← Book details Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gently,sukaji ana buga kofar dakin, a hankali kuma aka turo kofar.
DR. FARIDA ce ta shigo cikin murya mai sanyi tace:
"Assalamu Alaikum."

HAJJA ce ta washe baki , fiskar ta d'auke da farin ciki ganin ta, tace:
"Wa alaikumus salam. Masha Allahu! Gata nan! Doctor Farida… laleh maraba da yâr albarka!"

Cike da sakin fiska Dr. Farida ta karaso , sannan ta matsa kusa da Hajja tana kallon fuskar ta , cikin sakin fiska tace

"Alhamdulillah, naji dadin ganin ki cikin walwala, Hajja. Hakan Yana nuna alamar sauki yafara samuwa, alhmdullah!."

HAJJA ce ta kamo hannunta, tace:
"Ke kika cancanci godiya. Allah ya saka miki da alkhairi. Nagode kwarai da gaske , Allah yayi albarka."

Cike da girmamawa Dr Farida tace.
"Ameen Hajja nima nagode da addu'a".

AA Turaki ne ya dago kai yana d'an kallon su. Jin yanda Hajja ta sake da wannan likitar saikace sunjima da sanin juna.

A dai dai wanna lokacin ne Ameer ya shigo d'akin bakin sa dauke da yar karamar sallama, daman ya dan shiga restroom ne , shiyasa Dr Farida ta fad'a masa numbern dakin da zai same ta in ya fito.
Hajja ce ta d'an juyo ta kalleshi, tare da cewa.
"Shi kuma wanene wannan yaron wa yake nema a nan?"

Dr. Farida ce ta kalli Ameer, ta dan sosa gefen kanta tace.

"Danane… Sunansa Ameer."
Hajja ce ta washe baki tare da sake kallon Ameer tana murmushi tace.

"Ay mashaa Allah. Yaron ki ne, Abu yayi kyau, Kai yaro, zo nan."ta karasa maganar tare da yafito Ameer da hannun ta da baya d'auke da drip.

Cike da ladabi Ameer ya karaso , ya gaishe da ita. Hajja ta amsa cike da fara'a a saman fiskar ta tace .
"Allah ya raya shi ya sa ya zama abin alfahari kamar mahaifiyarsa."

Murmurmushi Dr. Farida tayi tare da zama a kusa da Hajja, tana kallon result din na'urar dake recording din lafiyarta.

A hankali Dr Farida ta Kalli Hajja tace.
"Masha Allah, an samu cigaba sosai jiki na ta samun lafiya, may be nan da dan wani lokaci za a iya discharge d'in ki , sai kici gaba da karb'an drugs daga gida".

Hajja ce tace "alhmdullah nagode wa Allah, kin ga yanzu ya ke cemin ya kama ta a sallame ni haka , kin san shi yafi son a kula dani a gida, Hajja ta karasa magabar cike da barkwan ci".

Jin abun da Hajja ta fada ne yasa Dr Farida ta d'an juya ta kalla direction da Hajja ta nuna mata da yatsa.

Wani irin dumm dumm gaban ta ya yanke yafad'i , ganin mutum , a zaune a gefe d'aya, fiskarnan a murtuke ba alamar fara'a kan sa a sunkuye sai danna wayar sa yake hankali konce kamar ma baisan da wanzuwar su a cikin d'akin ba.

Sani PA dinsa na tsaye a dan gefe da shi.

Ameer ya kalli wajen shima, sake rufe idanun sa yayi ya kara bud'e su, ganin kamar a mafarki ,yau gashi ga role model din sa a go aban sa zahiri muraran ba a cikin TV ba ,kamar yanda ya saba ganin hirarrakin sa a gidajen tv, da sauri ya matso kusa da AA Turaki cikin ladabi, jin dadi yace.

"Good morning, sir."

