← Book details Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Ibtihal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy ta ce “Ayi Haƙuri yallaɓai a barsa haka “
Kafin ta maida kallonta ga Ashraf ta ce “ina yaran”

Ransa kamar an aiko masa da saƙon mutuwa ya ce”Su na tare da Dadynsu sun rakasa Asibiti Ziyara”

Ummy ta ce “to daga dawowa ƙasar ko hutawa baiyi ba Allah ya dawo da su lafiya na so tare ma zamuyi tafiyar da yaran to makaranta ita kuma Zenat ta na fama da laulayi saidai gaba idan Cikin nata ya yi ƙwari itama suntafi kartaga wannan karin an tafi da ƴar uwarta kaɗai nayi mata bayani anjima ta shigo insha Allah”

Shidai Ashraf bai ce komai ba amma har yanzu ransa ɓace ya ke ya na zaune saudat ta shigo da ƙatuwar akwati ya ɓalla mata harara ta turo masa baki ta na miƙawa Abba Passport ɗin ya amsa tare da cewa”shige ciki abinki ki zaɓi Ɗakin da duk ya yi miki a dafa miki abinda kike so ki samu bacci ki huta Allah miki Albarka”

Ta amsa da “Ameen Abbanmu”

Ta na nufar ciki da sauri ta na murmushi,

Ummy ta yi murmushi ta na girgiza kai ta san don ya ƙara ƙular da Ashraf ya ke haka Wanda ko zuciyar Ashraf ɗin kamar ta fashe don haushi ciki-ciki ya yi musu sallama ya fice”

Lokacin wata kyakyawar farar budurwa mai matuƙar kama da ummy ke saukowa daga stairs Ɗin bene kai tsaye wajen Dad ta nufa ya na wara mata hannu da murmushi a fuskarsa ta ƙarasa ta na ƙarasawa tare da basa hug ya ce”I really miss you Auta na since yesterday at 9 pm rabon da na saki ido na”

Ta na sakin rungumar tare da zama gefensa ta na kama hannunsa duka biyu ta ce “i miss you too Abba yau tun asuba akace ka fita kuma na tafi school sai yamma na dawo Abba gobe ina son zanje Hospital gaishe da marar lafiya daga scool”

Da damuwa a fuskarsa ya ce “waye ba lafiya”

Ta ce “Abba ka tuna Besty Safa Aminiyata “
Ya ce “eh waye bai san Safa Aminiyar Auta ba a gidan nan”

Ta ce “To Cousin sister ɗin ta ce Ba ta da lafiya kwana biyu ba ta zuwa school shine jiya ta ke sanarmun jinya suke a asibiti Cousin ɗinta ba ta lafiya shi ne ɗazu na kira na ji ya me jikin na ji ta na kuka wai kwana ukku ba ta farfaɗo ba Abba karkaga yanda safa ke son sister ɗin nata ko ni ta na yawan yimun hirarta ban taɓa ganinta ba amma Abba na tausaya mata shiyasa zanje na duba ta gobe”

Abba ya ce “Ya Allah ya Bata Lafiya ohh nima koda bansanta ba na tausaya mata Allah bata lafiya to amma me ya sameta har kwana ukku ba ta farka ba”

Ta na ƙara narke Fuska ta ce “nima bansani ba Abba “

Ya ce “to Allah ba ta lafiya”

Ta amsa da “Amen “

Ummy ta kalla da ta tashi ta na miƙowa Abba abun sha ta ce “Ummy bakice komai ba”

Ta ce”Allah ya bata lafiya Auta ai ya kamata kije ki kwanta da wuri tunda kince tun 7:30 kike da C A”

Ta na shagwaɓe fuska ta ce “Nidai Ummy sai yaya yazo tun da akace ya dawo Ƙasar ban gansa ba”
Ummy ta ce “to Allah sa yadawo da wuri”

Ta ce “amen ta na juyawa sun cigaga da hira da Abba,

Minti talatin saiga Sallamar marzouq tare da Ahmad da ke goye da Tasnem da tagaji da kukan bayan sun biya ya kai su shan ice cream a hanya ta yi bacci”

Da sauri Lena ta ruga da gudu ta na rungume sa ta ce “Missing you alot yayana “
Ya na shafa kanta ya ce “Miss You too Autan Abba “

Ummy na kallon Ahmad ya ce “itafa wannan na ga fuskarta duk hawaye ta yi bacci haka”

Ya na tura baki ya ce”Ummy daga fa mun raka Daddy duba marasa lafiya shine ta haɗu da wata yarinya age mate ɗinta suka dinga wasa wai da zamu taho ta dinga kuka ita saidai a bar ta a chan “

Ummy na amshe ta ta ce “Allahsrk Tasnem akwai son ƴa mace ko dan ta ga ita kaɗai ce mace a yaran ba ri na miƙata wajen mamanta kafin ta kalli Lena da duk ta maƙalƙale Yayanta daƙyal ma ta ƙyalesa suka gaisa da Abba ta ce “ba surutun banzan zaki zauna kina masa ba ki kai masa abinci part ɗinsa tare da Fruit salad ɗin Da na haɗa masa mu kwana lafiya”

Ta na barin wajen Marzouq ya ɗanyi murmushi ya san har yanzu ummy fushi ta ke dashi akan maganar aure da tayi masa kafin ya bar ƙasar a ransa ya ce”za ma ki sauko ummy amma aure kam ni da shi har Abada”

