← Book details Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*

*Bismillahirrahmanir Rahem*

Ina Godiya ga Allah S W A da ya bani ikon farawa Lafiya Allah ya sa na gama lafiya ya hane hannuna da rubuta sab’o👏🏻

Saƙon gaisuwa ga dukkanin ɗaukakin masoyana Ina muku fatan Alkhairi da nasara a rayuwa Allah ya bar Ƙauna

*Ƙirƙirarren Labari*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*01*

*ABUJA ,GARKI G R A*

Kwance take saman ƙatoton Gadon baccinta ,
bacci ta ke cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ƙaram ringing wayarta ƙirar iphone 16promax ne ya tayar da ita harga Allah ba don baccin ya isheta ba ta miƙe zaune tare da Adduar tashi daga bacci Ta na ƴar gajerar miƙa domin har yanzu gajiyar dawowarta daga Japan shekaranjiya bai sake ta ba.

A hankali ta janyo wayar tare da ƙure number da ke kiran na ta da Kallo wanda true caller ya shaida mata mai kiran,wani ɗan naci ne da ya takura mata tun a Japan Ta rasa inda ma ya samu number ta,

B’acin rai ne ya bayyana ƙarara saman kyakyawar fuskar ta mai matsakaicin haske ,Fara ce ba sosai ba,Kwanciyar fatar ta da manyan idanunta shine farkon abunda zai d’auki hankalinka tattare da baiwar kyawun fuska da zubin zatin halitta da Allah S W A yayi mata ,

Kyakyawa ce ta yanda ka kalleta dole ka maimaita mata kallo ,

ta na da siririn hanci daidai da madaidaiciyar shape din fuskarta ,
sai bakinta ɗan madaidaici ba za ka kirashi ƙarami ba haka bazaka kirashi babba ba ,

ta na da manyan idanu masu d’auke da Zara-zaran gashi ga yalwataccen gashin giranta da ya k’ara k’awata kyawunta,

ya Allah ni na ma rasa gane da wata k’abila zan danganta wannan baiwar Allah da shi Ita ba Fulani ba ita ba balarabiya ba haka zalika ba india na ita ba buzuwa ba,
Kai tsaye dai tafi dacewa ka kirata da Shuwa Arab domin sak har kalar hasken fatarta irin na su ne banbancin ita haskenta bashi da d’au saidai ni a gaskiya kalar fatar ta ta ma ya fi burgeni domin ƙalilan ne ka samu masu irin ta kashi biyar cikin Dubu,

Ba tare da ta bari wayar ta gama ringing ba ta ja dogon tsaki cikin Tsananin ɓacin rai ta ciro barima d’ankunne da ke kunnan ta tare da ciro da sim ɗin daga jikin wayar tare da Karya sim d’in baki ɗaya,

Sosai mamaki ya kamani ganin yanda lokaci guda ta sauya tamkar wacce bata taɓa sanin Kalmar dariya ba ma,

Miƙewa ta yi ta na kallon agogo sosai ta yi mamakin har 5:30 lallai ta jima ta na baccin gajiya kasantuwar ta na fashin salla wanka kawai ta yi ta fito wanda take ɗakin ya Gauraye da daddaɗan k’amshin sabulullukan da tayi amfani da Su ,

turare kawai ta fesa ba tare da ta duba ko madubi ba ta kimtsa jikinta cikin Atamfa doguwar riga street gown d’inkin ya kamata kad’an sai sannan na k’arewa surar jikinta kallon doguwace mai madaidaicin jiki Allah ya Albarkaceta da albarkatun jiki daidai baiyi yawa ba haka zalika bai yi kaɗan ba.

Kallabin atamfar ta ɗaura simple ɗauri ta yi amma yanda yayi mata masifar kyau zaka ɗauka wacce zata tafi wani gagarumim biki ne irin yanda tayi masifar kyau a hakan ma wai ba make up fuskanta to inaga ta yi kwalliya,

Ihun da ta jiyo daga falo ne ya sanyata kallon ƙofa wanda Kafin ta yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi an banko kofar tare da shigowa da gudu sai Jin runguma tayi cike da tsantsar murna

ta ce “Fav sis irin zuwan shammata haka Wlh bansan sam da zuwan ki ba sai ɗazu Hajiya ke sanar da Momy ta fad’a mun dawowata daga school kuwa ko zama banyi ba direct na ce sai nazo na ga y’ar uwata ya Japan d’in”
Ta na sakin fuskarta daga murtukewar tare da sakin gajeran murmushi ta ce “Japan alhmdllh Sis Safa Irin k’iba haka kamar ba karatu kike ba “

Ta na sakin rumgumarta tare da kama hannunta Su na nufar k’ofar da zata sadasu da falo ta ce “To me zaisa na rame wannan ai sai ku masu hana ido bacci don karatu Alhudu-hudu yanzu dai sai a tsaya da karatun haka anyi tunda anyi Degree anyi masters anyi PHD ya isa haka kuma”

Ta gama faɗa daidai lokacin su na gama shiga k’aton falon da bashi da hayaniya kujeru ne saiti biyu masu kyau da taushi sai katuwar plasma sai Frames na hotuna mabanbanta a Zagaye da falon,

“Kema dai kin faɗa mata Gaskiya Safa yanzu kuma sai tazo ayi aure yawon gararambar ya isa haka”

Farar Tsohuwar da ke zaune da hijab da charbi a hannunta ta faɗa fuskarta babu wasa.
Turo baki gaba tayi tare da zama ta na ɓata rai batare da ta ce komai ba,