Cikin mamaki AA Turaki ya dago kai , yana kallon yaron. Wani kyakkyawan yaro ya gani a tsaye a gaban sa , bai san san da wani murmushi mai nauyi da kwarjini da annuri ya bayyana a saman fuskarsa,ba, cikin nitsuwa da kamewa yace.

"Good morning, young man, how are you doing.
Cikin murna Ameer yace.
"I'm fine sir."
"Kullum ina kallonka a TV Sir , yau kuma gashi na gan ka da ido. Kai ne Mr. AA Turaki, ?" Ya karasa maganar cikin sigar shirme irin na yara masu kananun shekaru.

Wani irni cute smile ya sake masa.Wannan karon murmushin nasa ya kara bayyana, sosai har Dr. Farida da ke gefe ta kura masa ido ba tare da tasan da hakan ba,tana mamakin yadda fuskar sa ta canza da annuri, a lokaci guda.Ganin haka, sai ta dan janye idonta cikin kunya, ta kawar da kanta gefe.
AA TURAKI yana kallon Ameer, yace Mr young man:
"To ya sunanka?"

Cike da farin ciki AMEER yace sunana.
"Ameer."
AA TURAKI ne ya dan shafa kan shi kafin yace:
"Ameer... Nice name, kana da guts. Me kake so ka zama nan gaba?" Ya jiho masa tambayar a bazata .

Wani irin dad'i ne ya ziyarci AMEER jin tambayar da AA Turaki ya ke masa, cike da yaranta yace:
"Ni ma ina so in zama business tycoon kamar kai. In yi kasuwanci a duniya, in taimaka wa mutane da yawa."

AA Turaki ne ya dago hannun sa ya dafa kafadar Ameer, cikin murmushi wanda ya ke fitowa daga kasar, zuciyar shi. Hajja ce ta kalle su, idonta cike da mamaki d'an nata ganin ya sake da yaron a lokaci guda, ji tayi Ameer ya sake kwanta mata a rai, sai taji ina ma ace Ameer jikanta ne.
Tun shekaru 21 da suka wuce baya bata sake ganin murmushin a saman fuskarsa ba sai yau da ya had'u da Ameer.Wannan yarinya... da yaron nan, suna da wani abu mai karfi a tattare da su.” nan taji Dr Farida ta dad'a burgeta.

Cikin nitsuwa, AA Turaki ya zaro wallet dinsa ya dauko bandir din kudi da wani card mai design dake d'auke da sunansa na Musamman. Ya mika wa Ameer, tare da ce masa.
"Ka rike wannan. Za ka iya tuntubata duk lokacin da kake bukatar shawara. Na yarda kai yaro ne mai cike da buri."

Cikin farin ciki Ameer ya karba ,a lokaci guda ya ruga da gudu ya rungume Dr. Farida yana fadin “Thank you, Ummi!” yau kinsa na had'u da roll model d'ina.

Hajja ce ta kalli Dr Farida da murmushi, d'auke a saman fiskan ta,cikin tausayi ta ce:
"Doctor, dan Allah... wa ya haifi wannan yaro? Ina son in san mahaifinsa." Haka kawai naji kun kwantamin a rai, ina jin Ameer kamar jikana wlh.
Dr. Farida ta dan saki numfashi, ta sosa gefen gashinta cikin nutsuwa tace.
"Mahaifin sa Ya rasu tun yana karami... A yanzu ni da mahaifiyata muke kula da shi."
Hajja ta dafe zuciyarta cike da tausayawa, tace .
"Subhanallahi...!Allah ya jikansa. Yaro irin wannan... dole ka yi alfahari da shi." Nasan da mahaifin shi yana raye shima zai yi alfahari da shi.

Jin yanda Hajja ta dage tana ta zuba surutu ne yasa ,AA Turaki ya mike tsaye tare da PA dinsa.

yana kallon Hajja yace .
"Hajja Zan dawo daga baya , ki huta, lafiya."

