Sashe 1
Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
© Fikra Writers Association
*KASHE FITILA*💡1
*Batul Mamman*💖
*FWA Girls Secondary School Abuja*
_SS 2A_
Hankalin malamin Civic Education da kusan duka daliban yana kan monita wadda aka sanya rarraba takardun test da akayi satin da ya wuce. Wannan ya bawa 'yan mata biyu cikin daliban da suke zaune a layin farko daga tsakiya damar karasa shirin abin da suke kullawa tun safe.
Daya daga cikinsu ce ta rike ciki tare da kwalla kara iya karfinta sannan ta sulale a kasa ta kwanta. Kafin malamin da sauran su ankara dayar ta durkusa a gabanta tana jijjigata a hankali da muryar kuka take cewa "Rumana me ya sameki, tashi don Allah, wayyo...."
Murmushi ne yaso kwacewa Rumana ai kuwa taji kyakkyawan mintsini daga wurin Yusra kawarta "don ubanki idan kika tona mana asiri wallahi cewa zanyi ba dani akayi ba"
Tsabar tsoro ne yasa Yusra yin zagin. A lokacin malamin har ya iso, sauran 'yan aji duk an zagaye su ana tambayar me ya faru. Yusra harda kukanta tace haka kawai ta ga Rumanan ta fadi.
Health prefect aka kirawo daga ajinsu tare da taimakon Yusra da wata malama suka kai Rumana karamin asibitin cikin makarantar. Sannan aka nemi numbar makusancinta wanda ya kasance kawunta aka kira shi.
Bayan an saka mata allura ana yi mata karin ruwa ne kowa ya fita sai likita da Yusra. Suna jin shiru Rumana ta bude idanu tare da saukowa daga kan gadon ta durkusa a gaban likitan "doctor ka taimakeni idan Uncle dina yazo ka fada masa ulcer ta kusa cinye hanjina"
Duk da ya dauki maganar rainin wayo amma bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Sai kuma yayi saurin daure fuska.
"Nayi miki kama da abokin wasanki ne ko me?"
Yusra ma durkusawar tayi "idan baka taimaketa ba wallahi yunwa zata kasheta a gidansu. Ulcer din gaske ce zata kamata"
Juyawa yayi zai fita Rumana wadda ta tabbatar idan hakkansu bai cimma ruwa ba yau kila banda yunwa jikinta sai ya gayamata a gida bata san lokacin da ta fizge hannu daga jikin allurar ta ruga ta tare kofar ba "idan baka taimaka min ba wallahi zanyi muku hauka a asibitin nan. Ka fada masa mugun ciwo ya kamani a kaini gidanmu kada na mutu a nan"
Saroro yayi yana kallonta. Bai ankara ba ya ga ta nufi gadon dakin ta daga shi da yake ba wani nauyi ne dashi ba ta kifar. Dan tebur din kusa da gadon ma hantsila shi tayi tana ihu da kuka. Yusra wadda tare sukayi shirin ciwon karyar ma sai da ta tsorata ganin da gaske Rumana tana neman yin hauka.
Suna haka likitan yana kokarin riketa taji muryar kawunta daga dan karamin reception din yana tambayar inda take. Idanunta cike da hawaye ta sake kallon likitan alamun roko da neman agaji.
Tausayi ta bashi, ita kuwa Yusra kuka take yi.
Awaisu yana shigowa dakin ya ganta biji-biji kamar anyi wasan kura da ita. Ga hawaye ya wanke mata fuska. Da saurinsa ya karasa inda take ya rikota "Rumana me ya same ki? dena kukan ki fada min abin da kike so"
Kasa magana tayi sai kukan da ta cigaba da yi. Ba a son ranta tayi wannan abin ba amma idan ba gaban iyayenta ta koma ba bata jin zata iya cigaba da hakurin zaman gidansa.
Hankali a tashe ya dubi likitan "me ya sameta?"
Hadiyar yawu yayi yana kallon yadda 'yan matan suka tsare shi da idanu "uhmm a binciken da nayi yarinyar nan tana fama da ulcer sosai har tana neman lahanta mata hanji" mamakin kansa yayi da biye musu harda aron kalamansu.
