← Book details Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Kashe Fitila Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan Alh Mudi ya yace lallai sai Awaisu ya zauna a Abujan domin idan ya bayar da takardun washegari mai yiwuwa zuwa litinin a bukaci ganinsa a bankin. Sannan yayi alqawarin bashi makwanci har zuwa lokacin. Harisu ya rasa bakin godiya. Mutanen kirki basa karewa a duniya. Sai dai haduwa dasu dace ne. Duk kudin Alh Mudi Maibuta bashi da dagawa da girman kai.

Da safe Harisu ya koma Fika bayan yaja kunnen dan uwansa akan ya kula da kansa kuma ya kame mutumcinsa.
*****

Tun tafiyar yayansa baya fita ko'ina. Kullum yana daki sai sallah da take fitar dashi wadda Alhajin ko wani saurayi da Awaisu bai tantance matsayinsa a gidan ba suke jagoranta. Safe, rana da dare maigadi zai miko masa abinci ya karba da godiya.

Yau lahadi sun idar da sallar magariba Alh Mudi yace ya shigo falonsa su gaisa da iyalin gidan. Domin idan har ya sami aiki an barshi a nan Abujan to dole kafin ya sami wurin zama nan zai cigaba da zama tare dasu.

"Ni kuma ba mazauni bane, shiyasa na ga ya kamata kasan mutanen gidan suma su san ka"

A baya ya bishi suka shiga wani falo wanda aka kawata da duk wani abu na jindadi. Kafin su zauna wata mace ta shigo sanye da hijabi da alamun sallah ta idar. Sai 'yan matan ranar da suka zo biyu da wani yaro da suke sallah tare wanda bai wuce shekara goma ba.

Awaisu ya gaisheta ta amsa da fara'arta ta tambayi sunansa.

Kafin ya amsa babbar wadda yake tsammanin ita Alh Mudi ya kira da Gimbi tace "A.S Abali, Mama shine yayi vice president na S.U.G a makarantarmu"

Da mamaki ya dago yana kallonta. Shi dai bazai iya tuna fuskarta ba amma dai abin da ta fada gaskiya ne. Kyaunta kuwa tuni yayi tasiri a zuciyarsa.

Maman tace "Gimbi rawar kai, ai ba ke na tambaya ba. Naga yayi shiru ne shine nake son jan shi da hira ya sake damu."

Ta koma tana kallonsa "Alhaji yayi min bayanin komai game da kai. Allah Ya bamu ikon zaman gaskiya da amana"

"Amin Hajiya nagode. Allah Ya kara girma"

"Amin, sai dai Mama ake kirana ba Hajiya ba"

Daga nan sun dan taba hira wadda hankalinsa gabadaya yana kan Gimbi. Tunda ta fadi sunansa dazu zuciyarsa take kawo masa sabon tunani game da ita. Sai dai a wurin ya yakice shi. Ai ido ba mudu ba amma yasan kima. Ina shi ina 'yar babban gida irin wannan.
*****

Washegari da sassafe ya tashi ya shirya kamar yadda Alh Mudi ya umarce shi. Yana wurin maigadi suka fito tare da Gimbi. Taci kwalliya tayi kyau sosai.

A bayan mota ta zauna kusa da babanta shi kuma Awaisu yana gefen dreba. Babu inda ya gane a wurin da suke tafiya sai dai kawai yaga an rubuta Zenith Bank. A reception Alh Mudi ya barsu shi da Gimbi ya wuce wurin manaja.

Hira suke tabawa jefi jefi saboda shi dai ya kasa sakewa da ita duk kuwa da cewar ya fahimci sakon da yake boyewa a zuciyarsa itama shine a cikin ta ta zuciyar.

Ba jimawa Alh Mudi ya fito ya bukaci Awaisu ya shiga wurin Manaja. Shi kuma suka shiga wani dakin daban da Gimbi. A nan ne aka yi mata bayanin aikin da zata rinka yi.

