← Book details Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Abdullahi Turaki ne ya gyara zaman sa tare da cewa:
"Alhaji Musa, Hajiya Rakiya… akwai wani al’amari mai nauyi da ya shafi ‘yar mu wato Ramlartu .
Wani irin bugawa ƙirjin ramlart yayi ,har wani jiri jiri take ji yana kok'arin ibanta, da kyar ta iya seta kanta, duk wani addu'a da yazo bakin ta karantashi kawai takeyi, jin Baffah yaci gaba da cewa"Mun tabbatar da cewa ita ce ta sakawa Hajja wani sinadari a abinci, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyan Hajja a asibiti…"
Kuma Likitocin sun gano hakan ne ta hanyar gwaji inda board na asibitin suka had'a meeting naganin cewa sun tsanan ta bincike angano mai laifin, ganin hakan ne yasa Aliyu ya nemi alfarma yadakatar da su inda ya tabbatar musu dacewa zai dauki mataki da kan sa, bayan bincike da aka gudanar ansamu ganin hoton Ramlartu ta cikin CC camera in da aka tabbatar da cewa ita ce ta aikata hakan ,hakan ne ma yasa mijin ta ya umarce ta da ta dawo gida, toh kaji wannan ne dalilin zuwan mu .

Ai a lokacin baba ji yake kamar lokacin ya tsaya masa baya tafiya, kowa dake dakin yayi shiru har Aunty hauwa da ta cika musu gaban su da abubuwan motsa baki cike da mamaki suke kallon ramlart dake rakube a gefe kamar muna fuka. Ramlart na rakube a gefe, ta sunkuyar da kai kasa.

Cikin fishi Alhaji Musa ya kalle ta fiskar nan babu alamar rahama a tattare da ita cikin tsawa yace.
"Ramlart! Wannan ai ba laifi bane kawai, wannan keta mutunci ne da rashin hankali! Abinda kika aikata ya wuce a yafe miki da cikin sauki, kisan kai fa kike kok'arin yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un baba ya kara maganar cike da rauni."

Cikin kuka Mami tace"Na yarda da tarbiyyar da muka baki ba haka take ba. Me ya rinjaye ki har kika aikata hakan?"

Cikin bacin rai Aunty Hauwa ta matso tare da zabga mata wani lafiyayyan mari, wan da yasa jinta ya d'auke na wucen gadi, ta sake dağa hannun ta zata sake zabga mata taji Baffah yace kull kull hauwa'u barta haka, ai shi duka baya gyara sai dai ma ya sake lalatawa dan haka addu'a zaki mata, Wani irin kallon zamu had'u Aunty hauwa ta mata tare da cewa.
"Na rasa dalilin da zai sa ki hallaka kanki da hannunki. Wannan kuskure ne babba!, kuma ina mai tabbatar miki da sai kin girbi abunda kika shuka."

Cikin miryan kuka Ramlart tace "Na tuba… na yarda da kuskurena. Don Allah ku yafe mini…wlh sharrin shaidan ne bazan karaba wlh na tuba."

Cike da ta kaicin ta Alhaji Musa ya juya zuwa ga Alhaji Abdullahi Turaki yace ."Wallahi in har wannan abun ramlart ta aikata , to sai dai ta zauna a nan gidan. Ina son Ka umarci Aliyu da ya sauwake mata ta dawo nan ta zauna … tunda ta zubar da mutuncin ta."

Cike da jin nauyin shi Alhaji Abdullahi Turaki yace "Alhaji, ba karamin nauyi na ji ba, dana kawo maganar gaban ku sai dai kuwa ba yadda zanyi ne ya zama dole kusan da maganar a matsayin ku na iyayeh a gare ta. Amma ina rokon ku daku dubi girman zumunci, da girman mutuncin mu, ku yafe mata. Mu ma muna bakin cikin faruwar hakan. Amma in ba damuwa, a bata dama ta biyu ta gyara. Allah yana yafe wa bawansa, mu ma mu yafe mata, hakan zai sata ta gyara kura kuran ta na baya."

Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli AA Turaki wanda bai ce komai ba, kamar ma wanda baiya wajen.

