← Book details Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 15

Sashe 7

Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Bayan kwana hudu aka kirasu sune diba na biyu. Awaisu da drebansa sukayi mota biyu aka kaisu Airport. Basu dawo ba sai da jirginsu ya tashi.

Madina suka fara wucewa. Tun a hanya Gimbi ta soma zazzabi mai zafi da amai. Suna isa aibiti aka kaita likita yace taci wani abu ya bata mata ciki. Duk rashin kirkin da taso gwada musu sai ta koma abar tausayi suna jinyarta. Kwanakin Madina kaf bata ji dadinsu ba. Haka suka je Makkah can ma bata da wani kuzari. Wannan Hajjin dai bata ji dadinsa ba kwata kwata. Daga zazzabi ya warke sai mura mai zafi da ciwon wuya. Haka sukayi kwana talatin suka dawo da ita duk ta fige sai mugun nufi a zuciya.

*****
Sai da sukayi sati da dawowa sannan suka koma Fika aka bar Maamu da Rumana. Gimbi ce ta samar mata makaranta wadda bata da nisa sosai da gidansu. Makaranta ce mai tsada mai kyau don kawai ta burge Awaisu.

Da taga hankalinsa a kwance yake da abubuwan da take yi ta koma gidan Anti Bebi tana korafin rashin aikin maganin Wangesi.

"Kwantar da hankalinki naje na same shi. Yace wannan magani ranar da suka je gidan wani abu ya bata sihirin da yake ciki." Wata leda ta dauko ta mikawa Gimbi.

"Ga wannan yace ki dafawa mijinki abinci dashi. Daga ranar a hankali duk wani so da kulawa da yake yiwa uwar tasa zai fara fita daga zuciyarsa. Sai kiyi amfani da wannan damar ki gasa mata aya a hannu. Da kanta zata kwashi kafarta ta gudu gashi an daure bakin"

Karba tayi jindadi ya bayyana a fuskarta
"Ina fata wannan karon a dace. Idan ba haka ba kuma zanyi maganinta da kaina. Shiru shirunta irin na munafukai shi nafi tsana. Kinsan irinsu abin tsoro ne. Ga wannan yarinyar da suka zo tare mai cin tsiya. Ina tsammanin horon yunwa zan fara yi musu a gidan"
*KASHE FITILA*💡10

*Batul Mamman*💖

Ranar laraba da daddare Gimbi da kanta tayi girki sabanin yadda ta saba saboda yanayin aikinta Laminde ce take yi. Maganin da aka karbo mata ta juye shi tas a miyar Awaisu ta kara maggi.

Da ya dawo dakin Maamu ya fara zuwa ya gaisheta tare da zama zai fara hira ta dube shi duk da alamun gajiya a tare dashi
"Ka tashi kaje kaci abinci ka huta na yafe hirar nan"

"Maamu ni sai kiyi ta korata. Da Yaya Harisu ne ai sai kin gama sauraronsa"

"Sannu baban kishi. Yanzu dai ka tashi, ka ga matarka itama ba zama take yi ba. Dan lokacin naku kuma bazan so na hanata sakewa ba. Ni ban zo gidan nan don takura muku ba. Abokan hirar nawa ma abinci suka tafi ci. Yanzu zaka ga sun dawo"

Tashi yayi rike da coat dinsa a hannu yace zai dawo bayan yaci abinci yayi wanka. Har ya fita tana cewa ta yafe hirar yau.

Wanka yayi Gimbi ta biyo shi da abincinsa daki wai falon hayaniya tayi yawa. A haka tana yi masa hira ya cinye tuwon da ta zuba masa harda neman kari. Dadi ya kamata kuwa. Yanzu abin da ya rage kawai shine ta fara gwada aikin maganin.

*****
Washegari saboda fitarsu aiki da zuwan yara makaranta tun asuba suke tashi ranakun aiki. Kitchen ta shiga ta aunowa Laminde shinkafa sannan ta fito da kazar da ta tafasa tun dare.