Lena ta miƙe ta ce “muje yaya na kai maka sai ka cinye tas a gabana kafin na ƙyaleka”

Abba ya ce”idan ya ƙi cinyewa kiyi masa ɗure Autana”

Marzouq ya yi murmushi ya na sallama da Abba ya fice Lena ta bi bayansa da Warmers ta na ta masa surutu ya ƙyaleta don ba ya iyawa da surutun Lena yau agajiye ya ke,

Tsarin part ɗinsama kaɗai abun kallo ne domin wasu ƙasaitattun kujeru da carpet tare da labulaye sai Frames da lamps da centre table da ƙatuwar plasma wacce ni tsawon rayuwata ma bantaɓa ga irin ta ba ,Part ya matuƙar haɗuwa da ƙayatuwa,

saida Lena ta tabbatar ya ƙoshi kafin ta ƙyalesa shima don gyangyaɗi da ta fara ta na miƙewa ta ce “yaya saida Safe Gobe da safe daga school zanje hospital duba cousin ɗin ƙawata”

Ya na miƙewa tare da shigewa bedroom ɗinsa ya ce”Allah ya kaimu”

Wanka ya yi bayan ya sauya kaya ya na Feffeshe jikinsa da mabanbanta Turaruka Ya kwanta domin akwai gajiya tattare da shi ya na buƙatar hutu Ga mamakinsa Yarinyar da ke kwance gadon asibitin maƙale da na’urori take masa gizau Da ya rumtse ido sai ya ganta lokacin da ya je dubata “

“Me hakan ke nufi”?

“Tausayi”?!

Wata zuciyar ta ba sa amsa ,

“Ciwon Zuciya “Maganganganun Sanata Bashir Dikko game da ciwon nata ya ji suna masa gizau a kunne ,
“Me zai haɗa yarinya ƙarama da larurar Ciwon zuciya”?
Me ya haifar mata da ciwon meye Sila “
Sanin bashi da mai bashi amsa ya sanya wa zuciyarsa ƙoƙarin sharar da batun
Ya kai 30minutes kafin wani bacci mai cike da gajiya ya kwashe sa cike da mafarkai Kala-kala,

Kamar yanda ya saba bayan sallar asuba Al-Qur’an ya ke ta karantawa har gari yayi haske kafin ya yi shirin fita exercise a 30minutes ya yi ya dawo kafin ya yi wanka ya shirya cikin wani blueblack yadi da yayi masifar masa kyau sai baza ƙamshi ya ke,
Kallon agogon dake maƙale a hannunsa ya kalla ya ga 8:30 sashen iyayensa ya fita lokacin Abba na shirin fita suka gaisa kafin ya ƙarasa ya na jiran ummy tadawo daga raka Abba,
Ya na zauna ya na latsa waya har ummy ta dawo ya ɗago ya kalleta ta haɗe fuska cike da ladabi ya ce “ina kwana Ummy antashi lfy”
Ta na zama ta ce”lfyqlau ya gajiya “ya ce “Alhamdulillah”
Ta ce”masha Allah”
Daga nan duk sukayi shiru a hankali ya ke satar kallon Ummy kamar bazatayi magana ba sai chan ta dubesa fuska ba wasa ta ce “Kai yanzu haka zakayi ta Zama Marzouq babu aure hakan da ka zaɓa ka na ganin shi zai fishsheka “?

Cike da ladabi ya ce “Kiyi haƙuri Ummy matan ne sam basa burgeni sannan har yanzu bansamu wacce nake ganin zan iya aura ba amma na baki zaɓi kamar yanda kika zaɓamun a baya a wannan karin ma ni mai yimiki biyayya ne”

Ta katse sa da cewa “Har Abada Na gama maka zaɓin mata Marzouq ina fatan Allah ya haɗaka da zaɓin ka ba zaɓi na ba Allah ya maka Albarka ya azurtaka da mata tagari tare da zuriya mai Albarka”

Ya amsa da Ameen tare da cewa “Banji Motsin Auta ba”

Ta ce “ba ta jima da fita ba wai zata biya school ta yi C a kafin ta wuce dubiya Asibiti”
Ya ce “Allah dawo da ita lafiya Ummy ni zan wuce Majalissa”

Ta miƙe tare da cewa “Allah ya bada sa’a ya baka Halal mai Albarka ya haneka da cin Haram”

Ya amsa da” Amen Ummy na”

sukayi sallama ya na fitowa cikin sauri security suka nufa tsadaddiyar motar sa ƙirar Marcedes-Maybach Exelero da ta haura 1B wanda shine mutum na farko da ya mallaka motar daga shigowarta a Ƙasa Nigeria,
suna buɗe masa tare da gaishe sa cike da girmamawa ya amsa a Kame ya na shiga baya aka rufe masa driver ya shiga ya ja motar inda ta gaba Security ne haka ta baya ma suka tada motar suka bar wajen Ya ciro jarida ya na fara karantawa har yanzu Yarinyar Faɗo masa ta ke a rai tabbas Abar tausayawa ce lokaci guda ya ji ya kwaɗaitu da son sanin Labarin halin da ya jefata a wannan ciwon mai hatsari”?

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*11*
Chapter 15 · 0% Book details