Shi kuma Awaisu takardu ne aka bashi yayi ta cike cike. Bayan ya gama aka sanar dashi zai dawo washegari interview sannan yaje Lagos sati na sama training na wata daya daga nan ya jira posting.
[7:43PM, 1/20/2018] Sweety: *KASHE FITILA*💡5

*Batul Mamman*💖

Abu kamar wasa sai gashi komai ya kankama dangane da samun aikinsa. Awaisu ya koma Fika sanar da mutan gidan halin da ake ciki da tafiyar da zaiyi Lagos.

Kafin ranar tafiyar Maamu ta tura shi wurin yayanta ya karbo rago biyu cikin tumakin da ake yi mata kiwo ya sayar. Da kudin wanda ko sisi bata cire a ciki ba tace yayi kudin mota da guzuri.

Kamar kullum kyakkyawar addua yayi mata tare da godiya.
"Ba godiya zakayi min ba. So nake idan kaje ka dage yayi abinda ya kaika. Lokaci yayi da ya kamata ace kana da iyali kaima sannan ka fara ragewa dan uwanka nauyi. Ga zuri'a Allah Ya bashi sosai. Kaga yanzu cikin yaran sai ka rinka biyawa wasu kudin makaranta idan ka fara daukan albashi"

"Maamu kenan, Allah Ya bani iko. Nifa babban dana ma sunansa Haris. Tun yanzu ya kamata ki fara kirana Abu Harith irin na Larabawa"

Neman abin da zata buga masa tayi saboda rashin kunyar da yake yi a gabanta. Ba shiri ya tashi ya gudu.

Bayan kwana biyu Harisu ya raka shi tasha ya wuce Lagos. Watansa daya wurin induction din sababbin ma'aikatan banki. Ana gamawa ya koma Abuja domin jiran posting. A wannan lokacin ne kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsa da Gimbi. Tun yana ja da baya har ya amince. Ji yake yafi kowa sa'a. Mace kamarta tana soyayya da talaka irinsa.

Da taimakon Alh Mudi ya samu aka barshi a Abuja maimakon Ilorin da aka tura shi da farko.

Ganin yana da kwanaki goma kafin lokacin fara aikin ya hada kayansa sai gida. Gimbi harda kuka da zai tafi saboda sonsa take da gaske. Alkawari yayi mata cewa bazai wuce sati ba zai dawo sannan suka rabu.

Yana isa gida yara suka fito ana ta murnar dawowarsa. Ya shiga ciki nan ma su Baaba sai murna aiki ya samu. Nan yake jin kwanaki hudu da suka wuce matar Harisu ta biyun ta haihu. Kai kace shi aka yiwa haihuwar ya fita neman dan uwanansa yana murna.
*****

Washegari suna zaune a bakin shagon Harisu suna hira Awaisu yace ya zabawa jaririya suna Ummu Ruman. Amma Rumana za'a kirata.

"Kai kuma a ina kaji wannan sunan" Harisu ya tambaya yana kallonsa.

"A littafin tarihi"

"Idan munje gida sai kayi mata huduba dashi" cewar Harisu

Duk da cewa ya riga yayi mata da suna Aisha amma baya son batawa kaninsa. Shima kuma Awaisun da yasan da hakan bazai taba kawo wani sunan ba.

Sai yamma suka koma gida. A bakin kofa ya tarar da dansa na biyu yana shirin fitowa.

"Sarkin yawo ina zaka da yamman nan"

"Baba kayi bako daga Kano. Shine aka ce na kirawo ka"

Harisu ya shiga ciki dakin Baaba inda suke yana tunanin waye yazo.

Abin mamaki Saminu ya gani tare da matarsa da yaransu biyar. Tsabar murna ya rungumeshi suna dariya.

"Bala dreban tifa ne ya fada min haihuwar nace to lokacin tada zumuncin mu fa yayi. Dole mu hada kan iyalinmu."

