← Book details Jeji Girl Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Jeji Girl Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan Abba ya kalleta yace "ikraam shin kinsan Wani abun Gameda iyayenki? Tinda yanzu bakinki yabud'e zaki uyagayamana abunda kikasaki ko hannun wasu mutanen kikataso amatsayin iyayenki? Yatambayeta Yana kallan yanayinta...duk'arda kanta tayi ak'asa kana tace bansan komaiba Gameda kowa Abba inba Abeee naba da ammeee sune kawai nasani acikinsu nataso acikinsu narayu suna bud'e Ido nagani Abba bansan wata kalmaba inba kukansuba dana tsintsaye se k'ugin ruwa Dana iska bansan kowaba sesu tinda nafara wayo sune abunda kemun hidima harna fara yiwa kaina. Dan shiru tayi hawaye nabin fuskarta kamun taci gabada fad'ar bantab'a Ganin halitta irin tawaba seda girmana dasu babbakun mutane keshiga jejin danufin cutardani sune way'anda nafara Gani irin halitta ta Amma Abun gudune ataredani domin nema sukeyi su hallakani kota yaya se idan abeena yakawomun d'auki alokacin. Ya fadeel ne mutun nafarko Dana fara Gani me irin halitta ta Amma bamacuciba sekuma su ya irfaan dasukazo tafiya dashi daga farko batsorata daganinsu Amma danaga basada nufin cuttadani na aminta dasu harnaji ba dad'i alokacinda sukafi. Abba bansan kowaba face namun dawa acikinsu narayu sune iyayena Yan uwana abokaina komainawa Abba ni y'ar gatace agaresu Abba sautin muryarta d'aya ya,Isa yahargitsa jejin Abba domin basa bari kowanne abun cutarwa yarab'eni suna bani kariya fiyeda yadda suke bawa kansu Basa barinada yunwa ko k'ishi Abba sa,Anna ko iskarda Basu yadda da,itaba Bata Isa tatab'ani agabansuba Abba kaga kuwa sunfi iyayen nawa Sona sunfisu buk'atana nibanada wasu iyaye samadasu sekuma kuda yayana inasanka Abba abei Ammi momma ya irfaan ya Hafees ya fadeel ya Mahmoud ya Muneer way'annan sune ahalina jigona Kuma gatana tubalin rayuwata sukuwa namun dawa sune karkuwata Kuma jinin jikina Ina kewarsu sosai Abba Ina kewarsu tafad'a tana rusheda kuka...kowa awurin seda yayi k'wallar tausayinta watodai acikinsu tataso anan tagirma wannan ai Se y'ar baiwa tabbas wannan Al,amarin daga allah ne yak'are baiwarsa Kuma yasaka wasu bayi nasa abun tsoro acikin al'umma suka zame mata karguwa suna gadinta har izuwa lokacinda yatsara zatabar jejin kenan shine sanadin b'atan fadeel tinda komai yanada sanadinsa tabbas iKon allah yafi gaban mmki domin komai narayuwar Dan adam atsare yake tinkafin yashigo duniya.

Nisawa Abba yayi kana yace kiyi hak'uri ikraam kiyi shiru kinji barakiji asalinki Kuma iyayenki nasanki k'addara ce tarasu Dake. Kinga wannan itace mahaifiyarki sunanta Maryam Kuma k'anwace agunsu momm d'inku sudai nasan kinsan komai gamedasu to Maryam k'anwarsuce Kuma mahaufinki mutumin kirkine Alhaji Abbas Kuma buzuneshi haifaffen agadas ne Kuma shid'in marayane ankashe iyayenshi duka shine abunda yasa yabar kasarsu nigar yashigo Nigeria har allah yahad'ashi da mahaifiyarki ya aureta,,mahaifinki Costum ne Kuma jajirtacce ne tsayayyen mutin agun Al'umma da iyalinshi. Alokacinda allah zerabakune aka janzamishi wurin aiki daga Lagos aka mayardashi Ibadan to sesukayi tafiyar cikin dare ana ruwan sama alokacin bakifi 1 month ba da haihuwa Wanda tafiyar itace silar rabuwarku Kuma silar rasuwar mahaifinki ko ita maryam allah yanufi tanada sauran kwana agaba har wasu mafarauta suka tsinceta Amma sunce ita kad'ai sukagani Bada jinjiraba alokacinda Maryam tasamu lbrn dagake har mahaifinki bakwaraye tashiga tashin hankali ba kad'anba kumashi mahaifinki daga Baya ansami gawarshi Amma kekam ko lbrn ki ba,ajiba sedai yau da mahaifiyarki kefad'ar kece y'arta data b'ata Kuma asalin sunanki Khadija ne wato sunan momma.

