyi for the first time da zai je asibitin da ummin sa take aiki , sabi da haka ya kasance cikin farin ciki.

Bayan wani lokaci, Dr. Farida ta kammala duba marar lafiyan da da aka kawo a bangaren gaggawa wato emergency Ward. Hannunta dauke da medical file, fuskarta cike da gajiya amma annurin fiskar ta yana nan bai bace ba. Tana tafe a hankali tare da Ameer a gefen ta, wanda ke kallon kowane sashe na asibitin cike da sha'awa. dakin da Hajja ke kwance Suka nufa, bayan an mayar da ita VIP room saboda saukin ciwon da tafara samu.

AA Turaki na zaune a gefen gadon, cikin manyan kaya masu tsari, fuskar sa cike da nutsuwa, amma akwai alamun damuwa, a tattare da ita. PA dinsa, tsaye a gefe yana duba wayar sa lokaci-lokaci. A gefen gadon, Hajja na zaune cikin rigar asibiti, tana dan dariya da alama wata maganar ce ta sata dariya d'an hira suke d'an tab'awa ita da d'an nata.
Chapter 11 · 0% Book details