"Sosai kuwa, sannu yaya hanya"

Matar Saminu mai suna Amina da yaransa duk suka gaishe da Harisu. Ana ta barkwancin yadda zasu rinka magana tunda Hausa a gidan bata zauna sosai ba. Baaba da Awaisu sune masu Hausar sosai. Awaisun shima ya shigo suka gaisa. Fita yayi sauran kudin hannunsa yasa ya siyo lemo, kaji da kwai ya bawa Maman Antu uwargidan Harisu domin karrama baki. Yaushe zai manta Saminu a rayuwarsa.

****
Kwanansu hudu a gidan duk an saba kamar sun dade tare. Yaranma kowa da abokin sa ban da babbar wadda ta girmi duka yaran gidan.

Ana gobe zasu tafi ne Harisu da Saminu sun zauna hira da daddare Harisu ya sako zancen da yake ta son yi.

"Mardiya shekararta nawa ne yanzu?"

"Ka ganta tayi tsayi ko? Shabakwai zatayi da azumi. Badi zata gama sakandire in sha Allah"

Harisu yayi murmushi "To Allah Yasa abin da zan zo dashi yayi maka. Nace mai zai hana mu hadata da Awaisu?"

Saminu ya kalle shi sosai "da gaske kake yi?"

"Indai ka amince. Wallahi Saminu ban taba ganin mutum irinka ba. Halayenka abin koyi ne ga wasu. Idan na bari damar nan ta wucemu ai na cuci zuri'ar Awaisu. Mai alkhairi irinka dole a kyautatawa 'ya'yanka zato"

Saminu ya kama hannunsa kam "in dai haka ne na bawa Awaisu Mardiya halak malak inyi maka ta yara"

Dadi ya kama Harisu suna dariya "in sha Allah Awaisu bazai bamu kunya ba. Dama watan da ya wuce na gama biyan su Zakiyya kudin gidan Malam da ya fada rabonsu a gado. Gyara shi zanyi sosai kafin shekara mai zuwa shima Awaisun ya tara abin da ya tara sai su zauna a ciki. Ba munyi maganar a Abuja zaiyi aiki ba? To muna sa rai zai sami muhalli kwanan nan. Kaga sai su koma can ya sa ta cigaba da karatu ma"

Saminu farinciki ya cika zuciyarsa. Shi yana yiwa Harisu kallon mutumin kirki. Shima Harisun kallon da yake yi masa kenan.

Sun yanke shawarar sanar da Mardiya babbar 'yar Saminu da Awaisu shawarar da suka yanke domin jin ta bakinsu da kuma basu hakkinsu don kada a zalinci kowa.

Awaisu wanda yake bayan kofa tun bayan yaji an ambaci sunansa ya fasa karasawa wurinsu. Ji yayi kamar an dora mada dutse a kansa. Shi kadai ya soma magana a hankali "yanzu wannan yarinyar da bata gama zama mace ba za'a bani? Wallahi da sake. Ko ban hadu da Gimbi ba babu inda zan kai wannan yarinyar"5*KASHE FITILA*💡6

*Batul Mamman*💖

Tun daga wannan rana Awaisu yake wasan buya da Harisu. Duk inda yasan zasu hadu su kebe guduwa yake yi. Ranar da zai koma Abuja ma kamar ana korarsa don sauri. Haka ya tafi tasha kafin Harisu ya dawo daga shagonsa inda ya ajiye masa kayan amfani kamar su madara da ganyen shayi da yake son bashi guzurin tafiya.

Baiyi sati da komawa ba Alh Mudi ya dawo daga Kano. Wata rana da yamma ya tura karamin dansa ya kirawo Awaisu. Da ya zo ne ya tabbatar masa da Gimbi ta sanar dasu abin da ke tsakaninsu. Karshe yace yana so ya sanar da yayansa cewa su same shi a Kano shi da Saminu idan har da gaske yana sonta da aure suyi magana.

"Ban yarda da bata lokaci ana soyayya ba indai akwai halin yin auren gara ayi kowa ya huta."
Chapter 3 · 0% Book details