Kowa awurin shiru yayi Yana sauraren Abba harya Kai k'arshe. Anata jajanta abun yayinda ikraam keta famar rusar kuka itada anty Marwa da anty Safah. Cikin k'arfin Hali tamik'e tsaye zata nufi inda anty Maryam take ai wata azaba dataji taratsata batasan lokacinda tadurk'usaba awurin tana Sakin marayan kuka. Mik'ewa irfaan yajeyi ahanzarce ya Mahmoud Dake kusanshi yarik'eshi Yana nuna mishi anty Maryam da momma tace taje gareta domin tagano wurintane yarinyar kesan zuwa. Tana zuwa tasaka hannu ta tallabota tareda share mata hawaye Kuma itakanta hawayen takeyi tace kiyafemun anty Dhija kiyafemun kinji badasanina kikarayu acikin dabbobiba Kuma bantab'a sanin cewa kina Rayeba sedai Wanda yatsara Hakan yafimu sanin dalilinshi nayin Hakan Kuma gashi cikin ikonshin da buwayarshi yasaka yayunkine suka ceceki kidena kuka kinji kiyafemun...ya,Isa Hakan anty Maryam nibakimun komaiba Kuma inasanki kamar yadda kowacce y'a kesan mahaifiyarta Kuma Ina alfaharida ke da y'an uwanki dakuma y'ay'anki.

Murmushi anty Maryam tayi kana tace muma Muna sanki fiyeda yadda kikesanmu anty Dhija.. dasauri ikraam tad'ago tace anty Maryam ni sunana ikraam shine yayana yasakamun tafad'a tana turo Baki gaba..aiko tabawa kowa dariya hadda anty Maryam d'in cikin dariyar tace tofa 🤔 iKon allah to aidama hakanne sunanki Khadija Kuma ko alokacin da ikraam ake Kiranki domin shine yafara kirankidasunan tinda yaji sunan anty Dhija gareki. Kowa awurin yak'ara Saka dariya. Baki ikraam tak'ara turowa kamun tayunk'ura zata mik'e tsaye cikin sauri anty Maryam tace inazakije? "Gun Ammi tafad'a atak'aice. "Yuzamanki barani nazo sukatsinkayo muryar Ammi d'in...tasowa tayi tazogunsu tazauna tana fad'ar Gani. Jikinta ikraam tashige kamun tamatso k'wallah tace Ammi "kigayawa Abba karya rabanida ya irfaan please tinda kunce Kuna Sona Nima inasan yayana kunga bakwaso arabaku Dani Dan Allah Nima karku rabanida yayana. Tak'arasa zancen tana matsar k'wallah. Kowa awurin yayi mmki Jin furucinta domin ita batasan cewa su Abba wada sukeyiba sabida hankalinta baya taredasu tinda taji ance and'aura aurenta da Hafees.

"Murmushi Ammi tayi kana tajuya tana kallan IRFAAN Shima d'in kuwa suyake kallo yanajin kamar yaje yarungumeta ajikinshi..hannu Ammi Tamik'a mashi alamar yazo. Aiko tasowa yayi cikin sauri Yana Saka hannunshi cikinna Ammi d'in. Kamo hannunta Ammi tayi tasaka cikin nashi kana tace ga irfaan Nan my baby nakine har abada su Abba bazasu tab'a tabakuba domin Suma sunfi buk'atar ganinku atare zancen aurenkida Hafees irfaan ne suke tsokana kinji aure da irfaan aka d'aura Mikishi allah yabaku zaman lpy yakuma albarkaci yarayuwar aurenku ku dukanku. Ameen y hayyu y qayum suka amsa dukkansu kana Ammi tace irfaan d'aukar kakaimin ita bedroom d'in anty Dhija inazuwa tafad'a cikin Bada umurni domin itama ayanzu ta fahimci Wani abun. To kawai yace tareda mik'ewa yad'auketa sukabar parlor. Se alokacin kowa yasaki murmushi kana Abba yace to maryam anjima kowacce amarya akaita d'akin mujinta banaso Ganin kowacce anan..Amma Alhaji ikraam fa batada lpy Kuma..Kinga Khadija mujinta ai ze,iya kulada ita sabida Hakan kowacce akaita gidan mujinta.

"Shikenan Alhaji za,ayi Hakan Amma Dan Allah kayimun alfarman barin ikraam agidana tawarke tukunnah itada zeelha se akaisu lokaci d'aya Rana ita yau mako d'aya kenan Dan Allah. Ammi tafad'a cikin magiya.

