← Book details Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama hajara ba ta ɓoye masa komai ba da ya shafi rayuwarta da ɗanta ya matuƙar tausaya mata kafin a ƙarshe ya nemu buƙatar aurenta daƙyal ya sha wahala kafin ta amince dukda itama hada jan aji da tsoron abunda ya faru da ita a baya kafin ta amince bayan sunje Haɗeja ta nema wasu daga cikin dangin mahaifinta suka ɗaura musu aure wanda lokacin sosai tayi mamakin halin da ta samu matan babanta da ƴan uwanta nan take samun labarin shafa tayi aure a katsina ta so ta taimaka musu amma hassada ta hanasu karɓa dukda suna buƙata domin sunyi mamakin yanda suka ganta a tunaninsu zuwa yanzu ta gama lalacewa domin a tunaninsu yanda suka koreta bata da wajen zuwa zuwa yanzu ta zama magajiyar karuwai Sai suka ga saɓanin haka,

Sai a lokacin ne Hajara ta san ta yi Aure domin Kulawa tattali soyayya kawai take samu daga wajen mijinta har mantawa suke da shekarunsu kamar su cinye juna don ƙauna to daman ba wasu yara gare su ba Sadeq ya na Karatu a india domin tsakaninsa da Ashraf shekara biyu ne Ashraf ya basa saika ɗauka ma ƴan biyu ne don sadeq ya fi Ashraf girman jiki hakan yasa ajinsu ɗaya a karatu don sadeq ya ma rigasa tafiya india da wata ukku.

Ashraf ma tare da Marzouq sun wuce switzerland tare wanda suka zama aminai tamkar uwa ɗaya uba ɗaya domin sa’anni ne haka suka ɗauki hajara tamkar uwa itama ta ɗauke su tamkar ita ta haife su ba ta banbanta su da ɗanta,

Tafiyar Marzouq karatu ba ƙaramun cigaba ta samar musu dashi ba domin overoller ya ke fitowa dashi a result Gefe guda kuma ya fara neman kuɗi wanda kafin ka ce me ya tara arziƙi mai yawan gaske ,

Mechanical engineering ya ke karanta Hakan ya ƙara haɓɓaka kasuwancinsa ya na kammala degree dinsa ya wuce china yo wani course game da koyon ƙera mota da babura da ya fara koya a nan shekara biyu ya yi ya gama iya komai har ma ya fi wanda suka koya masa ƙwarewa saboda Marzouq mutum ne mai kaifin basira .

a switzerland ya buɗe componyn ƙera ababen hawa wanda kafin kace me wajen ya haɓaka sai ya zama shi da nigeria sai dai ya ga iyayensa ya koma Domin Shima DR Nazir ya samu cigaba lokacin ya zama minister ilimi na ƙasa.

a lokacin idan ka kalli Hajara ba ka taɓa cewa ta taɓa shiga damuwa a baya ta zama hamshaƙiyar mace kyawunta da kwarjininta na ƙaruwa .

gefe guda ta na aikinta wanda zuwa lokacin tuni ta samu cigaba da matsayi babba a jahar ta kaduna dawowarsu abuja baisa ta bar aikinta ba domin lokacin Director ce guda a ministry of education da ke jahar ta Kaduna,

Sadeq ya yi Aure don ya riga su Aure dukda sun girmeshi Ashraf ma yana ta so ya yi amma ya ce shi sai tare da Marzouq zaiyi wanda sun sha faɗa da marzouq akan shi ya je ya yi aurensa shi mata ba sa gabansa amma sai ya ce bazaiyi ba saidai suyi tare .

itama mahaifiyarsa sai hankalinta ya karkata akan son ganin sunyi auren duba da yanda zamani ya lalace,Nan fa ake yinta domin Marzouq ba shi da budurwa bai taɓa kula duk ƴan matan da suke bibiyarsa ba Ya ce kawai Ummy ta zaɓa masa duk wacce ta mata zai amsa kasancewar Ummy ya ke ce mata hakan yasa kowa ya tashi da hakan har su Ashraf.

