← Book details Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin sanyi da nauyin damuwa ya sauka a zuciyar sa, sunkuyar da kan sa kasa yayi, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, tamkar ana tsaga masa kirji ji yake yi kamar ciwon sa na barazanar tashi .

“Why… why would she do that?” Ya furta ƙasa-ƙasa batare da sanin cewa maganar ta fito waje ba.

Dr. Farida ne ta ce :

“There could be a thousand reasons. Fear. Pressure. Regret. But for now, she needs healing — physically, emotionally, and spiritually. And she needs you more than ever.”

Turaki ya dafe kansa, numfashinsa ya yi nauyi. a hankali yace:

“So… there’s no hope?”

Dr. Farida ta kalli sa kai tsaye:

“I didn’t say that. There are assisted options. But it will take time, patience, and strong commitment. From both of you.”

Ya lumshe idanu, sannan ya ce:

“Thank you, Doctor… for your honesty.”

Dr. Farida ta gyada kai tace:

“It’s painful, but you deserved to know the truth. I’ll be here to guide you both… medically and emotionally.”

Ya miƙe, jiki ba ƙwari, amma yana jin wata irin kauna da rauni da su ka haɗu a zuciyarsa, Allah ya gani yana son ya'ya duddah ba auren soyayyah sukayi da ramlart ba ya so ace ta haifa masa yara, saidai kash wani gurbaceccen tunanin ta ya ja ta aikata aikin da zatayi nadama a karshe, cikin karfin hali Ya fice a hankali, zuciyarsa na neman amsoshi fiye da wan da likita ta bashi.
Ganin irin halin da Ogan nashi ya fito ne yasa ka PA take masa baya cikin hanzari, ganin yanda yake tafiya a gaggau ce ganin ya nufi hanyar fita daga Ward din ne yasa, tun kafin isowar su PA ya sanar da bodyguard din da su kasance cikin shiri, hakan ce kuwa tafaru suna fita aka bude masa mota ya shiga, jin ya zauna a kan sit din motar ne ya sa ya lumshe kyawawan idanun shi , a hankali yake sauke ajiyan zuciya, sunan Allah kawai ya ke iya ambata a kasan zuciyar sa, jin motocin sun fara tafiya ne ya sa ya d'an gyara zaman sa, Wani irin matsanan cin ciwon kai yake ji, ga gajiyar tafiya da ya kwaso, abun duk ya hade masa .

A bangaren ramlart kuwa tun tana saka ran dawowan mijin nata har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido.
Zuwa yanzu Zuciyar ta tashiga tashin hankali da firgici wanda ita kanta ba ta san adadin shi ba, ganin bini bini tana kallon bakin kofa ne yasa aunty hauwa tace "lafiyan ki kuwa ramlart" ganin kar anty hauwa ta rafko jirgin ta ne yasa tace "lafiya qlu anty" daga haka bata sake ce mata komai ba , sai ma zame wa da tayi ta kwanta a bisa gadon jinyar tata tare da lumshe idanun ta kamar mai bacci.

💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫

✍️Mrs Alkali

Page 2️⃣

Yayin da motoci suka shigo babban katafaren gidan AA Turaki a Maitama Abuja, wata ƙofar ƙarfe mai ƙyalli ta buɗe da kanta ta hanyar automatic.
Wani irin babban mansion ne, na zamani amma an kawata shi da hadin kayan gargajiya da na zamani, hakan sai yasa ya zama na musamman zaka jima baka ga mansion irin sa ba .
Gininsa gwanin ban sha’awa ne, wanda ya sha gyare-gyare daga lokacin da ya gina shi , kasan cewar bai manta asalin sa bane yasa ya zaɓi kawata gidan nasa da Kayan gargajiya game da na zamani.

Akwai fitulun wuta masu ba da sanyi da wani haske na Musamman ,a gefen titin cikin gidan, ga wasu flowers da tsire-tsire masu fidda ƙamshi na Musamman ,.
Motar sa limosine da ya ke ciki ne ta tsaya a gaban babban foyer, bodyguards dinsa, guda biyu suka buɗe masa ƙofa, yayin da ya bar sauran bodyguard din sa a chan parking space dake haraban gidan.

A hankali ya fito, fuskarsa cike da natsuwa amma idanuwansa na bayyanar da damuwa, Tattare da gajiya da ɗan ɓacin rai, yana sanye da suits mai tsada, amma haryanzu babu walwala akan fiskar sa, fuska tana ɗaure tamau kamar wan da bai taba dariya ba, a hankali ya ja wani irin numfashi mai sanyi, cikin nitsuwa ya fara takawa cikin main parlourn gidan ya nufa, da sallama d'auke a bakin sa ya shiga cikin parlourn sai dai kamar ko yaushe idan yayi sallamar bai zama lallai mutum ya ji sa ba.

Wata mace ce mai kusan shekaru 60, kyakkyawar, gaske doguwa, mai launin fata fara sol, irin mai sanyi da kyan ido irin na Fulani usuli.
Sanye take da atamfa mai Holland da gyale wan da ta lulluɓe saman kanta da shi, kana ganin ta kaga jin dadi a tare da ita.
Tana zaune a kan farfajiyar da ke kusa da living room, kallo d'aya zaka mata kasan cewa akoi wani abu mai muhimmanci da take jira.
Ganin wanda ya shigo ne ya sa ta fad'a'da murmushin ta.

"Yeroh !"Ta ce da murmushi mai sanyi akan fuskar ta, a lokaci guda kuma ta tashi tsaye tana mai cewa, "Lale marhaban da dawowa daga London."