“Gaskiya Hajiya ta faɗa ai sis Ibti Wlh ya ci ki nutsu ki zaɓa duk Dubunnan masoyan nan naki ki darza ɗaya kawai mu sha biki kinsan da kowa daman jiran dawowarki yake ni dai har yanzu yayana nakewa fadanci wlh Ibtihal sosai yaya Yusuf yake kaunarki yara biyar Mahaifiyarsa na zab’a masa ya ce shi baya so duk saboda ke please ki auri yaya yusuf don Allah ibti wlh zai kula dake fiye da yanda bakya tunani zai mantar dake duk wata jarabawa da k’unci da damuwar da kika shiga a baya zai baki farinciki fiye,……!.
“Enough don Allah Safa kar ki ɓata mun rai daga zuwa na ,
“Na faɗa maki karki ƙara Kawomun zancen wani ɗa namiji ma bare har batun Soyayya na faɗa miki ina buk’atar abokin rayuwa ne?ko na ce miki ina buk’atar aure ne?karki ƙara zomin da maganar wata soyayya ai ni zan zauna a rayuwar auren to bazanyi ba anbi an sakamun ido da batun aure duka da wata nawa na girmeki ke an dameki ko Sajida da ta bani 7months da haihuwa an dame ta ko sai ni?“

Ta k’arasa fad’a cikin k’unar zuciya b’acin rai na bayyana k’arara a fuskarta,

Itama cikin fad’a Hajiya ta ce
“Aure Kam ya zama dole kiyi ko kina so ko bakya so ko don kinga na zuba miki ido Sajida da Safa da kike magana ke da su ai ba ɗaya ba ne ko sai na fito na miki dalla-dalla yanda zaki fahimta sannan suma ina sane da su duk zan gamu da iyayen naku ko don kunga duk na zuba muku ido sannanma ke wata irin kafirar zuciya ce da ke da abu ba ya wucewa to daman jira nake ki dawo daga karatun da Shi Bashir ɗin da ya goya miki bayan kike abunda kike so zan gamu da shi na baki wata guda a duk cikin masoyan nan da suke sonki ki zaɓa ɗaya idan ba haka ba ko na zaɓa miki da kaina don ni ba tsohuwar banza ba ce ba zan zauna Ina zuba miki ido kina gagaranba ba”

Wata harara Ibtihal ta bankawa Safa wanda saida dariya ta so subce mata ta narke fuska ta na haɗe hannayenta Alamun tayi hakuri ,

miƙewa fuu Ibtihal ta yi ta na nufar Bedroom tare da rufowa ta murza key ta na faɗawa saman gado rubda ciki tare da sakin kuka .

Sosai ta ke kuka ta na jin damuwa da ƙuncin da ke cikin zuciyarta har yanzu bai Kau ba ,

wani ƙududu take ji a cikin zuciyarta ba ta son maza ,bata k’aunar soyayya ba ta buk’atar Aure me ya sa dole sai maza sun bibiya rayuwarta me ya sa suke binta da kalmar soyayya me ya sa su Hajiya Su ke son dole sai tayi Aure alhalin ba ta buƙata ba ta son ko da jin kalmar ,

Saboda maza ta manta rabon da ta shafa ko da kwalli a fuskarta ballantana hoda duk da ƙaunarta da kwalliya tun yarinta haka ta haƙura shakera fin ukku kenan da rabonta da ta ce ta zauna ta yi kwalliya duk don kar ta burge maza har Su ce suna sonta amma duk da haka ba ta tsira ba ,

gashi yanzu daga dawowarta Hajiya za ta fara mata da batun aure wanda da tasan haka ne da komai zasuyi bazata dawo ba duk da a chan ɗin ma ba sha tayi da bibiyar samari ba amma dukda haka gwara chan tunda ba iyaye ballanta har Su tilastata da batun Auren”!

Knocking kofar ne ya sanyata tsagaita kukan ta na jin Safa na mata magiyar ta yi hakuri ta buɗe kofar tayi mata banza domin wani haushinta takeji don ba don ta kawo maganar yaya Yusuf ba gaban Hajiya ba da hajiya ba ta tuno da batun yanzu ba,

Gajiya da bugawar ya sanya Safa barin kofar tare da barin gidanma gaba ɗaya ta na jin zuciyarta ba daɗi da niyyar gobe za ta dawo ta ba ta hakuri,

Haka Ibtihal ta ƙarasa yinin ranar cikin k’unci da ciwon Kai sakamakon kukan da ta sha ko cin abinci daren ranar ba ta fito ba hajiya ta aiko ta bude ta ki buɗewa ta ce a kyaleta yunwar cikinta,

Sai wajen 12 bacci ya dauketa washegari ta tashi ba ciwon kai saidai da ka kalleta ka San ta ci kuka,ko da ta je gaishe da hajiya fuska babu walwala hajiya ta ce “kin gama murtuke-murtuken ki ba tsoronki zanji ba,

Da kanta ta fita ta had’a breakfast tun 7pm kasancewar Yau take son komawa Aiki domin tafi buk’atar fita dukda Sai ta so ta koma d’in amma haka kawai tafi bukatar barin gidan ba tare da ko hajiya sun sake Haɗuwa ba ta d’auki makullin motar ta Ash ƙirar Judgement Day 2016 saida ta biya ta yi register sabon layi kafin ta nufi UNIVERSITY OF ABUJA,GWANGWALADA.
Yanda ta ke tuƙin ma kaɗai ya isa ya matuƙar burgeka tayi matuƙar kyau da motar musamman yanda ta ke komai cikin aji kamun kai gami da nutsuwa da kallo ɗaya zakayi mata kasan ta haɗa dukkan waɗannan ɗin.
Chapter 1 · 0% Book details