Sashe 4
Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na san yaron nan bai ya son wannan auren , Bai taɓa soyayya da ita ba, Ka duba yadda damuwa ke bayyanuwa a fuskar sa, a mai makon ya samu nitsuwa da farin ciki.
Biyayya ce kawai ta sa ya auri Ramlart, Bai dade da dawowa daga asibiti ba, yanzu, amma kallon sa da nayi ya bayyana yanda zuciyarsa ke cikin rauni, da tashin hankali ko da kuwa bai furta hakan da bakin sa ba ni mahaifiyar sa ce ina iya fahimtar sa koda kuwa baice komai ba".
A hankali Ta share kwalla da gefen mayafinta.
"Duk da cewa ya a zabtu a baya kuma ya jure, amma na tabbata yana cikin azabar rashin haihuwa, a halin yanzu."
Cikin hanzari Alhaji ya miƙe damuwa na sake baiyana a saman fiskan shi, yace:
"Kull kull kull, Habiba! Nace maki kar na kara jin wannan zancen. Kaddara? Me yasa kike kokarin tona abin da muka rufe da addu'a a tsawon shekaru? Wannan irin maganar taki ne kike so ya jawo mana matsala, gaskiya?"
Saba babban rigan sa yayi da sauri Yana tafiya a cikin falon, ya Dan tsaya yana kallonta da fushi amma cike da d'an rudani yace
"Mu da muka rasa mafita sai muka yanke hukunci mai nauyi, yanzu kina kokarin dawo da tunanin da muka binne da hawaye? Wallahi bana son jin wannan zancen a cikin gidan nan!".
Ya Dan numfasa da ƙyar, yana ƙoƙarin kwantar da zuciyarsa, yace
"Wannan fa yaro ne da nake alfahari da shi, mai hankali da mutunci, karki manta yana da kima da da raja a idon duniya, Sai mu ɓata masa goben sa saboda abinda muke ɓoyewa a baya? Wallahi Habiba, ki dakata da wannan shirmen na kin."
cikin murya mai rauni Hajja tace:
"Toh me kake so na yi? Zuciyata cike take da tsoro… kai ka kalle shi, yaushe rabon da na ga ɗana yana dariya da walwala na gaske? Me zai hana na firgita, Abdullahi?" Ta karasa maganar tare da kiran sa da asalin sunan sa .
Shiru ya sake cika dakin, na yan mintuna.
Alhaji ne ya share gumin da ke kansa da hannunsa, a lokaci guda ya kalli matarsa cikin kallo mai zurfi,da nazari, amma bai ce mata komai ba, Sai ya juya a hankali, yana tafiya zuwa dakinsa, zuciyar sa cike fall da damuwa.
Ba zato ba tsammani taji saukar Muryar sa.
"Ki ci gaba da addu’a, Habiba, Wannan kadai ce mafita da muke da ita a halin yanzu."
Yana gama fada'r haka Ya fice ya bar ta a falon, tana kallon bayansa, a hankali ta runtse idonta , hawaye na rige rigen gangaro wa a saman fiskan ta.
A cikin katafaren dakinsa mai fadi da tsari, a hankali ya shigo , fuskarsa cike da damuwa, da nauyin abinda Dr. Farida ta sanar masa.
Dakin nasa na alfarma ne, wanda yasamu gidauniyar ginin zamani, mai tsarin luxury design, tiles d'in dakin masu haske ne ,gadon nasa King-size ne, mai dauke da gadon fata da lallausan katifa , TV screen mai fadi,manne a bango, fitilun da ke fitar da haske mai launin fari da light blue ga kuma zane-zanen classic art manne a bangon dakin.
Aword da abubuwan kyauta daga kasashen waje suna shimfide akan wasu shelf na ado .
A gefe kuma akwai wardrobe din zamani wan da ake bude ta da fasahar "fingerprint".
Cikin nitsuwa ya tsaya a gaban madubi, yana kallon fuskar sa dake nuna alamun gajiya, damuwa, da tsantsar karfin zuciya, a hankali Ya dafe kansa kadan, sannan ya fara tafiya toilet ya shiga domin yayi wanka.
Wankan sa ya yi da ruwa mai dumi, da sabulun sa mai kamshi wanda yake odern sa daga Qatar, sannan ya fito yana sanye da farar doguwar rigar sleeping gown mai laushi, da santsi.
Bayan ya fito, ya shimfida dadduma a wani sashe na dakin da aka ware don sallah, Ya rama sallolin da suka wuce shi, ya karanta addu'oin sa cikin kwanciyar hankali, Bayan kammalawa, ne ya zauna na dan lokaci cikin shiru mai karfi, yana tunanin abinda ya faru d'azu a asibiti.
Zuciyarsa ce ta buga sau daya da karfi, Ya jingina da bango, sannan na dan Wani lokaci a hankali ya mike da d'an sassarfa ya nufi wata madai dai ciyar drawer da aka kulle da key, ya bude ya dauko Wani d'an kwandon da ke d'auke da kwalabe, na magunguna, a ciki ya zabi daya sannan ya sha, yana kallon maganin kamar wan da yake son tambaya: "Shin yaushe zan daina shan wannan magungunan ne?". Ya tambayi kansa.
Bayan ya sha maganin, hayewa yayi kan gadonsa mai laushi, gadon da aka lullube da farin duvet mai dumi sosai, da kamshi na musamman.
Cikin nitsuwa Yayi kwanciyar shi yana kallon silin d'in dakin, idanunsa na cike da hasken da ke kunshe da zafi da tarihi na shekarun baya.
Kafin ya ankara, wani bacci mai nauyi ya dauke shi, sabi da maganin da yasha ma yana saka bacci, ga gajiya da ya taru masa.
