← Book details Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To fa jikata kinji asalim Tarihin *MARZOUQ MALEK MARZOQ* ban ɓoye miki komai daga abunda na sani dangane da rayuwarsa ba jikata ban taɓa zaunawa na ba wani wannan labarin ba sai ke kema kawai don ina jinki ne tamkar jikata yanzu wannan ba abun a tausaya masa ba ne”
Mama salame ta ƙarasa faɗa ta na kallon Ibtihal”
Batayi mamaki ba ganin Hawaye a fuskar Ibtihal ta ɗanyi murmushin yaƙe tare da cewa “ai nasan kema dole ki zubar masa da hawaye Jikata domin duk wani mai imani yaji labarin Marzouq sai ya tausaya masa saidai muna masa fatan Nasara a gaba kamar yanda Mahaifiyarsa ta yi nasara bayan ƙalubalen rayuwar da ta fuskanta kala-kala a baya”
Ibtihal na sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayen da suka zubo mata ta kalli mama salame ta ce “tabbas akwai tausayawa a labarinsa ina masa Fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya haɗasa da mata ta gari a gaba sannan ya basa haihuwar da ya ke buri me Albarka”……………..✍🏽

https://chat.whatsapp.com/JYPWPtF78zlIr2kJcbp6ms?mode=gi_t

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*8*

Mama salame ta amsa da “Ameen jikata kema Allah ya yaye miki abunda ya ke damunki idan kina da aure ya ƙara miki zaman lafiya da mijinki tare da baku zuriya ta gari idan kuma baki da aure ya baki miji na gari”
Ibtihal ba ason ranta ta amsa da “amen ba saidai kawai ba daɗi mutum yayi mata addua ka ƙyalesa amma a ranta tasan ita ta gama aure har abada ta gwammace ta ƙare rayuwarta a haka,

Tayiwa mama salame alkhairi sosai sai ƙarfe 1:30 ta bar gidan marayun zuciyarta cike da tunanin labarin nan da mama salame ta bata har ta isa gida abun ya na ranta ,

Ga mamakinta duk yanda ta so ta manta da batun *MARZOUQ MALEK* hakan ya gagara bacci tazo yi amma hakan ya gagara tiryan-tiryan labaran suke dawo mata tamkar a film ta rumtse ido bacci ya ɗauke ta yafi a ƙirga amma hakan ya gagara,
sosai mamaki ya kamata akan meyasa labarin bawan Alllah nan ya tsaya mata a rai,
bacci bai ɗauke ta ba sai bayan Asuba shima bayan ta gama salla ta fara karatun alƙur’ani sai taji damuwarta ta ragu a haka ɓarawon bacci ya sace ta.

Ibtihal ba ta tashi ba sai ƙarfe sha biyu na rana ta ji daɗin ramuwar baccin da tayi dukda batayi tunanim zata kai haka ba,

Yinin ranar sukuku ta yini tamkar mara lafiya don sai azahar ta karya Hajiya na kula da ita sai ta ɗauka ƴan miskilancin ne suka tashi,

Daren ranar ma sosai ta dulmiya duniyar tunani ƙarfe sha biyu ta yi kwance ta na kallon POP donma sun jima suna waya da mom ta na ƙarfafa mata gwiwar akan kar ta damu game da shiga kotu insha Allah su ke da nasara don ganin yanda tayi sanyi kamar bata lafiya ta ɗauka duk damuwar shiga kotun ce.

Jin murza key tare da buɗe ƙofar ne ya sanyata zubawa ƙofar ido ta yi mamakin ganin yusuf sanye cikin kayan bacci da zallar mamaki ta miƙe zaune ta na rufe jikinta da blanket don kayan bacci ne jikinta hankali tashe ta ce.