Girgiza kai yake yi alamun rashin yarda "Ulcer, ulcer ciwon yunwa? Mtsew, ba dai a gidana ba wallahi."
"Abin da bincike ya nuna kenan ranka ya dade" Tuni likita ya fara tsorata kada a daga maganar gaba.
Harzuka yayi "kasan ko ni waye zaka kira min ciwon yunwa? To ko maigadin gidana bazai kira yunwa ba balle 'yata"
Gaban likita ya fadi a zuciyarsa yace 'yarsa kuma, wace 'ya ce zata yiwa iyayenta sharri irin wannan. Harara ya jefa musu duk da ba kallonsa suke yi ba.
Awaisu ya katse masa tunani " kaga ka sallameta zan kaita babban asibiti."
Bai jira amsarsa ba ya ya durkusa ya dauko takalmanta ya saka mata sannan ya kamata suka fita. Wani irin tausayinsa ya kamata. Sai dai ko ana muzuru ana shaho da yardar Allah sai ta koma garinsu.
Suna shiga mota taji ya umarci dreba da ya kaisu asibitin kudi da iyalan gidansa suke zuwa. To kada karyarta ta kare kawai sai ta sandare masa tana mimmikewa. Hankalinsa ya kara tashi. "Uncle babu inda zani, ka mayar dani gida na mutu gaban Mama. Kada na mutu ban sake ganinsu ba"
A take ta karyar masa da zuciya. Asibitin dai yasa suka karasa sai dai a binciken gaskiya an tabbatar masa da gaske bata da kuzari. Tana bukatar hutu da abinci mai gina jiki.
Wannan jawabi ya sanya shi cikin rudani. Duk yadda yaso su kwantar da ita fafur taki yarda ita Mama kawai take son gani.
Gida suka koma yayi ta fadan yaya akayi bata cin abinci ba'a sanar dashi ba. Maamu mahaifiyarsa ita tayi jinyar Rumana a ranar. Da gaske ta rinka sambatu tana kiran babarta ko runtsawa basuyi ba. Dole washegari yayi shiri shi da dreba zai mayar da Rumana gida. Sai dai yana tunanin me zai fadawa dan uwansa a matsayin dalilin da yasa ya dawo da ita.
Suna fita Maamu ta leko ta tagar dakinta tana kallonsu. Hawaye taji ya taho mata mai zafi tana tunanin yadda karamar yarinya ta samarwa kanta mafita. Ita kuma ta yaya zata ta bar gidan dan da ta haifa a cikinta?*KASHE FITILA*💡2
*Batul Mamman*💖
*Fika LG-Yobe State*
Yara ne suke ta tsalle-tsalle a tsakar gida saboda yau alhamis babu makarantar Islamiyya. Masu dan girman kuma musamman matan kowacce ta kama aikin gida tana yi.
Sallamar da suka ji ce tasa suka tashi babu babba babu yaro suka tafi tarbo mai yinta. Murnar ganin Kawunsu suke yi sai dai ganinsa rike da Rumana tana tangadin karya yasa suka yi cirko cirko. Sarkin surutun gidan ne ya ruga ciki yana sanarwa ga Rumana ta dawo.
Mahaifiyarta wadda ta kasance mata ta biyu cikin matan gidan bata san lokacin da ta janyo hijabi ta fito ba. Addu'a take yi Allah Yasa ba wani abin Rumanan tayi ba Kawunta ya kasa zama da ita.
Ko da ta fito sauran matan gidan wato uwargidan da amaryar duk sun fito suna musu maraba. Ganin yanayin Rumana yasa suka san babu lafiya. Maman Antu kamar yadda ake kiran uwargidan ita tayi saurin riko hannunta suka shiga babban dakin da yake mazaunin falo a gidan. Tuni Awaisu ya wadata musu shi da kayan kallo da kujeru masu kyau.
