Sashe 1
Kauna Da Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫
(Love and Destiny)
Na
UMMUH EYSHAL
Mrs. Alkali
بسم الله الرحمن الرحيم
*Da sunan Allah me rahma me jin kae,Godiya ta tabbata ga ubangijin talikae wanda yabani damar fara rubutamuku wannan littafin,Amincin da taslimi sukara tabbata ga annabin mu annabin rahma annabi muhamammad salallahu alaehi wasallam*
*Sadaukarwa*
Na sadaukar da wannan littafi ga maigidana, masoyi na, ginshikin farin cikina kuma uban Ya'ya na.
Nagode da ƙauna, fahimta, da goyon bayan da ka ke bani a kowane mataki na rayuwa.
Haka kuma ga yayana kuma ɗan uwana na jini, *Bashir Ahmad Musa*, wanda kalmominsa suka zame mini garkuwa a lokacin da zuciyata ke da rauni.
Ku biyun kun taka rawa ta musamman a rayuwata — wannan rubutu sadaukarwa ce gare ku, alkhairin Allah ya kaimuku a duk in da kuke.
*Gabatarwa*
Rayuwa wani tafarki ne mai cike da sirrika da sauye-sauye da ba kowa ke iya hango su ba. Akwai lokutan da burin zuciya ke bijirewa kaddara, sai dai a ƙarshe, abinda Allah ya rubuta shi ne zai tabbata.
Littafin *Ƙauna da Kaddarah* ya ƙunshi labarin wata mace da ta fuskanci ƙalubale daga kuruciya zuwa girma, cikin soyayya da ciwon zuciya, tsanani da juriyar rayuwa. Kaddara ta raba ta da farin ciki, amma soyayya ta nemi hanyarta ta dawo da shi.
Wannan littafi ba wai labarin soyayya bane kawai, har ila yau yana ɗauke da darussa na rayuwa, hakuri, yanke shawara, da ƙarfin zuciyar mace da namiji a lokacin da jarrabawa ta same su.
Ina fatan wannan littafi zai tabo zuciyar ki/ ka, ya baka nishadi, da kuma zurfin tunani game da yadda kaddara ke tafiyar da rayuwar mutum.
GARGADI
*Labarin littafin ƘAUNA DA KADDARAH ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.*
Wannan littafin mallaki na ne Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗
Page 1️⃣
*"National Hospital Abuja, Garki – Area 11, Central Area, Abuja."*
Misalin qarfe 12:30am na rana, sautin karar motoci masu sirri ne ya karade harabar asibitin National Hospital Abuja.
Wata mota kirar SUV ce mai gilashi mai duhu ta shigo cikin nutsuwa, tana jagorantar tawagar, motocin ,Bayanta kuma motar limousine baƙa, ce ta biyo, tana tafe cikin natsuwa kamar ba tafiya take ba. A karshe, wasu motoci biyu na tsaro (escort vehicles)suka rufo musu baya, kowacce dauke da ma’aikatan tsaro masu rigar fata da tabarau masu duhu sanye akan fiskar su.
Ma’aikatan asibitin da marasa lafiya da ke kai kawo a harabar asibitin ne, su ka tsaya suna kallon tawagar motocin ,ba tare da sanin wanene ya iso ba. A lokacin ne wani daga cikin masu tsaron ya fita daga motar gaba, ya duba gefen kofar motar limousine, d'in sannan ya bude cikin ladabi da nitsuwa.
Da sauri wani matashi da akallah zai kai shekaru 37yrs ya fito ya tsaya a bakin mota limousine d'in da alama yana jiran fitowan uban gidan nasa ne.
Shiru wajen yayi na wasu mintuna a kallah ya kusa 5 minutes .
Kafafunsa ya zuro a hankali sanye suke cikin takalma masu sheƙi baƙaƙen designer cover shoes na Louis Vuitton.
a hankali ya fito daga cikin motar, kai kace shugaban ƙasa ne.
Dogon mutum ne mai surar jarumta, fuskarsa cike da nutsuwa da kamala, yana da dan kauri kad'an amma ba sosai ba, fari ne irin sosai din nan, don har yellow -yellow fatar sa tayi, kana ganin sa kaga farin bafulatanin usuli, kamar zaka taba fatar sa jini ya fita sabi da hasken sa .
Sanye yake da bak'in suit na alfarma – custom-tailored Italian design wanda ya zauna a jikinsa luf-luf tamkar an zana shi ne sabi da shi. Shirt dinsa fara ce mai sheƙi, da silin tie mai launin royal blue.
Hannunsa ɗaya na daure da wristwatch mai tsada (Rolex), ɗayan kuma yana riƙe da jakar laptop ta fata da sauri PA ya karbi jakan laptop din nasa tare da dan rusuna masa, alamar girmamawa.
Fuskar sa a had'e take ba ta da alamar murmushi amma akwai nutsuwa mai cike da kamala da daraja, akanta.
idanuwansa kuwa sun nuna gajiya alamar yafito daga doguwar tafiya , Duk da hakan, in ka kalle shi baza ka iya gane hakan kai tseye ba sa bida korjinin sa da girma da izza.
Cikin nitsuwa da kasai ta ya fara takunsa na ingarman namiji maiji da lafiya.
P.A din sa ne ya take masa baya ,sauran bodyguard din kuma anan aka barsu a kame kamar wasu marassa rai.
Kamshin turarensa ya cika iskar da ke zagaya harabar asibitin.
İn ka kalli yadda ya ke tafiya cikin nitsuwa da kasaita, zaka dauka ba shi da wata damuwa a tattare da shi.