Cikin nitsuwa Hajja tace "To… kamar dai yadda Alhaji ya fad'a Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare kuma ace mu bayin sa , dan haka nima na yafewa ramlartu ,Amma fa wannan kuskuren ba ƙarami bane, sabi da haka saita kiyaye gaba duddah har yanzu bamu san dalilin ta na aikata hakan ba."

Shi dai AA Turaki bai ce komai ba, sai ma wayar sa da ya ci gaba da dannawa, amma a chan cikin kasan zuciyar sa bakaramin haushi yake ji ba, a zaton sa Hajja zata sa ya rabu da ramlart amma sai gashi sun buge da yafe mata, duddah iyayen ramlart sun chanchan ci fiye da haka a wajen su dan ba karamin girmama su yake ba sabi da karamci irin nasu, sai dai duddah haka albasa batai halin ruwa ba.

Cike da borin kunya Ramlart ta taso ta durƙushe a gaban iyayenta da iyayen mijinta, fuskarta cike da hawaye. cikin rawar murya tace"Na gode… Na gode da wannan dama da kuka bani. Nasan Ban cancanta ba, amma duddah haka kun yafe mini. Allah ya saka da alheri, zan gyara halayena, wallahi zan gyara..."

Hajja ta tab'e baki tace"ai kuwa kam gara Ki gyara Ramlart, kada ki sake kuskuren da zai sa mu zubar da hawaye saboda ke anan gaba."

Cike da tsantsar girmama wa Alhaji Musa kalle su yace "To amma ina da wani sharadi. Ramlart ba zata koma gidan mijinta yanzu ba. Zata zauna a nan gidan tare da mu na wani lokaci... har sai Aliyu ya sami wata matar da zai aura. Na yi alkawari , zan nema masa auren mace ta gari. Sai ya auri wata, sannan sai Ramlart ta koma d'akin ta Wannan shine hukuncina a gare ta."

A hankali AA Turaki ya d'ago ido ya kalli iyayen nashi a karo na farko tunda ya zauna a falon cikin shiru, zuciyarsa cike da rudani da nauyi, jin hukuncin da Baba ya sake yankewa, Hajja ta kalleshi da damuwa dauke a saman fiskan ta sabi da tasan an sake jefa rayuwar d'an ta a cikin tsaka mai wuya, tana tuna auren Ramlartu ma da yaya ya amince bare kuma wani auren a karo na biyu.

Cikin hikima Hajja tace"Alhaji Musa, wannan hukunci mai nauyi ne, amma ka nuna mana karamci da adalci. Allah ya saka da alheri."

Alhaji Abdullahi Turaki ya gyara zama kafin yace"Mun amince da hukuncin ka, kuma muna godiya da fahimta da muma karɓan uzurin mu da kayi."
Baffah ne ya Kalli Aliyu ya ce"ina ce kaji hukuncin da mahaifin ku ya yanke, ina fatan ka fito da matar auren ba da jimawa ba".
AA Turaki ne ya ɗago ido ya na kallon kowa, dake cikin falon ba tare da furta kalma ba, ya sauke kan sa kasa, A zuciyarsa kuwa, ya kudirta cewa kasar ma zai bari gaba daya… ba auren da yake so, kuma zuciyarsa har yanzu cike take rauni da kuma dacin abun da yafaru da shi a shekarun baya, sabi da haka bazai yadda ya sake wani auren ba.

Ita kam ramlart duddah hukuncin da Baba ya yanke bai mata dad'i ba amma a hakan ta daure zuciyar ta dan tasan taci darajar su Baffah ne da yanzu ba wannan maganar ake ba , duddah tana tunanin cewa su baba basu hakura ba, ga Mami dake gefe guda tana ta kuka tun d'azu da taji abunda ramlart d'in ta aikata, Aunty hauwa ma tana zaune a gefe tana hararan ramlart d'in, da ba don idon su Hajja ba da sai jikin ta ya gaya mata a hannun ta yanzu ma bata tsira ba jira take su Hajja su tafi .
Bayan Wani lokaci su Baffah suka musu sallama, haka su rabu cikin mutunci da girmama juna.

