← Book details Jeji Girl Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Jeji Girl Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌳🌴🌳 *JEJI GIRL*🌳🌴🌳

SANARWA!
Wannan littafin Yasmeen Ahmad (Autar Alheri) ne kuma akwai wadanda su ka sanya batun ba free ba ne na siyarwa ne, duk wanda ya tura kudi domin siyen littafin nan muddin ba Yasmeen Ahmad ce ya turawa ba to ya fada hannun masu ci da guminta ne, idan da hali sai a fada mata domin ta dauki mataki.

An dauko littafin ne a shafin www.hausanovels001.com.ng
sannan kuma duk mai bukatar mgn da mu zai iya tuntubar mu daga cikin WhatsApp community dinmu da za a samu link dinsa a kan website dinmu can kasa wurin download na littafi, mun gode.

(Yarinyar jeji,,renon namun dawa👱‍♀️🦣🦍🐆🦑)

*Labari meban Al,ajabi da birgewa (romantic love and sexy story)*

Daga alk'alamin taku har kullun Autar alheri ✍️ marubuciyar 👇

SOLDIERS FAMILY
INGARMAN NAMIJI
WAYE MIJINA return
TANTIRANCI sabon salon
IZZAR MULKI
BIG LADY'S
MY LITTLE SISTER

Wannan novel paid book ne Kuma Dan Allah idan bakida aure karki karantamun novel banasan kananun zantuka harkullun Ina gayamuku domin kawo sauyi acikin rayuwar ma,aurata muke bayya komai acikin novel Amma bakwa fahimta,,bazamuyi novel Dan bata tarbiyar kowanne yaroba domin muma iyayene mun Haifa kozamu Haifa sabida Hakan Dan Allah kowa tayi Sha,anin gabanta.

Gargad'i ban yarda kowa yajuyamin novel ba Kuma banyadda akarantamun Abu afidda audio ba indaibatareda izininaba.

*Idan Baki biyaba karki karantamun novel idan Kuma kika karanta kokika fitar batareda kinsan wahalar danayi wurinyin abunaba keda allah 🤷*

Bismillahirahmanirrahim

Free
Page 1 & 2

_____✅_____&&&&&&&&&&

"Wata motace kitafiya acikin dokar daji daga Legos zuwa Ibadan tafiya takeyi hankali kwance mutanen ciki sefira sukeyi ahankali cikin nishad'i da kaunar juna daga Gani base katambayaba kasan cewa mata damijine

Da jinjirar yarinya ahannun matar tafiya sukeyi suna yankar Jeji sosai sukayinisa cikin tafiyarsu,,,hadarine yataso Babu kama hannun yaro me iska da tsawa,,cikin tsoro matar tace "Alhaji hadarinnanfa yataso sosai Kuma gashi dareyayi inajin tsorofa musamu mutsaya harya lafa..dubanta yayi cikin murmushi kana yace shikenan hafsat yafad'a taredayin perking d'in motar agefen hanya,,kana yakarb'i yarinyar Dake hannunta kyakkyawa da,ita Yana mata wasa,,sunjima ahakan kamun ruwa sukece kamarda bakin k'warya ruwa akeyi sosai kamar zasutada garin abun har zabban tsoro,,itadai hafsat inbanda addu,a babu abunda takeyi yayinda megidan nata kuwa ko, ajikinshi,,,anjima sosai anaruwannan kamun Kuma sud'auke d'if kamar ba,ayiba se walk'iya kawai da,akeyi jefi jefi,,,motar yatayar kana sukaci gabada tafiya Ammafa garin yayi Baki kirin ga duhun hadari gana dare gakuma sanyin damuna

Sunyi tafiya medan Nisa kana hafsat tadubi megidan nata tace wlh ni banasan tafiyar dare seda nace mubari mutafi Ido naganin Ido Amma kace aa...murmushi yayi kamun yace to ai allah yakaddari yanzune zamuyi tafiyar Kuma bakisan manufarsa tayin Hakanba..berufe bakiba suka d'auki salati atare sabida fad'awa dasukayi cikin Wani katon ramen dayacika tab daruwan sama jikakeyi tsum,dummm motar tanutse duka acikin ruwan..hasbinallah😥

Washe gari dasanyin asuba haske yad'an fara fitowa nahango jaririyarnan kwance agefen wasu manyan ruwan gadukkan alamu tekuce anan,,abunda yafaru ajiya motar nafad'awa ruwa allah yabawa hafsat iKon bud'e gabun motar tafito itada jinjirarta sedai Bata iya ruwaba kamun tayi Wani yun kurin tuni igiyar ruwa takarb'e yarinyar tayi gabada,ita itako akayi gabada,ita..to shine ruwan suka wullo yarinyar anan.