Bai bi bayansu ba ya wuce dakin Baaba Hure. A zaune ya sameta tana jiran shigowarsa tun bayan taji an ambaci sunansa da na Rumana. Sai da ya gaisheta cikin yarensu na Bolewan Fika sannan yayi mata bayanin dalilin zuwansu.
"Kuma ka tabbata ba aljanu bane da ita?"
"Ko daya Baaba, jiyan nan dai ta bani tsoro shiyasa nace bari na kawota ta huta kwana biyu. Makarantar tasu zanje sati mai zuwa duk da sun san bata da lafiya na sanar musu halin da ake ciki"
"To Allah Ya sauwake, ina 'yar uwata? Kwana biyu ko a waya idan nace yayanka ya kira ba ma samunta"
Dan murmushi yayi "tana nan lafiya, kinsan sai ta ajiye wayar ta manta inda take ma. Alhaji bai dawo bane?"
Kafin ta bashi amsa suka jiyo muryar Alhaji Harisu yayansa. Dakin ya karaso suka gaisa inda ya sake labarta musu dalilin zuwansu. Wannan karon harda matan gidan da Rumana a wurin.
"Zancen banza" cewar Alh Harisu
"Shine zaka biye mata ka baro aikinka ku taho"
Rumana ta tsuke baki, fatanta kada Alhaji ya bata shirin da suka kwashe sati uku suna yi ita da Yusra yace ta koma wannan kurkukun. Ita yanzu ko sunan Abuja ma bata son sake ji.
Shi dai Awaisu lallabata yace ayi kuma a tambayeta dalilin kin cin abinci. Domin ko mutan gidan suna ganinta sunyi korafin ramarta. Yarinyar da ko da tana makarantar kwana kafin komawarta Abuja da kibarta. Ita ko ramar nan ta kewar gida bata yi.
*****
Washegari da sassafe Awaisu da drebansa suka kama hanya.
Sai da Rumana taji tashin motarsu tayi wata kyakkyawar ajiyar zuciya. Za taci karenta babu babbaka, ta mike kafa taji dadin rayuwarta. Abinci kuwa tun daren jiya take yi masa cin hauka.
Bayan kwana biyu da dawowarta suna daki ita da babbar yayarsu da tazo daga gidanta. Hira suke yi Rumana tana bata labarin horon da akeyi musu a gidan Kawun nasu. Karshe ma tashi tayi tana kwatanta irin abin da tayi a clinic din makaranta. Mahaifinsu ne yazo ya tsaya yana sauraren bayaninta batare da ta sani ba. Ita kuma Maryama yayarta da ta ganshi ta kasa cewa tayi shiru sai kai da ta sunkuyar. Tana cikin nuna mata sandarewar da tayi a mota ta kula da Alhajin. Nan jiki ya fara rawa, kanta yayi yana duka ko ta ina.
"Har kinyi wayon yiwa dan uwana sharri Rumana?"
Ihu take yi tana kuka "Wallahi Baba ba karya nake ba. Ba'a bamu abinci sosai a gidan. Daga ni har Maamu bama koshi"
"Rufe min baki sakarai mara godiyar Allah. Sharrin naki harda Maamu a ciki? To zan kira Awaisun da kaina muyi magana"
A fusace ya fita ya shige dakinsa. Ko zama baiyi ba aka sanar dashi Baaba tana kiransa. Ya tashi ya fita.
"Ina gidan nan kake hukunci irin haka ko? duk kiran da nayi maka kuma baisa ka dena ba"
"Kiyi hakuri Baaba wallahi banji ba"
Abubuwan da Rumana ta fada ya maimaita mata. Gyada kai ta rinka yi har ya gama.
"Babu abin da ya dace kayi da ta fadi maganar nan sai bincike ba duka ba."
Cike da mamakin rashin gaskata zancenta yace "bincike kuma Baaba? Awaisu fa ake magana"
"Na sani, fada maka ne kawai banyi ba amma dan zaman da nayi kwanakin baya banji dadi ba. Kuma kasan Maamu da zurfin ciki"
Kallon mahaifiyarsa yayi yana mamakin maganganunta.