Bayan tafiyan su Hajja ne Mami tasa Aunty hauwa ta jarawa ramlart zama dan acewar dama jira take su Hajja su tafi, babu bata lokaci Aunty hauwa dake jin haushin ta tafara sauk'e mata gajiya ,duk abunda ake yi baba bai hana ba hasali ma yaji dad'in hakan, bayan Aunty hauwa ta gama kumburawa ramlart jiki ne , Baba ya sake kafa mata sharrudan shi, yace duk wani aiyukan gidan daga yau itace maiyin su, hatta da sharan tsakar gidan nasu, haka ramlart ta ja jikin ta ta wuce d'akin ta jikin ta duk ya mata tsami.

🔚 ƘARSHEN FREE PAGES!

_Ahamdulillah, a nan nakawo ƙarshen Free pages... Amma tambayar ita ce:_

Shin ƙauna zata iya shawo kan kaddara?
Ko kuwa kaddara ce zata wargaza ƙauna? 😢💔

Wane mataki AA Turaki zai ɗauka bayan sake ganinta?

Shin wace yarinya ne AA turaki yake yawan mafarkin ta ?

Shin zai sake had'uwa da ita shin wace kaddarah ce ya ke gudu?

Ramlart zata iya samun yafiya daga zuciyar AA Turaki?

Shine da gaske ramlart tayi nadama?

Shin Ya alak'ar ramlar da majeed İbrahim jatau?

Shin sabuwar soyayya zata iya dinke tsohuwar rauni?

Ko kuwa sabon masoyi zai bayyana daga inda bamu zata ba?

Shin AA turaki zai sake aure a karo na biyu?

Shin wacece Dr Farida?

Mene yake kunshe a cikin rayuwar shin da gaske Ameer dan ta ne?

Shin zata auri Dr İmam?

Shin wani sirri ne su Hajja su ka boye shekaru 21 baya?

Mene musabbabin ciwon zuciyar AA turaki?

Shin wannan ƙaddarar soyayya ce ko hukunci?

Shin da zuciya Daya zuly take son ramlart?

🔥 *Zuciyoyin ku na da ƙarfi?*
_Toh ku shirya domin zuwan sassan da za su girgiza zuciya, su tada hankali, su raunana jiki…_

*📌PAID PAGES sun kusa farawa immediately zamu fara!*
📍Farashin littafi: *₦500 kachal!*
📍PROMO: *₦300* kacal nan da sabuwar shekara!

*🟢Zaki iya Biyan kuɗin ki ta: 7025348616 (Opay – Sakina Ahmad Musa)*
*📲 A turo shaidar biyan kudin ta WhatsApp: 07025348616*

Kokuma kije arewapen ki biya ki karanta complete.
👇👇👇👇👇👇👇
https://arewapen.com/u/mrsalkali01

1. Idan kai ne AA Turaki, zaka iya yafe wa macen da ta kusan halaka mahaifiyarka?
2. Wane hukunci kaddara zata yanke tsakanin ƙauna da laifi?
3. Shin yafe wa alamar rauni ne ko ƙarfin zuciya?
4. Idan soyayya ta mutu, shin zata iya farfadowa?

5. Shin wata mace zata iya jure irin jarabtar da Ramlart ke ciki?

*Nasan akwai tarin tambayoyi dake ranku daban daban ku dai ku biyo NI sannu-sannu in sha Allahu ba zaku yi nadamar biyan kudin ku ba, akwai chakwakiyoyi da yawa a gaba*

*"Labarin bai fara ba tukunnah… yanzu ne tafiyar zata fara da gaske!*
Me kike jira, Hajiya ta? Hanzarta kibiya naki domin kasancewa cikin masu kwasar:
**Zallan ilimi,
Darasin rayuwa,
Nishadi da fadakarwa,
Gwagwarmaya a soyayyah,
Sadaukarwa,
Zallan kaunah,
Kaddara,
Da kuma tsaftatacciyar soyayya mai tsayawa a zuciya!**

Wannan ba kawai labari ba ne — *ƘAUNA DA KADDARAH* ce!
Labarin da ba za ki karanta ki manta ba!"

*_SAI NA JIKU YA'N AMANA_*

*🖋️ RUBUTAWA: UMMUH EYSHAL (Mrs. Alkali)*
*📖 ƘAUNA DA KADDARAH – _Labarin da zuciya zata karanta kafin ido ya Fara gani!_*
Chapter 15 · 0% Book details