“meye haka yaya yusuf ya kake abu kamar baka da hankali ƙarfe sha biyu ka shigo mun ɗaki a haka me kake nufi”

Ya na nufo gadon ta ƙara matsawa chan ƙarshen gado hawaye na zubowa daga idamunta ,

gadon ya zauna tare da cewa”Zaɓi na zo na baki Ranar Talata Abba zai dawo zai miki magana domin na faɗa masa mun riga mungama sasinta kanmu jiran dawowarsa kawai muke mu tsaida ranar aure don Allah idan ya tambayeki kar bakinmu ya banbanta idan ba haka ba hmmm”

ya gama faɗa ya na wani ciza lips
“Idan na ƙi faɗa masa hakan me ka isa kayi ko an faɗa maka tsoranka nake yaya yusuf kai bakasan kawaici ba to bazan faɗa hakan ba bazan aure ka ba ko ni kaɗai ce mace a duniya gasunan dayawa kaje ka auri wata mana ko dole sai ni”

Ransa na ɓaci a zafafe ya ce “Eh sai ke ke kaɗai kika rage mace a idanuna bazan auri kowa idan ba ke ba kuma ki ƙi faɗawa Abban ki ga abunda zan miki wlh sai na ja mana abun kunyar da dole sai an ɗaura mana Aure idan nayi miki ciki kika haihu ai magana ta ƙare tunda na kula kinfiso sai ta tsiya-tsiya zan mallakeki”

Yagama faɗa cike da masifa ,
Hawaye na zuba a idon Ibtihal ta ce “

“bazan aure ka ba sannan wlh baka isa kayi lalata dani ba kodan ka na ganin ina gidanku shiyasa duk wani iskancinka ya ke ƙarewa a kai na meyasa bakayiwa Safa haka ba ko don ita ta na gidan mahaifinta sannan meyasa bakace zakayiwa Sajida haka ba me ya sa sai ni watau ni ce marar galihu ko”

Ta ƙarasa faɗa ta na sanya kuka,Jikinsa ne gaba ɗaya yayi sanyi duƙursawa ya yi ya ce .

“kamar yanda nake da iko da nan gidan Mahaifina ne Ibtihal haka kema nan gidan mahaifinki Abba ya na sonki kamar yanda yake sonmu meyasa zakice haka wallahi soyayyarki ce tayimun kamun da bazan iya control ɗinta ba kinƙi ki gane Ibtihal ina sonki ina ƙaunarki bazan iya rasaki ba ke kuma kin kasa fahimta me yasa bazaki aure ni ba me ye aibuna me sauran maza suka fini da shi’?

Ya ƙarasa faɗa ya na nuna kansa”
Ibtihal batace da shi komai ba illah haɗe kanta da gwuiwa da ta yi ta na cigaba da kuka”

“Kiyi haƙuri My love kuka bai dace da kyakyawar fuskarki ba “

Cikin kuka ta ce “ka ficemum a ɗaki wlh ko nayi maka ihu sannan ka bani makulli na”

Ya na miƙewa ya ce “mu kwana lafiya”

Ya fice ba tare da ya bata makullin ba ta haɗe kai ta gwuiwa ta na cigaba da kuka ta kai 1:30 kafin ta lallaɓa ta yi alwala ta yi sallah ta na addu’ar Allah mata maganin wannan masifar ta yaya yusuf meyasa su maza gabaki ɗayansu matsala ne”

“Ya Allah ka ciremunsu daga rayuwata har abada”ta faɗa ta na hawaye itafa wallah muddin za a tilasta mata akan aure ta gwammace ta gudu tabar ƙasar ta tafiyarta ma ƙarin wani karatun ba tare da kowa ya sani ba.

Ranar Monday ta koma bakin Aiki lectures ta ke amma rabin hankalinta na a kotu da aka sanar mata a waya an shiga yanxu ,

Yanayin yanda take koyawar cikin zallar ƙwarewar turanci da kamewa kaɗai ya isa kasan yarinyar classic ce ajin ƙarshe sosai tayi kyau cikin shigar lafaya ta suturta jikinta cikin mutunci idanunta sanye da glass da yayi mugun ƙawata fuskarta.