Haka jama'ar dake wajen sai matsawa sukeyi wasu na kus kus din sa, Wannan shi ake kira banza a banza dan kuwa bai san ma da zaman su ba bare yasan sunayi, haka yaci gaba da sa kai cikin asibitin Sani P.A na biye da shi abaya, duk in da ya wuce sai ya barmusu tsarabar kamshin turaren sa mai sanyaya rai.
Obstetrics & Gynaecology Department naga an rubutu a saman department din da ya shiga, da alama asibitin ba bakon sa bane
Duk da takunsa mai nauyi da izza, akwai gajiya da damuwa a fuskarsa, amma ba kowa ne zai fahimci hakan ba, Likitoci da nurses ne suka shiga matsawa gefe, suna ba da hanya cikin girmamawa suna miko gaisuwar su ,hannun sa kawai yake daga musu alamar yana amsa gaisuwar da suke masa.
Da sauri wata Nurse ta shiga gaban su , da alama sun san da zuwan sa, da Sani PA su ka gaisa , haka tayi gaba domin yimusu jagora , shi ko uban gayyan ko a jikin sa bai nuna ma alamar ya san da wanzuwar wata halitta atare da su ba, dama chan tafiyan kurame ake yi a tsakanin sa da Sani PA.
Wani dan corridor ta bi da su a saman shi an rubuta VIP Ward , basuyi wani tafiya mai nisa ba , a kofar wani d'aki ta tsaya , asaman d'akin an rubuta Ward B3 Room 2, cike da yauki ta juyo ta kalli Sani PA tace "This is the room Sir".
Sani PA ne yace "thank you nurse"
Cike da salo na jan hankali tace "ur wlcm sir"
Ganin bai sake ce mata komai bane yasa Nurse d'in juyawa a sukwane.
D'an matsawa baya kad'an PA yayi ya Dan kame alamar girmamawa.
A hankali cike da nitsuwa, kamar wanda akayiwa dole ya saka farin hannun sa ya Murda handle d'in kofar d'akin a hankali ya saka kan sa cikin d'akin bakin sa d'auke da sallama kasa kasa kamar wanda baya son yin maganar.
Dakin ya kasance mai kyau da tsafta sosai, an kafe shi da lafiyayyun gadon asibiti na zamani, masu ikon daidaita kwanciya da tashi bisa jin daɗin mara lafiya.
Bangon dakin an shafe su da light cream colour, yana ba da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga me kallon sa, A gefe guda kuma, akwai window mai feshin gilashi, wacce ke barin hasken rana ya dinga shigowa a hankali.
An tanadar da split AC, refrigerator, plasma TV, da kuma kujera mai laushi domin mai jinya da wanda ke kula da ita. A gefen gadonta kuma, akwai small digital monitor wanda ke duba motsin jini da numfashi lokaci-lokaci.
Wata mata ce Jikinta na kwance a gadon asibitin, sanye take da riga mai launin fari da alama rigar marassa lafiya ce ta asibitin, fuskar ta kumbure kaɗan, ta rame tayi fayau da ita. Idonta a rufe suke ruf, amma numfashinta na tafiya daidai — alamar cewa jikinta na ƙoƙarin murmurewa, zata iya farkawa ako da yaushe.
Anty hauwa ce zaune a gefen gadon, tana riƙe da hannunta, tana shafa fuskarta lokaci-lokaci, tana karanta addu’o’i tana tofa mata, Tunanin irin azabar da yâr uwar ta ta sha yana bayyana a saman fuskarta, amma a lokaci guda, zuciyarta cike da godiya ga Allah cewa ta tsira da rainta.
A hankali a ka bud'e kofa , cikin nitsuwa ya shigo, bakin sa d'auke da sallama kasa kasa, Sanye yake da black designer suit, fuskarsa cike da damuwa da gajiya, golding eyes din sa ya zuba mata , Kallon farko da ya yi mata ya ya fahimci cewa bakaramar wahala ta sha ba , ramlart ce yanzu kwance ba hayaniya, ba tsiwa, kamar mai bacci, amma kuma ba barci ba ne mai nutsuwa dagani kasan barcin wahala ne.
A hankali Ya matso kusa, ya tsaya, yana kallon ta daga sama har ƙasa. Kamshin turarensa mai tsada ne ya cika ɗakin gaba d'aya.
Anty hauwa ta miƙe a hankali, ta d'an basar gaishe sa ta shiga yi, ba yabo ba fallasa haka ya amsa mata, babu wata sakewa a tsakanin su, ganin hakane yasa aunty hauwa ta nufi hanyar fita daga d'akin domin bashi waje ya gana da matar sa, cikin nitsuwa Ya zauna a gefen gadon, ya kama tafin hannunta a hankali, yana shafa shi cikin tausayin ta dana kan sa. Ya lumshe idonsa, ya dafe kansa kaɗan, cikin zuciyar sa yake furta, "
“Ya Allah, kai ne Mai kowa da komai... na yarda da ƙaddararKa. Na amince da rabonKa. Amma Ya Allah, sai yaushe? Sai yaushe zan riƙe ɗana a hannuna, in ji kamshin jikinsa, in kalle shi ya kirani ‘abba’? Kullum ina karanta ‘Laqad khalaqnal insana fi ahsani taqwim’... amma me yasa ni kake jarabta na da wannan jinkirin?, ya Allah idan hakan yana da nasaba da kaddarah n da ta fad'amini a shekarun baya , Allah na tuba ya Allah ka yafe mini kurakurai na"
Ya runtse idonsa da karfi, yana jin wani irin turirin zafi na fita daga kasan Zuciyar sa, a hankali ya shaki iska mai sanyi, yana jin nauyin hawaye a cikin zuciyarsa amma bai bari suka sauko ba. Zuciyarsa ta ci gaba da kuka cikin tawakkali da nadama, batare da ya bar hakan ya baiyana a saman fiskar sa ba.