Sashe 9
Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye take cikin dakin tana shiryawa cikin atamfa,kayan kwalliyane baje a gabanta tana makeup,zahara dake zaube tana miqo mata abubuwan da take buqata,dakin ya bade da qamshi kai kace barin turare akayi,ba abinda kakeji sai hira da shewarsu,a haka kakar rufaida hajiya kaka tashigo dakin.
Cikin mamaki take duban rufaida daketa zuba baki rai rai batama lura da shigowarta ba
"Ke aku,samu waje ki zauna" sai a sannan ta waiwayo,ta dakata daga saka dan kunnen da takeyi tace
"Kefa tsohuwarnan kin iya takura wlh" tafadi tana samun waje ta zauna kamar yadda hajita kaka ta buqata,saita itama tasamu waje tazauna tana dubanta
"Duk fitsarar da kike da rawar qafar da kike ina lura dake,to bari na gaya miki gaskiya idanma uwarki bata gaya miki ba,wannan mu a wajenmu abun kunyane aga amarya tana haka,don haka ki kama kanki karkice zaki shiga cikin matansa kina musu wannan rawar kan,idan kikai hakan kai tsaye za'ace ba daga gidan tarbiyya kika fito ba" dariya rufaida ta bushe da ita ita da sauran qawayenta na makaranta dake dakin masu irin tunaninta
"To hajiya yanzu so kike naje nayi ta sussunne kai ina abu kamar banje makaranta ba ko kuwa yaya?,nifa auren soyayya mukayi da mijina,kuma babu wadda zanwa biyayya tunda yadda suke matanshi haka nake,haba hajiya nafa fisu da komai,idan ba'a bini ba ai kuwa bi ba'ace nabi mutum ba" ta fada tana juya idanu,sai hajiya ta kama baki ciki mamaki
"Ni tarasulu,ke rufaida akul ki shiga hankalinki,mu idan muka aurarwa mace miji kunyarta mukeji,mukan jima bama iyama hada idanu da ita saboda abune me nauyi da girma,hakanan abokiyar zamana harta rasu ke har yanzu da nake miki maganar nan ban iya fadar sunanta yaya nake ce mata,haka itama bata taba batamin raiba ko sau daya,suna na kuwa nima ban tabaji ta fada ba,saida nayi haihuwar fari take kirana da sunan dana" sake kwashewa tayi da dariya har suna tafawa da zahra
"In gaya miki gaskiya hajiya?,wallahi bazan iya wannan rayuwar ba,banma tanadeta ba ko a mafarki,kishiyar zan shiga ina kwantarwa dakai ina yiwa biyayya?,bayan nasan cewa na fita da komai?,ai tsakanina da ita kawai shine nasaita mata hanya ta bani waje na sarara nida mijina,matan nashi gidadawa kada ma uwar gidan taji labari" da yatsa hajja ta nunata
"Ke wallahi ki kiyayi kanki,mu dukka din nan da kukewa kallon gidadawa da haka muka fiku iya riqe miji,me bokon taku ta tsinana muku banda tabarbarewa lalacewa da rashin iya zaman aure?,iyee ki gayamin?" Shuru dukka sukayi saidai rufaida tasan halin mutuniyarta,saita hau lallabata
"Aikin banza aikin wofi,duk bokon da kuke haryau sunqi karanta muku iya zama da miji da kishiya lafiya lau,kunawa aure kallon abu mai sauqi,bayan bakusan cewa *HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BA* ne"
"Kiyi haquri hajja nima tsokanarki kawai nake,zauna ki gayamin ina saurarenki" ta fada don kada hajjan ta ballo mata ruwa,ita ta haifi babanta tasan kuwa yanzu idan zance yashiga kunnensa sai ya bata mata ranta,fur hajjan taqi zama tace taje tagwada bokon tata.
Dariya sosai ta dingayi suna tayata sanda hajiyan tafita,haka tajuya taci gaba da diban kwalliyarta.