Yarinyar jinjira abun tausayi se cilla kafafunta takeyi sama tana kuka,,,Wani katon kada🐊ne yafito abakin ruwan yahangi yarinyar cikin zumud'i yanufota domin yunwar safece tafito dashi,,daga gefe Kuma zakine🦁 kwance Yana kallanta nesa dashi kad'an tawagar giwayene🦣 sukazo Shan ruwa daga Saman bishiya kuwa Wani katon gwaggon birine Wanda akekira gorilla 🦍ke zaune Yana Hangen yarinyar,,,cikin Isa datak'ama irinta sarakunan namun dawa zakinnan🦁yafara nufota Shima,,Dede lokacinda giwayennan suka,Iso suka mazajen suna rigangan wurinyin lak'um da baiwar allah,,,,adede lokacinda suka k'araso wurintane Wani irin haske yabaibayeta Wanda duk yakashe musu idanuwa dukkansu suntsorata domin kowacce halitta akwai tsoro acikin rayuwarta.

Bayan wasu sakanni wannan hasken yab'ace b'at kamar bewanzuba,,,abun mmki haskennan nab'acewa se way'annan manyan halittun masu razana D'an Adam suka fara zagayen yarinyar suna shinshinarta sunjima ahakan sunata zagayenta ba Wanda ya,iya yimata komai...sayin wurinne yafara ratsata sosai Hakan yasa tafara tsandara Kuma tana wulla kafafuwanta sama...cikin sauri giwarnan tasaka jelarta tanad'ota tadayin sama da ita,,,Ganin Hakan yasa wannan gwaggon birin saukowa daga Saman bishiya takarb'eta daga hannun giwar tareda yaye kayan jikinta da towel d'inda aka nad'eta ciki yayi mata tsirara,,kamin yagama tubeta tuni zaki yasaka kohotunshi Yana had'a karanda kewurin Yana tarasu wuri d'aya,,,shiko birin yagama cire mata gayan kenan Sega k'waguwa🦑tafito kamar abunda akaturo tahad'a jelunanta tarik'a bugasu aiko Sega wuta takama cikin sauri birinnan yafigo wata katuwar kunnen bishiya me fad'i sosai yad'ora yarinyar Akai kana yazo kusan wutarnan da,ita yanad'an jigata alamar rarrashi,,atake kuwa tayi shiru.

Itakuwa giwarnan katuwar bishiyar lemu Dake wurin tarik'a girgizawa tana kad'o yayan tana Saka kafarta tana dansu kad'an sunayin laushi,,, birinnan na hud'eshi Yana matsa mata abaki tanasha harta k'oshi se bacci...kallan kallan sukatsaya yiwa juna ga dukkan alamu kowannensu soyakeyi yayi renon yarinyar Amma bahali tinda basuda hannun d'aukarta Hakan yasa suka barwa birin dole Badan sunsoba Amma fa anan kan katuwar bishiyar rini Dake bakin ruwan suka aminta yazauna da,ita yagano hakanne tahanyar zagayenshi dasukayitayi Kuma suna zagaya bishiyar.

Atake yahaye Saman bishiyar yashiga had'a sanyunta da hakinta Yana had'a Dan k'aramun bukka kamar gije,,seda yagama had'awa kana yashiga cikin jeji shida giwa dakuma Wani shirgegen maciji🐉 daya take musu baya..kad'a da zaren tunfafiya birinnan yashiga had'awa Yana murjesu gu d'aya idan ya murje seya majininnan yanad'eshi ajikinshi kana giwa tarik'a janshi da jelarta kana birin yadawo yarinka sak'ashi atake suka had'a mata zannuwa irinna kayan jeji Dade abunda zasu rik'a nad'eta dashi kana suka dawo inda sukabar basawan nagadinta.

Abakin babbar tekun Legos Wani matashin saurayine Dan kimanin shekaru 22 tsaye yake Yana d'aura igiyar shiga ruwa,, kyakkyawan saurayine ajin farko gashi fari tass kanar ka kwanta jini yafito yanada manyan idanuwa masu firgitarwa Kuma inada tsayi Dede gwargwado Dan k'aramun bakinshi medaukeda pink lips Wanda kananun Suma baka tayi liflif azagayenshi,,,yanada fad'ad'an girji medaukeda lallausar suma Masha allah irin k'irar jikinshi itace akekirada namujin zaki abun gwanin ban Sha,awa..Yana gama d'aura igiyar kawai yayi supa daga cikin katon jirgin ruwan🚢 se acikin tekun..!

Humm 🤔 muje zuwadai salon wannan labarin dabanne karku manta *JEJI GIRL* paid book ne Kuma idan kinada buk'atarshi nera 500 ne kacal zaki iya tura kud'inki ta wannan account d'in 👉2276776261 Sha,awanatu kasim UBA bank...kana kitura shedar biyanki awannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp

Autar Alheri ✍️
🌳🌴🌳 *JEJI GIRL*🌳🌴🌳

(Yarinyar jeji,,renon namun dawa 👱‍♀️🦣🦍🐆🦑)

*Labari meban Al,ajabi da birgewa (romantic love and sexy story)*

Daga alk'alamin taku har kullun Autar alheri ✍️ marubuciyar 👇

SOLDIERS FAMILY
INGARMAN NAMIJI
WAYE MIJINA return
TANTIRANCI sabon salon
IZZAR MULKI
BIG LADY'S
MY LITTLE SISTER

Wannan novel paid book ne Kuma Dan Allah idan bakida aure karki karantamun novel banasan kananun zantuka harkullun Ina gayamuku domin kawo sauyi acikin rayuwar ma aurata muke bayya komai acikin novel Amma bakwa fahimta bazamuyi novel Dan bata tarbiyar kowanne yaroba domin muma iyayene mun Haifa kozamu Haifa sabida Hakan Dan Allah kowa tayi Sha,anin gabanta.