Cike da d'an sassarfa Ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta ya na mai riƙe hannunta, a lokaci guda , ya sunkuyar da kansa kasa.
Ganin irin halin da tagan sa a ciki ne ya sa ta kara zuba masa ido, kallon sa tayi na Yan mintuna, Tuni ta fahimci baya cikin walwala, duddah hakan ba wani sabon abuba ne a gare ta amma sai take ganin kamar na yau din ya sha banban dana sauran lokutan.

Cike da na tsuwa tace
"Alhaji ya ce mini ka biya ta a sibiti , to Yaya jikin ramlatun, ? Yanzu ace muna gida d'aya ramlatu ta kasa fad'a mana cewa bata da lafiya, sai dai kawai Muji cewa tana asibiti."

Dago kansa yayi daya ke jin ya bala'in yimasa nauyi, kallon mahaifiyarsa,ya yi a hankali ya ɗan sauke numfashi.

"Mun same ku lpy? Shine abun da yafara fad'a , kafin ya sake cewa jikin ta da sauƙi, amma..." Sai kuma d'an tsaya, yana juyar da kan sa gefe guda, yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika idanunsa, baya son Hajja ta gansa a irin wannan yanayin .

A hankali Hajja tace:

"Yeroh ..!Na san murmushinka haka zalika nasan kukan ka, sabi da haka" ko fe'ihh" Me ya faru?" Ta karasa maganar cikin harshen fulatanci.

muryarsa a rauna ne, yana jin zuciyarsa kamar an tsinke ta, kamar zata faso ƙirjin sa ta fito waje.

"Abu ne mai nauyi, Hajja Wani abu ya faru da bazan iya furta shi cikin sauƙi ba..."

A dai dai lokacin ne Alhaji Abdullahi Turaki, mahaifin sa, ya shigo daga sashen karatu, na cikin gidan.
Alhaji Turaki dattijo ne mai kusan 70yrs, dogo, ne fari, fuskar sa a cike da nutsuwa da dottaku, cikin nitsuwa Ya zauna yana kallon ɗansa d'aya tilo cike da kulawa.

" A duk in da namiji yake an san shi da gwagwarmaya da kuma jure ƙaddarah, don haka baka da wan da zaka fad'a wa matsalar ka bayan nida mahaifiyar ka, sabi da duk wani abu da ya same ka ba kai kaɗai, ya shafa ba har da mu" Alhaji Abdullahi ya kara sa maganar tasa cike da hikima da son karantar yanayin d'an nasu.

Wani irin yawu ya haɗiye masu dacin gaske, kamar wanda akayi wa dole ya ce:

"Doctor tace... Ramlart na iya rasa damar sake haihuwa gaba ɗaya, Kuma... wannan ba shine karo na farko da ta yi amfani da abortion pills ba."

Wani irin shiru ce ta ratsa tsakiyar family lounge, din, Hajja ce ta saki ajiyar zuciya, a hankali ta koma dabaya ta zauna deb'es a kan lallausan sofa, hawaye na kokarin cika idonta, wani irin tausayin ɗanta da halin da suka tsinci kansu a ciki shekarun baya ya dawo mata sabo fill a zuciyar ta ji takeyi kamar ma yanzu ne abun yake faruwa da su.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..." Shine kawai abun da bakin ta ya iya furtawa.

Alhaji Abdullahi Turaki ne ya girgiza kai, fiskar sa dauke da tausayi yace

"Zamuyi magana da ita, in ta samu lafiya Amma ina son kai ka kwantar da hankalinka, Aliyu Allah yana jarabtar bayinsa masu imani."

A hankali ya miƙe yana kallon su, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da ƙunci amma yana samun sauƙi da d'an sassauci da ganin irin kulawarsu, a gare shi.

“ cikin sarkewar murya yace Zan shiga ɗaki inyi sallah, ina so in huta .” daga haka bai sake cewa komai ba ya juya cike da sassarfa yana jin kamar gangan jikin nasa zata gaza daukar sa.

A haka Ya nufi ɗakin sa mai kama da suite dake bisa babban bene na gidan wanda a cikin sa ya ke tattare da komai na more rayuwar duniya, office, library, da bedroom mai kyau kamar na hotel, kitchen da toilet.

Zuciyarsa cike ta ke da damuwa… amma a ƙarƙashin zuciyar sa, akwai wani sabon damuwa da yake ji tunani yake akan maganar da Dr. Farida ta fad'a masa.

Bayan ya shige ciki, parlourn ya rage saura Hajja da Alhaji , shiru mai nauyi ne ya wanzu a cikin babban falon gidan.
Kowa na cikin tunani, kowa da abun da zuciyar sa take saka masa.
fuskar Hajja ta fara baiyana fargaba da shakku, a hankali Ta ɗago idonta, ta kalli mijinta da yanayin da ya jima rabon da yagan ta a cikin sa a tare da ita , cike da fargaba da jin tsoro tace

"Alhaji… Ina jin tsoro. Tsoron gaskiya. Kar dai ace… kar dai ace wannan kaddarar da muke gujewa shekaru fiye da ashirin ne ke neman biyo mu."

Cike da mamaki Alhaji yake kallonta cikin tashin hankali yace:
"Kaddara kuma? Habiba me kike nufi?"

Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, mai nauyi:
"Shekaru ashirin da ɗaya kenan da muke kok'arin ɓoye sirrin nan, Ka manta da abinda muka tafka? Wane hukunci muka tsallake mu ka gudu sabi da kunyar duniya? Yau ga ɗanmu , shekara biyar kenan da auren sa da Ramlartu… amma babu ɗa, babu diya, Yanzu kuma ga wata magana wai maganin zubar da ciki take sha ? Astaghfirullah! Wannan ai ba al’ada bace mai kyau."

A hankali ta girgiza kai , idanun ta cike da hawaye tace
Chapter 3 · 0% Book details