← Book details Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi dai dreba sai mamaki yake yi amma haka nan ya dawo cikin banki ya sami inuwa yayi parking. Nan fa daga mai kiran fitsari sai mai jin yunwa ko bacci. Haris da ya fisu hankali korafin rashin zuwa islamiyya yake yi. A haka suka yi ta zama har bacci ya kwashesu.
*****

A makarantarsu Rumana kuwa da break sai ga Yusra tazo ta bata naira dari kamar yadda Ummanta tace su raba. Da kyar ta karba duk da cewa yunwa take ji. Yusra tayi mata tayin abinci taki karba shima. A ganinta basu yi sabon da zata ci mata abinci ba bayan ita bata zo da nata ba. Karfe hudu da rabi suka fito ta nufi titi za ta tsallaka. Yusra ta dakatar da ita

"Rumana ki jira Umma tazo. Yanzu za ta biyo idan ta ajiye kannena a islamiyya"

"Idan na tsaya za'a yi min fada a gida."

Daga haka suka yi sallama ta tsallaka daya gefen ta kama hanyar gida. Tafiya ta rinka yi tana jan kafa saboda tsabar yunwa. Yau da azumi take yi ba karamar wahala zai bata ba. Daren jiya tun takwas da rabi tayi bacci ko abincin dare bata ci ba. Gashi yau bata samu ko ruwa ta sha ba.

Da sallama ta tura kofar falon sai dai babu alamar akwai mutane a gidan. Dakin Maamu ta wuce. Tana taba kofar dakin Maamu tayi saurin tura langar faten karkashin gadonta. Tsoronta kada Rumana ta gani har wani yaji ayi tunanin Awaisu ko matarsa basa sonta ne. Zata yi bakin kokarinta wurin kare mutumcinsu a idon duniya.

Takalmi kawai Rumana ta iya cirewa ta fada kan gado tana rike ciki.
"Maamu yau naji yunwa sosai har jiri ya rinka daukana a hanya"

Tasowa Maamu tayi ta dawo kusa da ita ta zauna tana dora hannu a kan Rumana
"Baki da lafiya ne kika ki cin abinci?"

Bata boye mata komai game da yadda sukayi da Gimbi ba da safe. Hatta kudin da Umman Yusra ta bata sai da ta nuna mata domin ko kwandala bata kashe ba. Hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba da kuma neman tabbatar mata da zargin da take gudun dorawa iyalin Awaisu.

"Tashi ki je ki hada shayi ki sha kafin su dawo. Doya aka dafa ke kuma nasan ba kya ci"

Rumana ta yamutsa fuska saboda yadda ta tsani doya. Falo ta koma sai dai babu kayan tea a tsakiyar dinning table kamar yadda ta saba gani tun farkon zuwanta. Ta shiga kitchen nan ma babu wani abin kirki sai ta tafi zata dauko indomie a store. Nan fa taji kofar a rufe. Tunani ne ya isheta game da sauyin da ta gani a gidan yau. Haka ta koma wurin Maamu ta fada mata.

Hankalinta ya sake tashi sosai. Duk da tana jin yunwa itama amma tausayin Rumana ne ya kamata. A ranta tana adduar Allah Yasa ba wani sabon salon zama zasu koma yi da Gimbi ba. Da wane ido zata kalli su Baaba Hure.

"Dauko wayata ki duba nambar Gimbi ki kira"

Rumana ta aiwatar da abin da aka sata. Tana zaune Maamu tana fada mata abin da zata ce a wayar.
*****

Zaune take tana cike wasu takardu taji waya. Tana dubawa ta gane numbar Maamu ce. Tsorata tayi ta kasa dauka sai a karo na biyar ta dake zuciyarta. Muryar Rumana taji ta gaisheta sannan tace

"Maamu ce tace na kira wai yau lafiya kuwa. Ko wani abin ya faru?"

"Kice mata babu komai nima na kusa tasowa"

"Su Haris basu dawo ba har yanzu sannan ni da Maamu bamu sami abinci ba. Shine tace ko zaki fadi inda key din store yake"

Maamu daga gefe tana 'yar dariya tace "yau zanyi musu girkinmu don dadi duk wanda yaci sai ya manta hula da takalmi"

Itama Rumana duk da yunwar da take ji jiki babu karfi dariyar tayi tana fassarawa Gimbi abin da Maamu ta fada.

Shiru tayi ta kasa bata amsa daga baya ta fara cewa "hello, Rumana bana jinki."

Daga haka ta kashe wayar ta cigaba da harhada kayanta a jaka. Tunaninta daya kada aikin ya baci ta sami matsala da Awaisu. Ta san yadda yake son Maamu da su Baaba. Tsoro ne sosai ya kama ta.

Lokacin da ta fito shida saura ta fake da cewa dreban ya sha fama da rigimar yara ta sallame shi. Duk sun bata motar da abincin da ta bayar da kudi aka siyo musu a wani gidan abinci mai tsada na kusa da bankin.

Gidan Anti Bebi ta wuce ta bar yaran a mota da gargadin kada wanda ya fito. Tare da maigidanta ta sameta ta gaisheshi yana ta bin ta da ido har suka shige daki ita da Anti Bebin.

"Me ya faru na ganki da yamman nan ko waya babu?"

Muryarta har rawa take yi tace "tsoro nake ji kada Awaisu ya sakeni wallahi. Yau baki ga abincin da na bar musu ba. Ina tsamani bata ci ba"

Yadda tayi a gidan tun safe zuwa wayarsu da Rumana ta sanar da Anti Bebi.

