← Book details Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Hajiya to Abban fa baya nan “
Daƙuwa tayi mata tare da cewa”ja’ira to don baya nan bazakije ki gaishe da matar sa ba”
Ta na tura baki gaba ta ce “to hajiya saikace ke gaishe ki take zuwa tunda nazo banga ta shigo ta gaishe ki ba fa sai Abba na nan ta kafa munafurci da nuna tafi kowa sonki “
Hajiya ta ce “naji dai yanzu tashi kije ki gaisheta shikenan”
Ta miƙe ba har a son ranta ba ta fita Ta cikin part din na Hajiya bayan ta sanyo hijab ta bi wata ƙofa wacce ta sadata da wangamemen ɗayan part ɗin da kallo ɗaya sakayiwa ɓangare kasan mamallakinsa ya mallaki kuɗaɗe ,

Ko da ta shiga palo na farko ba kowa a na biyu ta samu hajiya Lubna baƙar dattijuwa sanye cikin shiga ta alfarma ba kyakyawa ba ce haka ba ta da muni suna haɗa ido ta yi kichin kichin da fuska saida ta ƙarasa har tsakiyar palon bayan sallama har sau biyu da tayi wanda daƙyal ta samu amsa zama tayi saman carpet tare da cewa “ina yini mama munsameku lfy”

A taƙaice ta ce”lfy”

Itadai Ibtihal ba ƙara cewa komai ba,

Hajiya Lubna na gyara zama ta ce ,

“yawwa gwara da Allah ya kawoki daman ina son maki kashe na ƙarshe akan ɗana wallahi tallahi ki fita sabgar ɗana idan ba haka ba zaki shiga mafi munin linkin matsalar da kika shiga a baya wancen nafila ne akan wanda zaki shiga gidan ɗana gwara tun wuri kisan abunda zaki Faɗawa Alhaji idan ya dawo don wallahi tallahi kika kuskura kika aurarmun ɗa hmmmm”

Ta gama faɗa ta na wani cixon yatsa”

Ba tare da IBTIHAL ta ba ta amsar komai ba ta miƙe tare da nufar ƙofa ta fice a binta Hajiya Lubna ta bita da kallo cike da jin haushin ta ta ce “Marar kunya fitsararriya watau ga mahaukaciya ma na magana baki da lokaci na”

Ba ƙaramin tsanar halin nan nata tayi ba na ta datsa mata maganganu tayi kamar ba da ita ta ke ba ta fice,.

Ibtihal da sauri ta bar part ɗin ta na komawa batare da maganganunta sun wani dame ta ba ta ja tsaki tare da cewa”ɗan nakin ma da kike bambami akansa ni me zanyi da shi mtwss “

Da yamma Aunty Salma tare da Safa suka zo a ɗaki aunty salma tayi mata duk wani bayani kamar yanda suka Tsara sun ɗauki lawyer sannan anyi musu takardar shaidar inda tayi ɓarin harma idan ta Kama Dr ya je ya bayar da shaida akan hakan”

Sosai taji sauƙin damuwarta amma dukda haka a firgice take daɗi ɗaya ta ji da ba zata halarta kotun ba saidai idan abun ya fi ƙarfinsu wanda ba sa fatan hakan so suke suyi abun cikin sirri batare da hajiya ko Abba Bashir sun fahimci halin da ake ciki ba”,

Safa ba ta bar gidan ba saboda daman akwai shaƙuwa me ƙarfi da abuta tsakaninsu dukda iyayin da Ibtihal ke mata akan ita fa yayartace.

Suna shirin bacci Ibtihal ta miƙe tare da Ɗaukar wayarta ta na shiga whats app ta iske missed call ɗin momy video call barkatai mutanen da take chat da su basufi 10 ba wanda sosai hakan ya ban mamaki kiran number momyn tayi Allah ya sa ta na online,

Ba jimawa wata kyakyawar farar matashiya ta bayyana mai matuƙar kama da Ita saɓanin Haske da momyn ta fita amma sak kamar anyi kaki saidai Ibtihal ta fi momyn kyau “hmmm Sai yanzu akaga daman kira hajiya Ibti”

Ta na narke murya ta ce”kiyi hakuri mom jiya zankira naga 10 yayi yau kuma na yi busy”

Ta ce”yayi kyau toh fatan kinji yanda mukayi da salma”

Ta jinjina mata kai”

Ta sakar mata murmushi har dimple ɗinta side na dama na lotsawa tare da cewa”

“inye shiyasa na ga an bar kuka”

Murmushi Ibtihal ta yi ta na rufe fuska tare da sakin murmushin da saida duka dimples ɗinta ƙwara biyu suka lotsa mom ta ce “ga mutuniyar ki lallasheta zanje na kula da mijina ya dawo”

Ibti ta turo baki ta na haɗe fuska itama mom ta bita da hararar wasa tare da miƙewa tabar wajen ta na nufar wani Ɗaki daga wayar na iya hango yanda ɗakin ya gaji da kayan wasan yara,

Daidai fuskar ta na bayyana Ibtihal ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ba ƙaramin kewarta tayi ba a cikin ranta amma a zahiri za ma ka ɗauka ba ta damu da ita ba ,

Wata Kyakkyar farar yarinya ce ta bayyana mai kimanin shekaru ukku ko da bata cika ba kaɗdan ne amma a zahiri zakace ta yi 5 years saboda girman jiki fara ce sol tamkar mom ga gashinta tamkar ba na yarinya ba saika rantse ba ta haɗa jini da hausawa ba saidai ita ba ta kama da mom da Ibti sosai sai waɗansu Abubuwansu da ta ɗauka,

