← Book details Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 20

Sashe 12

Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dataji tashin motarsa ta tabbatar yafita sannan tadawo falon,yaran suna zaune suna kallo,ya sauya musu tasha zuwa mbc,cikin tsuke fuska ta dubesu
"Kai....ku tashi maza ku tafi dakin babarku ku kalla" ba musu suka miqe daya nabin daya suka fice,ta sauke labulenta sannan ta maida qofarta tarufe,tadawo tayi kwanciyarta bayan tasauya tasha tana kada qafa,haushin yaran yana cikata,haka kawai su zasu soma zame mata qarfen qafa babu gaira babu dalili?.

Zaune ya sameta cikin reception na asibitin,akwai fresh yo a hannunta me sanyi tana sha kadan kadan saboda wata sabuwar yunwa data taso mata kamar bataci komai ba kafin tafito.

Daura da ita yazauna yana mata sannu,sannan ya mashi dukka takardun gwaje gwajen
"Nan cikin asibiti za'ayi ko a wajene?" Ya fada yana dubanta,duk da fafur taqi dubanshi kai tsaye
"Sunce duk wanda yafi"
"Zauna anan naje lab din na tambaya wanne ne yafi saurin amsar result" daga haka yawuce xuwa lab na asibitin.

Bai jima ba yadawo
"Muje suyi mikin,sunce duka daya ne" daga haka suka wuce,tana gaba yana biye da ita a baya,da alama cikin yasoma mata nauyi sosai fiye da baya,don d'ai d'ai take daga qafarta har suka isa.

Ko lokacin gwajin ma yana tsaye bisa kanta,yana janta da hira lokaci lokaci,saidai duka bata fiya bashi wata cikakkiyar amsa ba,hakanan takejin haushi haushinsa,bakinta kuma takeji ya mata nauyi kamar me ciwon baki.

Basu bar asibitin ba saidaya tsaya aka kammala komai suka miqawa likitan,ya duba duka sakamakon sannan yadaga kai ya dubesu.

"Ba wata matsala bace mai yawa yadda na zata alhmdlh,saidai duk da haka tana buqatar hutu da kuma ci gaba dacin abubuwa masu gina jiki,jininta yahau kadan amma wannan ba matsala bace in sha Allahu,taci gaba dashan magungunanta"
"Toh likita,in sha Allahu" ya miqa masa hannu sukayi musabaha yana mishi godiya suka fito.

Da kansa yabude mata motar gidan gaba tashiga sannan ya zagaya shima yashiga nashi bangaren,ya tada motar suka fice daga asibitin.

Har suka hau kan kwalta sosai batace dashi uffan ba,sai daga bisani yadan dubeta kadan sannan yace
"Meye damuwarki?,me kike da buqata?" Itama duban nashi tayi kadan sannan ta dauke kai tana mamakin ma'anar tambayarsa da maqasudinta
"Babu komai" kawai tace dashi,numfashi ya aje
"Duka cikin amir da yake na fari,hanifa ahmad da rabi'a duka ba wanda jininki yahau sai wannan?" Sake dubanshi tayi kana tadauke kai
"Kowanne ciki da irinsa,hakanan ba lallai mace tayita samun yanayin cikkunanta yazana iri daya ba" sai yayi shuru duk da bai gasgata maganarta ba,zuciyarshi tana bashi kawai shine sila,hakanan yakejin duka ranshi babu dadi.

Bai sake magana ba har suka hau titin zooroad,wanda nata gane ina zai kaita ba saida suka kai bakin gate din gidan zoo,yayi horn masu gadi suka bude yabiya kudin shiga suka bashi ticket yashige.

Maimakon ya dakata a inda aka saba parking sai taga yayi ciki,tafiya kadan sai gasu a wani garden na daban,ya tsaida motar ya dubeta
"Fito muje" da mamaki ta dubeshi
"Me zamuyi anan?,bafa yara muka kawo ba?" Kai ya kada
"Na sani,ke na kawo kisha iska ki huta kadan"dan shuru tayi kana tace
"Amma kasani na baro yara a gida,sannan ana iyayin baqi yaudin"
"Yara ai basu kadai bane,akwai mutane a gidan,baqi kuwa duk wanda yazo akace masa kina asibiti ai yasan lalurarki" bata sake cewa komai ba ya dafe mata murfin motar tafito,nan ma yasake wani pyment din suka shiga.

Sosai wajen taji ya sanya mata nutsuwa,saboda yanayinsa dake luf luf da shuke shuke masu bayar da sanyi da iska mai dadi,hakanan babu hayaniya kai kace ma ba'a gidan zoo din kake ba.