Ya da. matsa kad'an,ya kalli Ameer da murmushi, kad'an sannan ya daga masa hannu, irin bye bye d'in nan sannan yace .
"Be good, Ameer. Ka kula da kanka sosai."

Dariya AMEER yayi yace
"Yes sir!"

Bai sake cewa komai ba, daga haka Suka fita tare da PA dinsa, yana tafiya cike da wani nau’in annuri da su kan su bodyguard din sa ba su saba gani a tare da shi ba.

💫 ƘAUNA DA KADDARA💫

✍️Mrs Alkali

Page 1️⃣2️⃣

Zaune yake a cikin babban falon sa, ya lumshe idanun sa yana nazari. Wayarsa na riƙe a hannunsa , tunani yake yi a game da ciwon Hajja , jin wayar sa ta fara ringing ne ya sa shi bud'e kyawawan idanun nashi a hankali ya duba wayar , ganin sani PA ne ke kiran nashi yasa shi yin picking call din cikin girmamawa PA ya gaishe shi,bayan gaisuwar ne ya d'aura da cewa.
"Mun samu access din CCTV footage na kitchen din Hajja! Kamar yadda ka bukaci a duba ranar da Hajja ta kwanta ciwo..."

A hankali ya sauk'e ajiyar Zuciya, cikin wata irin Murya yace.
"Ina bukatar flash drive d'in yanzu".
Yana gama fada'r haka ya kashe wayar, ba a fi minti biyu ba sai ga sallaman PA, bayan ya samu izinin shigowa ne , ya mika masa wani flash drive yana fadin:
"Yes sir, an aiko mini da shi kai tsaye daga Head of Security. Ba wanda ya san da wannan footage din." Ganin ya karb'a flash d'in ne yasa sani PA yimasa sallama ya wuce.

Karb'ar flash d'in yayi tare da saka flash din a laptop din sa, dake ajiye a table din dake gaban sa. A hankali ya latsa play. Kamera ta dauki cikakken lokacin da aka dafa tea na Hajja. Sai gashi a cikin video, ya bayyana mace sanye da veil ,tana had'a tea. Ta zuba wani abu a cikin flask din tea, ta juya ba tare da an hango fuskarta sosai ba.

A hankali , ya kame zuciyarsa, ya saki Wani irin huci, baya son hasashen shi ya zama gaskiya, matsa play forward yayi tare da sake zubawa laptop din idanun sa...

A lokacin da ta juyo kafin ta fita dağa cikin kitchen din, fuskar ta bayyana kadan , Wani irin bugawa zuciyar sa tayi, tabbas wannan fiskar Ramlart ce, hasashen sa ya zama gaskiya baya bukatan karin bayani.

A hankali,ya dağa kansa yana jin jikin sa ya dau sanyi. Zuciyarsa ta na wani irin bugawa da karfi. Idanunsa sun kada, a lokaci guda,hannunsa ya dunk'ule da karfin gaske, yana jin kamar ya fashe da ihu, ko zai ji saukin abunda ya taru masa a cikin Zuciya.

Magana yake da zuciyar sa
"Ramlart...? Me Hajja ta mata take son hanlakata...? "
Ya dafe kansa, dake barazanar fashewa.Duniya ta fara juyawa a idanunsa. Hankalinsa ya tashi. A lokaci guda, ya gane cewa rayuwar, Hajja ya shiga cikin hadari , tabbass in dai har ramlart zata iya aika tawa Hajja haka tabbas mata ba abun yarda bane duba da yanda Hajja take son ta, hasalima ita ce tayi sanadiyar auren su, don shi baiga abunda zaiyi da ramlart ba, ya aure tane bisa umarnin Hajja amma kuma abun da yagani ya basa mamaki, meya sa Ramlart ta ke son cutar da Hajja tabbas akoi wani abu daya kamata ya sani .
Chapter 12 · 0% Book details