Kafin ya koma Switzerland Mahaifiyarsa ta haɗasa da Mariya a nan garin abuja a ta ke duba da yanayin ladabin yarinyar ƴar maƙotansu ce amma kullum sai ta zo gaishe ta wanda bata san saboda Marzouq ta ke hakan ba daman saboda tsananin son da ta ke masa a tunaninta hakan zai sa mahaifiyarsa ta haɗa su aure sai gashi Allah ya cika mata burinta.

koda mahaifiyarsa ta zo masa da batun ya amshe ta ba don ta kwanta masa a rai ba sai kawai don son ya cikawa mahaifiyarsa burinta sannan bayajin zai iya taɓa bijirewa umarninta har abada.

bayan duk bincike da akayi aka gano yarinyar bata da wata makusa ƴar wani ƙauye ce da ke jahar sokoto iyayenta ba su da ƙarfi suka kawo ta wajen ƴar uwar babanta matsayin riƙo tafi da aikatau.

ta sata ta yi boko da islamiya amma bakinta sakandire lokacin yarinya mai nutsuwa da kawaici lokacin ma ajara ma hajara ta san ba ƴar gidan ba ce .

ba ɓata lokaci aka sha shagalin bikinsu tare da Ashraf da budurwarsa Saudat da tun a switzerland suka haɗu a makaranta itakuma ƴar masu kuɗi ce anan Abuja bayan aure Marzouq ya koma da matarsa Switzerland saboda kasuwancinsa duk suna chan ba yabo ba fallasa a zaman su ya na nuna mata kulawa saboda yanda ta ke nuna masa soyayya dole ya haƙura ya amshe ta hannu biyu suka cigaba da rayuwa kamar ko wasu ma’aurata ,

Lokaci kaɗan Marzouq ya zama hamshaƙin attajiri da Ya yi suna A chan ƙasar da ma nan ƙasa nigeria domin ya gina katafaren componyn sayar da motoci a nan Abuja saida ya zama ya na da componynnykan Ababen hawa goma a ƙasashen duniya ya mallaki manyan gidaje da kadarori tare da jiragen sama guda biyu ana masa jigilar ƙasashen duniya ya zama attajiri wanda duk inda ka ce *MARZOUQ MALEK* a Ƙasar nan to fa ɗaiɗaiku ne ba su sansa ba musamman a fannin taimakon al’umma.

lokacin ne mahaifiyarsa ta buƙaci da ya dawo nigeria da zama ta na buƙatarsa a kusa da ita a katafaren gidan sa da ya gina ya sauka lokacin shekararsu biyar da aure ba haihuwa dukda yanda yake tsananin so da buƙatar haihuwar haka ya daure bai furta ba a bayan dawowarsa ne ya gina katafaren gidan marayun nan wanda lokacin ni ina ɗaya daga cikin amintacciyar mai aikin Hajiya Hajara hakan ya sa ta buƙaci da na dawo nan naci gaba da tayasa kula da yaran domin ta aminta da ni kuma duk labaran nan da nake baki ita ta bani su da bakinta,

na manta ban sanar miki ba Hajiya ta haifi ƴa ɗaya da Alhaji Nazir mai suna Rabi’atu ma’ana sunan mahaifiyar hajiya ana ce mata Lena wanda yanzu zakuyi sa’anni yarinyace da ta taso cikin gatan uwa da uba da yayyinta domin ko ƙuda basa so ya taɓa ta musamman Marzouq da ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata,kodan kasancewarta tilon ƴa mace a cikinsu hakan ya sa suke mata soyayya ta musamman suka ɗan sangarta ta da shagwaɓa.

Lokacin ne fa Mariya ta dawo da sabon salon raini ita matar attajiri magana ma daɗyal ta ke ga wulaƙanta na ƙasa da ita amma duk iskancinta batayiwa Hajiya Hajara domin duk hakurinta da kawaici to fa ba ta ɗaukar raini ko ƙadan sannan ta na da kwarjini,.