"Kiyi min jallof din shinkafa taji alayyahu da busasshen kifi. Wannan kazar kuma pepper chicken nake so kiyi. Kiyi komai cikin sauri kinsan Abbansu Daula baya son jira."

Laminde ta gyada kai "To Hajiya, amma shinkafar bazata ishemu har su Hajiya Babba ba da 'yan makaranta"

Gimbi ta koma store din da yake cikin kitchen din ta dawo rike da wata karmasasshiyar doya. "Shinkafar ki dafa mana ni da yara da babansu. Wannan doyar kuma fate zaki yi muku ke da sauran mutan gidan"

Laminde ta kalli doyar ta kalli uwargijiyarta. Ita dai tunda take a gidan ba'a taba yi mata wulakanci akan abinci ba. Wani lokacin ma ita Gimbi take barwa zabin abincin da za'a dafa. Kasa shiru tayi ta dan rausayar da kai tana kara kallon doyar da ta bushe

"Wai Hajiya nace ba, uhmm ita Hajiya Babba nake nufi ki karo shinkafar saboda ita"

Daure fuska Gimbi tayi "sunanta Maamu ba Hajiya Babba ba. Wannan so kike yi wani yayi zaton ni da ita uwargida da amarya ne. Anyway, itama faten zaki zuba mata naji ance tana son doya. Ga langa can da na karbo wurin Mama. Kinsan mutanen da suna son komai irin na zamaninsu. Shine na nace har sai da Mama ta bani cikin nata tun na aure. A ciki zaki rinka zuba mata abinci. Kuma kiyi sauri tare zamu fita zan aike ki"

Kasa hadiyar yawu Laminde tayi domin tsananin mamaki. Langa ce da gaske ga kuma doya da akace ta zuba mata. Ko ita da take aiki yau tasan anso wulakanta ta bare uwarmiji. Magana take son yi amma sam bakinta ya kasa hada kalma ko daya. Tana ji Gimbi tace ita zata yi musu nasu girkin wanda suke tafiya dashi wurin aiki yaran kuma suje dashi makaranta. Ita kuma tace tayi sauri tayi faten kada su makara.
*****

Rumana cikin sauri ta gama shirinta tsaf saboda bata so a jirata. Tun fara zuwa makarantarta kwanaki biyu da suka wuce tare suke fita da yaran gidan da Gimbi. Dreba ne yake kaisu makaranta ya wuce da ita wurin aiki. Tunda a banki take shiyasa suke yin sammako sosai.

Ko da ta fito falo Mu'allim ne kawai Gimbi take bashi abinci a baki yana ta rigima shi bacci yake ji. Har kasa ta durkusa ta gaisheta sannan ta nufi dinning table inda kayan tea suke zata hada.

"Dakata Rumana me zakiyi a nan?"

Murmushi tayi ta kirata yadda yaran gidan suke kiranta "Mummy tea zan sha kafin su Haris su fito"

"Kinga daga yau ki rinka zuwa wurin Laminde ki sha tea din a can."

Bata ji komai a ranta ba tayi hanyar kitchen. Sake dakatar da ita Gimbi tayi "Kiyi sauri kisha ki fito kada ki makara"

Dayake bata san sunan dreban ba sai tace "Mai kaimu makarantar har yazo ne? Bari na fadawa su Amir suyi sauri su ma"

"A'a kina jina ko Rumana, makarantarku ba wani nisa gareta ba. Ki rinka shiryawa da wuri kina tafiya. Tafiyar da mukeyi da ke tasa ina makara kwana biyu. Gashi ba'a gama abinci ba. Idan kin dawo sai ki ci. Tea din ma ruwan zafin aka juye a girkin sai an dafa wani"

Sai a lokacin Rumana taji wani iri a ranta.
"To Mummy bari na tafi, sai kun dawo"

Gimbi harda murmushi "yauwa Rumanan Abba. Allah Ya kiyaye kinji."