*Idan Baki biyaba karki karantamun novel idan Kuma kika karanta kokika fitar batareda kinsan wahalar danayi wurinyin abunaba keda allah*🤷

Free
Page 3 & 4

_____✅_____&&&&&&&&&&

"Iyo yakeyi sosai acikin ruwan kamar Wani kifi,,se igiyar ruwa tajashi sosai kana ta hantsilodashi sama abun gwanin birgewa..Baki amininshi Hafees yasaki Yana kallan iKon allah dudda suke sojojin ruwa Amma shikan Sam baze,iya wannan kasadarba,,yajima tsaye yanasan Ganin ta,inda abokin nashi zefito Amma Sam ko alamarshi Babu,,seda yab'ata lokaci sosai har Hafees yafara shiga fargaba sekawai ya hantsilo tabayan Hafees d'in yafad'o cikin jirgin jikinshi shab'e shab'e daruwa..jiyiwa Hafees yayi cikin sauri Yana kallanshi yadda yawani had'erai kamar besan minene dariyaba kwantacciyar sumar jikinshi kuwa se sheki takeyi.

Murmushi Hafees yayi yace duk wannan cin maganin na minene my friend? Dan kawai banbika cikin ruwaba? Humm Toshikenan Yi hak'uri kaji lpyrmu ce ba d'aya ba nikam idan nashiga ruwa ai sedai ummi ta,aifi Wani badainiba.

Harara yazabga mishi kana yad'auki towel Yana tsane jikinshi zuwa sumar kanshi,,wayarshi yakallah datake famar ruri tindazu,,se ayanzu yasaki lallausan murmushin gefen Baki Wanda yak'arawa kyakkyawar furkarahi kyau da haiba Ganin sunanda ke yawo akan fuskar wayar waro momma,, d'auka yayi cikin nutsuwarshi yak'ara akunnenshi tareda bud'e Baki kamar meshirin kuka yace momma..Ido nazaro Jin daddar muryarshi kamar ana busa sarewa domin kuwa samun namuji me irinnan wannan muryar gaskiya zeyi wahala ko,acikin kabilar Fulani.

Daga gefen momma kuwa murmushi tayi cikin sanyin hakinta tace babana kana lpy? "Shiru yayi kamar bazeyi komaiba sekuma yad'an turo Baki gaba kana yace lpy qalau momma se kewanki kawai... murmushi momma tayi kana tace Masha allah ai dasauki tundadai Kuna lpy Ina Hafees ne?

D'agowa yayi yawatsawa Hafees harara kana yace gashi anan momma..to shikenan kagaidamin shi Kuma karkamanta kudawo cikin lokaci domin abbanku yatamba yoshe zakudawo nacemishi bazaku jimaba..shiru yayi Yana saurarenta seda takai k'arshe Yana yalumshe kyakkyawan idanuwanshi yace shikenan momma za,ayi yadda kikace..kana sukayi sallama yayanke wayar....kallanshi Hafees yayi Yana fad'ar momma tace mudawo ko? "Tashi yayi yaname shigewa Wani room daga cikin jirgin batareda yace komaiba...murmushi kawai Hafees yayi kana yace me Hali baya canja alinshi..

Yau kusan sati biyu kenan da zaman wannan jinjira acikin jeji k'ark'ashin kulawar manyan dabbobin dawa,,abunda zebaka mmki acikin wannan Karin shine bawani abunda yasamu wannan yarinyar Kuma tanacikin k'oshin lpy da kulawar sarakunan dawa..kwance take akan shimfid'arta da gwaggon biri tayi mata agefen teku se cilla kafafunta takeyi Asama tana kallan tsuntsayenda keyawo suna shawagi,,,bakowa awurin daga ita se halinta take wasarta cikin nishad'i daga Babu yunwa ko k'ishi atareda ita...hajiya boss ce tagitto tawurin tana tafe tana tak'ama wato kura,,tana hango kafafun mutin Yana cillawa tayi saurin nufo wurinta cikin mugun nufi nasan tacinye yarinyar yadda take tafe tana irin kukannan nata Wanda takeyi idan zatayi mugunta tana zazalo harshe wajene yafirgita wannan jinjirar domin daga inda take kwance tana hangota Kuma ak'allah yarinyar zatakai watanni 5 Hakan yasa tasan tsoro,,,wata irin k'ara tacillah tareda shek'ewa lokaci d'aya.
Chapter 1 · 0% Book details