Suncika shekara takwas da Aure wanda zuwa lokacin Hankalin Hajara ya matuƙar tashi game da rashin haihuwar don lokacin sadeq yaransa ukku Ashraf na da biyu kuma ta na kula da yanda Marzouq ke ƙaunar yaran ta san na daga dalilin son yara ne ya ja shi ga ra’ayin buɗe gidan marayu a nan ne ta ke ba sa shawarar da ta na son ya ƙara aure ba tare da ta faɗa masa dalilinta na hakan ba,

Da farko ya shashantar da maganar wanda a ƙarshe ya amince amma akan ta nema masa kamar yanda ta nema masa a baya haka ko akayi Hajiya hajara tayi matuƙar bincike a wannan karon kafin ta nema masa ƴar gidan wata Aminiyarta Hajiya Bara’atu a nan Abuja gidan dattako da kamala.

Aishatou kallo ɗaya tayiwa Marzouq ta ga ya yi mugun tafiya da imanin ta shima kuma ba laifi yarinyar ta ɗanyi masa akayi aure bayan hauka da mariya ta sha ba irin haukan da batayi ba akan hakan a ƙarshe uwar riƙonta ta lallasheta lafin ta fara aiki da shawarar mugayen sabbin abokan da ta yi .

da farko Hajara ta so a raba musu gida ga mamakinsu na dawowar mariya daidai itace hada bada haƙuri akan borin da ta dingayi zaka ɗauka tubar gaskiya ta yi sai hankakinsu duk ya kwanta akan haɗa musu gida mariya ta danne kishi ta amshi Aishato hannu biyu to ita daman ba mai fitina ba ce hakan ya sa suka zauna lafiya wanda hakan ya kwantarwa da mijinsu da surukarsu hankali,

Watan Aishatou biyuu ta samu ciki farimciki a wajen Marzouq ba ya musaltuwa haka hajiya hajara har kukan farinciki saida ta yi cikin na da wata ukku ya zube sunyi matuƙar damuwa kafin a ƙarshe su barwa Allah akan ya basu wani me Amfani.

wasa wasa aishato ta ƙara samun ciki wata biyu ya zube wani ma kafin yakai wata guda ya zube a shekara biyu da aurensu da Marzouq Saida Ciki goma Sha Ɗaya ya zube a jikinta kuma duk wani bincike anyi babu wata matsala daga gare ta ko daga gareshi Ayshatou kullum cikin kuka ta ke mariya na tayata yanda ta ke nuna damuwa sai ka rantse har ranta hakan ya sa babu wanda ya sa zargi a kanta tunda likitoci sun tabbatar da zubewar cikin daga Allah ne babu wani alamun zubar dashi ake,

Ayshatou ta ɗauki wani cikin wanda mahaifiyarta ta sanyata ɓoyewa hakan ga kowa matsalar irin matan nan ne masu masifar laulayi wanda dole saida mariya ta gano cikin na da wata huɗu shima ta yi ɓarinsa wanda a nan ne jini ya ɓalle mata rai ya yi halinsa ta koma ga mahaliccinta,

Mutuwar tayi masifar girgiza Marzouq domin har ga Allah ya so Aishato domin macece mai tsananin tarbiya ga kulawa da nuna masa ƙauna ba ruwanta da dukiyarsa saɓanin mariya da take harin dukiyarsa ya zuba mata ido kamar baisan me ta ke ba sata kawai take masa ta na sayan kadarori.,

Hajiya hajara ma ta ji mutuwar Aishatou ana kwana ukku da rasuwar ne jin shiru mariya ba ta fito ba ta aika Lena akan ta kira mata Mariya ko lafiya ta na niyyar tura ƙofar kenan ta ji ta babbake da dariya tare da cewa.
Chapter 9 · 0% Book details