Nan take ya lula duniyar mafarki in da ya dauke shi, zuwa shekaru 21 da suka wuce lokacin kuruciyarsa, abubuwan da ya tsananta yarda cewa ya riga ya manta da su, ya gama shafe su a babin rayuwar sa sai ga shi a kullum in ya kwanta bacci sai sun dawo masa a mafarki.
💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 3️⃣
Aliyu Abdullahi Turaki shi ne cikakken sunansa wan da akeyi wa lakabi da AA Turaki, in da mahaifiyar sa kuma take kiran sa da suna "Yero" kasancewar sa d'an fari a gunta kuma da d'aya tiloh a gurin su, Alhaji Abdullahi Turaki bafulatani ne daga rugagen Gembu, cikin tsaunukan Mambila Plateau, wanda ya tashi cikin arziki na noma da kiwo asalin Mahaifinsa makiyayi ne mai daraja, amma daidai gwargwado ,mutumin kirki, ne amma babu isasshen ilimi, sai tarbiyya da gaskiya a wanchan lokacin.
Aliyu tun yana yaro, yana da hangen nesa da kwadayin canza rayuwarsa da ta iyayen sa, Duk da halin rashin wada ceccen ilimi da suke ciki a yankin su, haka ya dage da karatu yana tafiya makarantarsu mai nisan gaske daga gida, a koda yaushe, kafin wata ƙaddarah ta gifta musu, su ka baro ainihin yankin su sukayi hijira zuwa garin kano, anan garin kano ne Aliyu yaci gaba da karatun sa na secondary bayan doguwar jinya da sha fama da ita wanda iyayen sa suka cire rai da tashin sa cikin ikon Allah da karfin addu'ar su Allah ya sake daga kafad'un sa sai dai ya kamu da ciwon zuciya da ake kira da mild heart condition, saka makon damuwa da ba'cin rai da ya shiga a baya.
Bayan ya kammala karatun secondary school, da sakamako mai kyau, ya fito sabi da kwazon sa, a haka ya samu ya jona jami'ar Ahmadu Bello University , in da ya karanci business administration, bayan ya kammala ne ya fito da result in da ya zama first class ya samu scholarship daga wata NGO, Bayan ya gama digirin sa na farko, ya samu damar zuwa UK inda ya yi Master’s a fannin International Business Management a London School of Economics, bayan nan ne ya jona degree din sa na uku a UK wato Phd , bayan haka ya karbi horo na musamman daga Executive Education domin kara kwarewa a harkar jagorahn ci da nazarin kasuwan ci, Daga nan ne rayuwa ta fara sauyawa, inda yafara halartar tarurruka na musamman kamar su , project management profession, Business networking, digital marketing da sauran su.
Yana da kwarewa, hikima, da iya sadarwa da kowa, hakan yasa bayan ya dawo Najeriya, ya kafa kamfanin farko mai suna Turaki Global Ventures, wanda ya fara da kasuwancin shigo da kayayyaki daga kasar China da Turkey.
Zuwa cikin shekaru 10, AA Turaki ya zamo jigo a harkar kasuwanci a Afrika.
Yana da manyan kamfanoni a fannoni da dama kamar su:
- Turaki Holdings Ltd – kamfani na kudi da hannayen jari
- Turaki Oil & Gas – yana da rijiyoyin man fetur a Najeriya da Angola
*Turaki Real Estate – gini da mallakar manyan gine-gine a Dubai, Abuja, Accra, da Istanbul
- Turaki Agro & Food Ltd – kamfani mai sarrafa kayan gona da fitarwa zuwa waje
- Turaki Airlines (JV project)– wani kamfani da ke tattaunawa da gwamnatin kasar Qatar akan kafa jirgin sama
Duniya ta sanshi a matsayin "Africa's Silent Billionaire", saboda hankali da natsuwarsa, baya shiga barkwanci da fallasa sirrin rayuwar shi.
Hukumar Najeriya (Federal Government),ta ba shi lambar girmamawa, saboda gudunmawarsa ga ci gaban tattalin arziki, har ta zuba hannun jari a daya daga cikin kamfanoninsa na makamashi da man fetur.
Kasashe kamar UAE, Turkey, UK, China, Qatar, da Saudi Arabia suna da hannun jari a kamfanoninsa – sannan ya kasance memba ne a International Business Council.
Tattaunawarsa da kasashen duniya kan batutuwan kasuwanci da cigaban Afirka sun sa ana kiransa "Voice of Emerging African Capitalists".
5 YEARS BACK...
A lokacin da harkokin sa su ka kan kama ,zuwa wannan lokacin AA Turaki ya zama babban business tycoon a Africa baki daya, zuwa lokacin ya tattara iyayen sa sun koma Abuja da zama, duddah shi kan sa bai cika zama a Nigeria ba.
Hajiya Habiba wacce yake kira da Hajja tana zaune a kan kujera mai lallausan fata, a hankali ta gyara mayafinta .
Aliyu Turaki ne zaune a gaban ta ya na zaune cikin natsuwa, yana sauraron mahaifiyarsa.
da murmushi Hajja tace
"Yeroh yau kimanin shekara talatin da biyar fa kayi... Ba aure lokaci yayi da zaka samu mace mai tarbiyya da zaka kira taka.
Ga Ramlartu nan ’yar kawata ce, naga halinta tun tana da hankali naya ba da halinta.
Yarinya ce mai ladabi da hankali. Kuma ta na girmama ka sosai, uwa uba kuma tana mutuwar son ka."
Cikin nitsuwa Aliyu ya dago kai kadan, ya kalli mahaifiyarsa, sai ya sauke ajiyar wata nannauyan ajiyar zuciya.
"Ina jin ki Hajja, Idan kina ganin hakan shine mafi alheri, a gareni na yarda da zabin ki."