Nisawa Abba yayi kana yace shikenan allah yakaimu...Ameen y allah suka amsa kana kowa yawatse. Ammi Kuma tanufi bedroom d'in momma tana zuwa batacewa ikraam komaiba tashiga bathroom tafad'a mata ruwan d'imi dakayan itatuwa Wanda zasu kashe mata raunin kana tazo tad'auketa takaita bathroom d'in. Dakanta tashiga gasata ananne ta tabbatarda zarginta cikin mmki tace iKon allah to ya,akayi irfaan yayi wannan aika aijar yanzu inda ba,a d'aura musu aureba shikenan ananufin y'ay'ansu sunyi Zina kenan? Cikin sauri Kuma takauda tinanin aranta tana istigifari tinda allah yarigada atsare seda aka d'aura auren.

Da yamma akad'auki Amare su Safah da Marwa aka kaisu gidan mazajensu. Ya Mahmoud kamar yatake kan jariri.. fadeel kuwa dayaji zancen ikraam Ashe y'ar anty Maryam ce bak'aramin mmki yayiba kumaji dad'in Hakan sosai domin Shima yanajin yarinyar aranshi kamar zeelha...mom d'in zeelha kuwa da dadynta yagaya mata zancen andaurawa Yarta aure Babushiri batace komaiba kotanuna rashin amincewarta tinda Dama tasanda zancen Hafees d'in addu,a kawai tayi musu tafatan alkhairi.

Bayan ankai Amare Ammi tad'auki Y'arta ikraam suka Koma gida yayinda tatura irfaan yad'auko mata zeelha bayan tayi wayada mmnta tagaya mata zata had'asu ne itada ikraam tasaka agyarasu domin ita y'a take kallon zeelha ba surukaba...aiko mom taji dad'in Hakan sosai batayi wata jayayya da k'awar tataba ta amince bayan tayimusu murnar bayyane ikraam amatsayin yatsu tajini...tofa tindaga lokacinda aka d'auko zeelha Ammi tadage take gyaransu itada ikraam Kuma tin wannan ranar har yanzu Basu k'ara had'uwa dajunaba tsakanin ikraam da irfaan hakama Hafees da zeelha. Ayau kwanansu shida gidan Ammi Kuma akulle basafita ko parlor daga bedroom d'in Ammi se bathroom sunyi kyau iya kyau Kuma suntsimu iya tsimuwa domin dudda zeelha da take normal yanzu tafara Jin buk'atar namuji atareda ita balle Ikraam da damacan ya lafiyar kura😂

Ashe gari tinda suka tashi aketa shirye shiryen tarewarsu domin abei yace da kanshi zekaisu gidajensu domin bayan gidan momma ne gidansu yake aiko Hakan akayi sabida ana gama Isha yazo yace sufito sutafi...Ammi tagyara yaranta iya gyara Masha allah Tami musu shiga iri d'aya takayan antamfa ahakan tafito dasu tanajin kamar tamayardasu ciki Dan so..ahakan abei da dadyn zeelha suka saukesu zuwa gidan mazajensu batareda ma ankaisu gun iyayensu mataba sumusu addu,a sedai kawai sukayi musu ita daga inda suke domin Ako,Ina mutin yayi addu,a Allah najinshi fatarmu kawai allah yakarb'i addu,oin mu Baki d'aya 🤲

Seda suka tsaya Bakin get d'in gidan momma suka kira Hafees da irfaan sa,annan suka tafi atare sukakai kowacce amarya da mujinta d'akinsu kana suka musu addu,ar zama lpy da albarka acikin rayuwar aurensu kana suka musu sallama suka tafi...!

iKon allah 🤔 yau akaron farko naga ankai amarya ada ango alokaci d'aya lallai abei abunka azimunne😂

*JJG*

___✅___&&&&&&&&&&&&&

Paid
Page 55 & 56

"Suna fita irfaan yarakasu har seda yaga tafiyarsu kana yacewa Muneer yak'araso su abei suntafi yakashe wayarshi...kominti 2 beyida kiranshibe segashi ya,isoda mota yafaka bud'ewa yayi yafito dawasu manyan ledoji hud'u yabawa irfaan din kana yajuya yayi tafiyarshi....shiko IRFAAN gidan Hafees yanufa taredayin nocking

Hafees d'inne yataso yabud'e gidan Yana mmkin wake yimasa nocking yazu..aiko seyaga irfaan tsaye murmushi yayi Yana fad'ar yadai angon kafin tariya domin mudai seda mukatare zamu angance...harara irfaan yawatsa masa kana yamik'o mishi Leda biyu batareda yace komaiba yajuya zuwa nashi gidan

Koda yashiga tatashi daga inda yabarta tashiga bathroom tana wanka murmushi kawai irfaan yayi yakum yace wannan amaryar se ita,,,kana ya,ajiye ledojinda yashigo dasu kana yajuya izuwa nashi bedroom d'in...Shima Yana shiga bathroom d'in yawuce domin yayi wankan.
Chapter 19 · 0% Book details