"Mtswww, ni kin bani haushi ma. Matsoraci baya zama gwani Gimbiya. Idan baki shafawa idonki toka ba a yadda nake ganin take takenta tunda har ta fara tambayar mukullin store saura tasa yayi miki kishiya ko ta rabaku gabadaya"

Gimbi ta kara shiga tashin hankali "wallahi bazata yiwu ba. Awaisu da taimakon Alhajinmu ya zama mutum. Duk wannan aikin da nake yi da wahalar da nake sha dominsa ne. Babu wadda ta isa tazo mu zauna taci arzikin da bata san samuwarsa ba"

Anti Bebi tayi dariya "yanzu kike magana, to kada ki damu idan kinje gida ta fadawa Awaisu kinga alamun zaiyi fada. Meye amfanin Laminde? Kafin ya fara fadan kiyi kanta da duka idan ya kama kina kuka kina cewa tana son kashe miki aure zata wulakanta miki uwarmiji. Daga nan ki dauki laifin duka ki nana mata ki sabule kanki ki koreta. Idan kin tashi neman wata mai aikim kizo zan hadaki da mai kawosu daga kauye"

Sai yanzu Gimbi ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Harda murmushinta ta fita suka koma gida.
*****

Maamu ta kai wuya wurin bacin rai jira take yi su dawo. Bazata bari wannan abin yayi nisa ba gara Awaisu ya taka burki idan ma bisa kuskure ne a tunaninta ya kamata da wayar ta katse lokacin da suke magana da Rumana ta sake kira. Shirun da suka ji har Rumana ta sake kira wayar a kashe shine ya bata mata rai.

Gimbi na shiga gida ta tarar da Awaisu shima shigarsa kenan. Yana son tambayarta inda ta tsaya kuma ga yara da kayansu tun na boko ya ga Maamu ta fito. Kana ganinta yau babu wannan fara'ar wadda da wuya ka ga fuskarta a hade. Jikinta gabadaya babu kwari saboda yini da yunwa. Ruwa kawai suke sha ita da Rumana.

"Yanzu nake shirin shigowa dakin naki" cewar Awaisu yana matsawa kusa da ita.

"Na hutar da kai. Dama nace ko kun manta damu a gidan ne yau baku ajiye mana abinci ba"

Dayake da yarensu take magana Gimbi duk ta tsargu.

Kallon Gimbi yayi "garin yaya kika fita ba'a ajiyewa Maamu abinci ba? Ina Laminde?"

Hantar cikin Gimbi ta kada ta fara in'inar da bata san tana da ita ba "uhmm-dama-da-fate-eh faten doya aka yi mata kafin-kafin mu fita"

Maamu sarai ta fahimceta sai kawai ta koma dakin ta dauko langar faten doya. A harzuke take sosai ta bude a gaban Awaisu, har wani ruwa ruwa ta fara ga baki da tayi sosai
"Wannan abincin zamu ci Awaisu?"

Yadda tayi maganar muryarta ta karaya domin kuka ne yake barazanar kwace mata saboda takaici. Ko aiki take yi a gidan aka bata wannan abincin tabbas anso cin mutumcinta ne.

Dagowa yayi da zafinsa zaiyiwa Gimbi fada. A lokacin ba karamin tsoro ne fal a zuciyarta ba sai ta tuna hudubar Anti Bebi ta daure fuska. Kamar anyi ruwa an dauke haka ya hadiye fushinsa ya koma yana kallon Maamu.

"Ai kuwa da gani faten nan zaiyi dadi. Gimbi ko zaki dumama mata a microwave yadda zata ji dadin ci"

Duk da tayi mamakin saurin sauyawarsa amma saboda tana son tabbatar da aikin Wangesi tace "to my dear, dan tambayar min idan tana son manshanu sai na saka mata ma. Kasan Laminde gwanar girki ce"

Haka kuwa ya tambayi Maamu hankali kwance. Kasa bashi amsa tayi saboda a take a lokacin wani irin abu taji ya soki zuciyarta. Tana kallo Gimbi ta wuce kitchen da langar wai zata dumama ta dawo mata dashi. Awaisu kuwa yana murmushi yace mata zaije ya watsa ruwa yazo suyi hira.

Bayan tafiyarsa Maamu ji tayi jiri zai kwasheta ba don yunwa ba sai don yadda zuciyarta ta karaya da halin da ta tsinci kanta daga zuwa gidan tilon danta abin alfaharinta.11*KASHE FITILA*💡12

*Batul Mamman*💖

Da kyar Maamu ta kai kanta daki inda Rumana take kwance duk sauran kuzarinta ya kare. Tana turo kofar Laminde wadda babu wanda ya lura tana tsaye a bakin kofar shigowa gidan ta dafe kirji. Duk abin da akayi a kan idonta ne. Wannan abu ya kara daure mata kai har ta rasa da me za ta kwatanta shi. Ko ma menene akwai wani abu da uwar dakinta take yi game da surukarta.

Tun safe da suka fita Gimbi ta aiketa kasuwa. Daga can ta ce ta wuce wurin kanwarta da aka kawosu aiki Abuja tare. Haka ta tafi cike da mamaki musamman da ta fada mata kada ta koma sai ta kirata a waya. Wayar da ba'ayi mata ba sai da ta baro gidan Anti Bebi.

Gimbi ta gani ta dawo da langa tana tiriri ta dorata akan wani tray na silver kasanta kuwa duk yayi baki.

"Yaushe kika dawo ban sani ba?"

"Shigowata kenan"

"To aje ayi min wanke wanke"

Laminde tace to ta juya kitchen.
*****
Chapter 8 · 0% Book details