Lullube amarya rufaida take cikin shigar atamfa da yalwataccen mayafi kamar yadda akasan kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mamanta wadda rafito da ita daga dakin mamarta zuwa dakin dakin da dangin ubanta suke don yi mata fada,qasa qasa tace da zahra dake kusa da ita
"Ke nifa na gaji da wannan qabli da ba'adin nasu,wai meye baka sani bane a auren nan da aketa damunka?,kwanciyar aurece kawai fa ta rage,kosu wlh saina koya musu wani abun,amma sun dameka da zantattuka wani sai haquri sai haquri suke cewa kamar ance musu anmin mutuwa" dariya zahra ta kwashe da ita cikin qunshe bakinta kana tace
"Salon bata lokacine kawai da al'adar da suka daukaketa,kedai kawai ki bisu a haka suyi su gama mu qara wuta" da wannan zancan aka qarasa dakin,sun mata nasiha daidai gwargwado,wanda wajen rufaida kallonta take a matsayin ita da babu duk daya,ta kunnen data shiga haka take fita ta dayan,har suka gama aka tattaro aka fito da ita don danganata da gidanta.👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA*👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*
*Haske Writers asso*💡
*BABI NA BAKWAI*
"Allah ya kawo mu gidan gimbiya rufaida,lokaci yayi,gamu gidan rufaida,mata mai cikakken iko a gidan jibrila" wata zabiya dake cikin tawagar amarya taketa faman fada tana sake nanawatawa,gami da hadawa da guda mai shiga tsakar ka,su kansu wasu daga cikin 'yan uwan amaryan basusan wace ita ba,suna dai biye ne,har suka wuce farfajiyar gidan zuwa babban tsakar gidan,wanda ke dauke da varender da dakuna manya a jere.
"Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" mmn amir take maimaitawa sanda takejin wata faduwar gaba da fargaba na saukar mata
"Uhummm,sun iso kenan" daya daga cikin matan qannenta ta fada
"Da alama" samira ta fada tana dawowa kusa da mmn amir din,qoqarin kauda duk wani surutun masu shigowa da amaryar take daga kunnuwanra,da kauda duk wani furuci da zaya iya fitowa daga bakinsu.
"Na shiga uku,hafsa sun kawota,wallahi gasunan" mmn ummi ta fada tana dora hannuwanta saman ka,hawaye yana balle mata,da sauri hafsan ta sauke mata hannun tana cewa
"Haba don Allah mana maryam,ki nutsu,a haka kikeso su shigo su taddaki?,haba don Allah" hafsan ta fada tana sauke mata hannun data dora din aka,jamila tamiqo mata mayafinta tace ta yafa,don wala'alla suce zasu shigo da ita nan din.
"Ku fara shiga da ita dakin uwar gidan" yayar maman rufaida ta fada sanda taga suna yunqurin shiga da ita dakinta,wani takaici yacika rufaidan,taji kaman ta dakatar dasu,saidai ba yadda ta iya haka tanaji tana gani aka sauya akalarta zuwa dakin mmn amir.
A mutunce suka amshesu,sannan suka gabatar da itawa mmn amir din gamida danqa amanarta a hannunta kamar yadda al'ada ta tanada,cikin matuqar dakiya da nuna juriya mmn amir tace
"Toh,amana abune mai nauyi,amma duk da haka muna fata da addu'ar Allah S W T yabamu ikon riqewa,yashige mana gaba ya kauda fitina" dukka suka amsa da amin cikin yabawa da halayyar mmn amir din.
Ta cikin mayafin rufaida ke tabe baki sanda mmn amir din ke karanto addu'o'i suna amsawa,qaramin tsaki taja qasa qasa cikin ranta sannan ta furta
"Bagidajiya,kawai zata batawa mutane lokaci" sai data kammala suka shafa sannan suka miqe da ita suka fice zuwa dakin mmn ummi,har cikin zuciyarta taji sanyi na sauka sanda take shafa addu'ar,ta saki sassanyar ajiyar zuciya gami da sake maida kanta cikin sabgogi ta hanyar sallama da maqotanta wadanda suka soma haramar komawa gida ganin an kawo amarya.
Idanunta qir a kansu sanda suke shigowa dakin nata,baqiqqirin take ganinsu,kallon da take musu tamkar ganin abokan gaba ne a sansanin yaqi.
Wani irin tafasa zuciyarta take,kaman ta tashi ta koresu,amma dole tazauna tanaci gaba da dubansu,saboda maganar da jamila tayi mata tun kafin su shigo.