Murmushi ibti ta yi ganin yanda ta tura mata baki ta na maida hankalinta kan ƙatuwar teddy da take wasa”
Cikeda lallashi ibtihal ta ce “wa ya taɓamun Afren ɗin momy na zanesa”

Ta na turo baki kamar bazatayi magana ba ta ce”is you”

Ta ɗan zaro ido alamun mamaki ta ce “to me nayi”

Ta na ƙara tura baki gaba ta ce “a lot of guilt”ta na langaɓe kai ta ce”to faɗamun laifin sai na baki haƙuri kinji princess ɗina”

Ta na gyara zama kamar wata babba ta re da fara nuna yatsa da hannu irin lissafin nan ta ce”First You haven't called me in four days And Second You said you would come and see me but You haven't come”

Ibtihal ta yi kalar tausayi tare da cewa
“Kiyi hakuri to”

Ta na sanya hawaye ta ce “I will not”

Safa na dariya ta amsa wayar tare da cewa “hy mummy’s princess “

Lokaci guda ta saki fuska ta na dariya ganin Safa ta bayyana a screen din wayar saboda kullum sai sunyi video call akwai shaƙuwa me ƙarfi tattare da su Ibtihal miƙewa tayi tare da nufar pridge ta na ɗaukar gorar ruwa me sanyi ta na kafa kai ta ce “kin fansheni rigimar Afren ina zan iya “

Safa na harararta ta gefe ƙasa-ƙasa yanda Afren bazataji ba ta ce”Kin saɓa mata alƙawari ba dole ta tuhumeki ba”

Sun kusan 50minutes suna wayar cikin harshen turanci kafin momy ta zo suyi sallama ta ce lokacin baccinsu ya yi sukayi sallama Ibtihal na kallon Safa ta ce ,

kun nace sai kun mayar da yarinya baturiya sarai tanajin hausar fa ta iya take ƙin yi wai ita yaren baya mata daɗi kiji fa wani rainin hankalin shiyasa ba na biyeta nake mata hausa kuma da kuna mata da dole zata so yaren ni ina mamakin mom da ta ƙyale ta “

Safa tayi ƴar dariya tare da cewa “mu abunda take so shi muke so yarinya ce idan ta girma zata daina in banda wayau ma da Allah ya bata wasu kamar ita bakowace magana suka iya ba shekara biyu da wata tara “

Ibtihal ta taɓe baki ta ce “kudai kuka sani ni dai amma dai ba two days ɗin da kika saba kiyi ki tafi ba zakiyi “

Safa na amsa wayar boy friend ɗinta ta ce “da kika samu ma zanyi two days ɗin ke ko kwana ɗaya daƙyal kike”

Ta ƙyaleta batare da ta amsa mata ba sai ma kwanciya da tayi tare da fara karanto adduo’in bacci.

Kwanan safa Biyu ta tafi ba a son ran Ibti ba don ta na matuƙar jin daɗin idan suna tare da safa ko ba komai za ta sata magana don safa ba dai son zance ba da kawo labari”

Washegari kasancewar ta na son yin safko kasancewar friday kuma ta na son ta yi sauko domin ziyartar gidan marayu kamar yanda tun wancen lokacin ɗan zaman da tayi a abuja ta sabarwa kanta xuwa duk friday sosai tayi missing yaran da tayi mugun sabo da su a wajen”

Washegari 8:30 ta gama shirinta sosai tayi kyau cikin shigar Doguwar riga Abaya mai matuƙar tsada ta amsheta tayi mata masifar kyau musamman yanda ta yi roalling gyalen kasan ƙwararriya ce a fanni saka irin kayan”

A gaggauce ta yi sallama da hajiya tare da fita ta na shiga motarta wanda mai gadi na hango hakan ya gaggauta buɗe mata get daidai motar Yusuf na fitowa ga alamun shikuma office zaije horn yayi mata da ƙarfi wanda tasan idan yayi mata haka alamun ta tsaya ne ya zo ya ɓata mata lokaci a cewarta hakan yasa ta murza motar da masifar gudu ,

hakan ba ƙaramin baƙanta ran yusuf ya yi ƙwafa ya yi tare da cize yatsa ya ce “zanyi maganinki marar kunya “

shima ya figi motar a mugun guje fiye da yanda ta yi.

Ƙarfe 9:30 ya yi mata a bakin gate ƙatoton gidan marayu da ya haɗu matuƙar haɗuwa don bazaka taɓa Ɗauka ma gidan marayu ba ne lura da yanayin tsarin ginin da yayi matuƙar haɗuwa ,

Tun a get ɗin farko securityn da ke gadin wajen suka shaida ta suka gaisa cikin mutunci kafin ta nufi gate na gaba ta na parking tare da fito da ƙatuwar ledar da ta biya shopping ta yo hakan ne ma ya sa har ta yi 1hour a hanya,

yara ne a farfajiya mafi yawaici duk uniform na makaranta jikinsu masu kyau da tsada cikin tsabta domin dukkaninsu kayansu ma har da guga bayan wanki,

sai wasa suke alamun kamar break suka fito tsayawa tayi ta na kallonsu cike da jin daɗin ganin yanda suke walwala da kulawa tamkar yaran da suke da gatan uwa da uwa tabbas ko wasu masu gatan bazasu sami gatan da yaran nan suke samu ba,

kafin ma ta ƙarasa wata yarinya da gudu ta rugo tare da rungumeta wanda hakan yasa sauran yaran hankalinsu dawowa gareta wanda kusan yara goma sha suka rugo da gudu har rigen-rigen rungumarta da zallar murnarsu na ganinta wacce ta fara rungumarta ce ta sanya kuka tare da ƙara rungumeta ta ce ,
Chapter 4 · 0% Book details