Rumana ta dan tsaya jim ko zata bata kudi tunda sai hudu da rabi suke tasowa. Gimbi ta fahimci dalilin tsayuwar ta dan sake fuska "ko akwai wani abu ne Rumana?"

"A'a babu komai. Na tafi"

Fita tayi tana tafiya a hankali. Allah Yasa makarantar a bakin titi take kuma babu wuyar ganewa. Tafiyar minti shabiyar zata kaita idan tayi sauri. Iyayenta ne suka fado mata a rai taji kamar ta fashe da kuka. Bata san yadda zata fassara abin da Gimbi tayi mata ba. Tayi kamar minti biyar tana tafiya taji mota ta tsaya a gefenta. Horn da akayi yasa ta kalli motar. Mace ta gani tasha lullubi sai wata yarinya mai uniform irin nata. Da ta sake kallonta ta tuna ajinsu daya duk da bata san sunanta ba. Gaishe da matar tayi cikin hausarta.

"Shigo mu karasa kin fito cikin sanyin nan ko rigar sanyi babu. Kada kiji tsoro ga Yusra ajinku daya tace min"

Bayan motar ta shiga ta sake gaisheta sannan Yusra ta juyo "Sunanki Ummu Ruman Abali ko"

Rumana ta gyada kai tana murmushi. Hira uwa da 'yar suka cigaba da yi har suka iso kofar makarantar.

"Umma baki bani kudin break ba fa"

"Yusra bana son wannan kashe kudin da kike son koya. Ga abinci nan a jakarki"

Yusra ta sake kwantar da kai "Umma ko hamsin ce saboda siyan ruwa"

Dari biyu maman ta mika mata "gashi ku raba da Rumana idan kun fito. Allah Ya bada sa'a"

Rumana tayi mata godiya suka jera cikin makaranta tare da Yusra wadda take yi mata tambayoyi akan makarantar da ta baro. Da haka ta manta da bacin ran da ta fito dashi.
*****

Duk sun gama shiri sun fito Awaisu ya tambayi ina Rumana. Gimbi tace
"Ta tafi, wai makarantar babu nisa zata rinka tafiya da kanta."

Bai ce komai ba suka fice saboda ya leka Maamu tana bacci.

Bata farka ba sai karfe tara da kusan rabi. Sabanin yadda ta saba ganin tray din abincinta na safe yau babu komai a wurin sai wata langa da cokali makale a hannunta. Bata kula ba ta shiga bandaki tayi wanka. Sai da ta gama shirinta ta zauna shiru Laminde bata kawo abinci ba. Fita tayi falon taji gidan tsit alamun ita kadai ce. Komawa dakin tayi tana tunanin ina Laminde taje haka. Dama ita take tayata hira kafin yaran su dawo daga makaranta. Langar ta sake kallo bayan ta koma sai ta bude. Faten doya taci karo dashi yayi wani baki ya cure wuri guda saboda rashin wadatar mai. Haka aka yi shi kandas sai kan sauran kifin da Gimbi tayi musu abinci. Mayarwa tayi ta rufe zuciyarta tana karyata cewa wannan abincin nata ne.10*KASHE FITILA*💡11

*Batul Mamman*💖

Haka Maamu ta zauna har azahar bata ci komai ba ga yunwa tana ji. Tasan dai wurin biyu da rabi yaran suke tasowa daga makaranta. Kila su dawo tare da Laminde. Da wannan tunanin ta cigaba da zama har uku ta wuce.

Karfe daya da rabi dreba ya kira wayar Gimbi ya sanar da ita zai je dauko su Haris. Ta umarce shi da idan ya daukosu ya taho dasu bankin su jira har ta tashi. Da farko wurin Mama tayi niyar cewa ya kaisu. Sai ta tuna zata iya cewa me ya hana su koma gida saboda Islamiyya. Ita kuma ko tana hauka bata jin zata taba tura yaranta gidan Anti Bebi. Ita din ma da take zuwa yanzu don biyan bukatar kanta ne kawai.
Chapter 7 · 0% Book details