Yadda sukayi bayani dakin mmn amir haka sukayi mata,zuciya ta ciyota,taga zallar rainun wayonsu,ita za'a baiwa wani amanar kishiya?,duk yadda taso ta danne tayi shuru saita kasa
"Dacan baku bata tarbiyyar zaman gidan miji ba da bazata iya ba har sai kun bada amanarta?" Da mamaki suke kallonta,idanunta qyar akansu tana jiran wata ta tanka musu,ware idanu rufaida dake cikin mayafi take,inama daga ita sai ita tafadi wannan maganar,lallai wannan matar saita gane kurentq,dama tana sane da ita sarai,bata manta daduk wani cin fuska data mata ba kafin shigowarta gidan ,ta kuma ci alwashi ta lashi takobi saita rama,saita bada mata yaji a rayuwarta mai radadi
"Ikon Allah,to adai dinga haquri" yayar umman tata ta fada,sai duka suka miqe tare da rufaidan don barin dakin
"Da ba'a haquri ai da ba'a kai yawar haka ba,da bata shigo bama" ta fada ranta na mata zafi.
Dubanta jamila tayi bayan sun fice
"Gaskiya baki kyauta ba mmn ummi,abu na 'yan mintina ki barsu suyi su gama su fita shine kika kasa shuru,nikam gida zan wuce" ta fada tana miqewa ta dauki jakarta ta rataya
"Madalla,Allah ya raka taki gona,tunda na taba qanwar umma uwarmu" bata tanka taba tafice a dakin,ta leqa dakin mmn amir da tuni baqinta suka yoye saura 'yan qalilan suma daketa hada karonsu zasu wuce,sai qanwarta salima da zata kwana gidan donta tayata hidimar gobe ta gidan.
Zuwa awa daya gidan ya yoye babu kowa,hatta da amarya sai ita kadai,don qawayen nata duka angon yasa an kwashesu an maidasu gida,don yace bazaiyi wani siyan baki ba,saboda yana bala'in jin nauyi da kunyar mmn amir,bazai iya tsayawa yayita wannan yarintar ba da qawayen amarya ana jinsu,duk da hakan bai yiwa rufaida ba,amma haka ta haqura suka tafi suka barta.
Dukka yaran mmn amir ta sanyasu suka canza kayansu,salima ta gyara musu wajen da zasu kwanta tasaka su sukaje suka kwanta,hatta dasu usman basu kalli qofar dakin mamansu ba,don sunsan qarshen zancan wala'alla kafin bacci ya daukesu sai sunci na jaki.
Dai dai lokacin da amarya rufaida take kewaye dakinta tana dubawa,ba laifi komai yayi mata yadda takeso,duk da tasan cewa data yarda bbn amir din ya raba musu gida to dakin nata sai yafi haka,saidai sam ita bata da sha'awar wani raba gida,tafi sha'awar a hadesun yadda zataji dadin nuna musu cewa ruwa na sa'an kwando bane,wannan ma hakan ya mata.
Babban falo ne mai hade da bedroom,sai wajen dining wanda kusa dashi kuma qofar toilet ne,duk da ita kitchen taso a mata a wajen,duka sauran falukan matan nashima haka yake,gini ne mai kyau wanda yasha tiles da fentin mai kala biyu,kalar da kowacce cikinsu ita tazaba da kanta.
Tana zaune tun dazun inda take,ba inda ta motsa,jikinta gaba daya ya mata nauyi,ga wani ciwon dako ina na jikinta ke mata,hakanan zuciyarta sam babu wani sauran karsashi ko qwarin gwiwa tattare da ita.
A haka taji shigowar baban amir din gidan,tanason ta tashi tabar falon amma ta kasa,a haka harya shigo gidan,sai daya tabbatar ya kulle ko ina sannan yashigo tsakar gidan bakinsa dauke da sallama,shuru tsakar gidan yake,saidai a kacame yake,ko baqone kai zaka tabbatar cewa lallai anyi wani sha'anine cikin gidan.
Idanunsa kan qofar dakin rufaida,wanda yake tarwai da haske kamar yadda dakin mmn ummi yake,sabanin dakin mmn amir da nata hasken baikai nasu ba,da alama ta rage qwayayen dakin nata.