Awa Ɗaya da rabi ta ɗauka ta na lectures kafin ta bar class ɗin ta na fita matasa suka hau cece kuce akan wannan kyakyawar budurwar fa gaskiya duk ta tafi da imaninsu ba mazan ba har matan domin tayi masifar burgesu ga kamewa ba ta dariya duk iskancinka ba ka isa ka kai mata wargi ba.,

Ba ta koma office ba kasantuwar ta na da metting da sauran malamai da shuwagabannin makaranta wanda a wajen metting ɗinma rabin hankalin wasu daga cikin mazan Shuwagabannin na a kanta wanda hakan ya sa ta ƙara kame kanta.

ƙarfe biyu ta samu kanta sallah ta gabatar a office ɗinta kafin ta ɗauki tarkacenta ta fice ta na nufar mota domin azumi take ba ta buƙatar komai.

Allah-Allah take ta je gidan aunty salma ta ji halin da ake ciki,

Sosai labarin da ta samu daga wajen aunty salma ya masifar kwantar mata da hankali domin karin farko sukayi nasara sa’annan kotu ta ci Sharef tarar kuɗaɗe na ɓata musu suna da yayi ƙarshe dai reshe ya juye da mujiya don daƙyal sharef ya kuɓuta bayan kotu ta kori ƙarar”

Hamdala Ibtihal ta yi ba iyaka domin bata taɓa tunanin lamarin zai zo da sauƙi haka ba a nan ta sha ruwa Safa na magiyar ta kwana ta ce “ba yau ba hakan ya sa ta yi fushi ta ce “itama bazata ƙara zuwa gidan Hajiya ta kwana ba”

Ibtihal ta yi murmushi ta ce”kinma Huce student ɗin Nile”

Ta na harararta tare da tura baki ta ce “to faɗamun magana sannu Malama”

Ibtihal ta ce faɗa ki ƙara ai da school ɗinku nake lecturing kuma class ɗinku da na sauke miki rawan kan nan naki don in ba da ƙatuwar hijab ba bazakiyi lectures ba sannan atteders ɗaya kika rasa kinsamu Carry over”

Safa ta kwashe da dariya ta ce “tab kinma isa ai bama zaki fara ba Ni da Besty Lena Kaɗai ma mun ishe ki don kullum saidai ki koma a Box tayar motarki zamu dinga sace miki”

Ibtihal zata kai mata danƙwashi ta ruga ta na dariya tare da mata gwalo ta ce “Bye ƴar ƙanwata “

Ibtihal ta shige mota ta na murmushi tare da tayarwa saida ta biya ta sayawa Hajiya Fruits kafin ta wuce gida.

Washe gari Abba ya dawo bayan magrib ya na ɓangaren Hajiya jin shiru baiga Ibtihal ba ya ce “Hajiya ya banji motsin ƴata ba “

Hajiya ta ce”wannan uwar zaman ɗakin ta na ciki na rasa ubanme ta aje a ɗakin yarinya ko hira ba ka isa ta zauna kuyi doguwa ta ita ba ta shige ɗaki kullum ta na gado ai ba ƙaramun kewar Marwan nayi ba don shine zai zauna kuyi hirar arziki da shi amma Waccen da yusufa ai basu da hali sam“

Abba ya yi murmushi ya ce “akwai gajiya ne har yanzu hajiya tattare da ita shiyasa”

Marwan da ke gefen Hajiya ya yi dariya ya ce “To hajiya ko dai mukaita ayi mata ruƙiya Kinsan mutanen Ɓoye suna haka”

Hajiya ta ce “Allah maka Albarka Marwan Nima abunda nake ta saƙawa a raina lamarin nata dole akwai mutanen ɓoye a ciki yanzu ka ganta mutum anjima wani abu daban”
Chapter 11 · 0% Book details