Sai da sukayi awa guda cikakkiya ya tabbatar data sake samun nutsuwa da hutu sannan yazauna yana fuskantarta,dukka hannayenta yakama yana duban qwayar idanunta bayan yakira sunanta,kasa amsa mishi tayi,sai zuciyarta tayi rauni,duk wani nauyi data rinqa daukewa a qirjinta taji yau yana neman ya rinjayeta,cikin murya mai taushi yace
"Nasani cewa kinyi qaqari matuqa,kinyi jajircewa da tsaiwar daka,hakanan kin nuna sadaukarwa da kuma kara da karamci irin naki,tunda lamarin nan yataso bama yanzu ba tun zamanin maryam zuwa yanzu,ina mai matuqar miqa godiyata a gareki da kika zamemin abun dogaro cikin gidana,kika amsa kuma wannan sunan da hausawa ke baku na UWAR GIDA RAN GIDA,babu shakka kedin ran gidana ce halima bawai ganin idanunki ba,Allah shine shaidata,na gode qwarai halima,ubangiji yaci gaba da baki juriya da qarfin hali,ya kuma saka miki da aljanna madaukakiya" idanunta yarausayar taba son qarfafawa kanta gwiwa ta amsa addu'arshi,sannan ya dora
"don Allah inason wata alfarma awajenki halima game da gidana"
"Allah yasa bazata gagareni ba" ta furta a sanyaye"
"In sha Allahu,na yarda da nagartarki halima,inason aduk sanda nayi kuskure a tsakanin kuku ukun kiyimin uzuri,sannan karki qyaleni ki sameni ki nusashe dani,ki dorani kan hanya" idanunta tawaro waje har hakan yaso bashi dariya
"Baban amir,gaskiya ka doramin aiki mai girma da nauyi,dukkaninmu matanka ne,hakanan kana qaunarmu ka auremu,ta yaya zan dinga bin diddigi kan lamuran kowaccenmu ina gyara ko kwaskwarima akai?"
"Ashe bakison kada nashiga wuta kenan ko halima?"da sauri ta girgixa kai
"a'ah,'a'ah,ko kadan,zanyi iya abinda naga zan iya dai,kuma shine daidai wanda zan fita haqqin addinina" kai ya kada shima
"Ko hakanma na gode,Allah ya saka da khairan" amin ta amsa mishi tana kallon yatsunta da suka dan tashi kadan fiye da dada kafin tasamu ciki.

"Amma kamar fa fushi ake dani,tunda kwana da kwanaki ko kallona ba'ayi" a hankali ta daga kai ta dubeshi
"To meye damuwarka tunda kana da sabuwar tauraruwar da idan ta kalleka koda ban kalleka ba ta isar maka?" Dariya sosao ta kamashi amma ya danneta,wato kishin dai,kishi kumallon mata,idan yataso sai an amayar dashi,kai ya kada
"Ko kusa ko alama babu wata tauraruwa da zatayi dai dai dake halima,ke din ta dabance,yadda kika zama ta farko a zuciyata da rayuwata haka kike ta farko har yanzun,matsayinki bazai taba dai dai dana kowanne mace ba,kece kika fara sanin waje jibril,ke kika fara shiga rayuwarsa,kikasan dukkan wani sirri nashi,kika zauna dashi a yadda yake tun a lokacin,tota yaya matsayinki zaiyi daidai dana wata?,ummm?" Sosai taji wani sanyi yana sauka cikin zuciyarta,bata taba tsammanin cewa har yanzu tana da wannan matsayin da martabar a zuciyar jibril ba,ta dauka tuni an mata overtaking komai nata daga gareshi,ashe batasan akwai wata qima daraja da martaba da ita kadai ta mallaketa ba daga wajensa
"Sarautarki ta dabance ai halima" dole murmushi ya qwace mata,ta dinga jin wani nishadi da farinciki yana ratsata.

Sai da sukayi sallar la'asar anan sannan suka baro gidan zoo din.

A hanya ya dinga tambayarta me takeso?,to kusan bataga abinda takeso din ba harsai da suka baro hanya sosai sannan taga rake tace tanaso,ya tsaya ya siya mata mai yawa kuwa sannan suka wuce gida.

Bayan ya aje motarshi a muhallinta tana gaba yana biye da ita riqe da ledar raken,dai dai sanda zasu shiga dogon soron dazai kaisu ga tsakar gidansu amarya rufaida ta rako nata baqin zata juya sukayi kacibus,tabi mmn amir da kallo wadda ke tafe a nutse,sanye da doguwar rigar atamfa budaddiya sosai,kanta yafe da mayafin daya dace da atamfar,qafarta plate shoes ne sai qaramae jaka ta maqalewa a hannu data sanya wayarta da tarkacen magungunanta.

Ta ganeta sarai,amma banda bbn amir dake bayanta riqe da leda niyya tayi tayi shigewarta da sunan bata gane wacece ba,ledar hannunsa tabi da kallo,wani baqinciki na tokareta,wato saboda ya raina mata wayo daga cewa zaikai mata kudi shine yaje yayi zamansa harya buge da riqo mata leda kamar wani almajirinta?,dukka kwalliyar datayi da tanadin datayi masa saidaya goge ya salance?,ganin irin kallon datake musu yasa ya mmn amir yin sallama wadda ra maidota hayyacinta,saita dan dake tana amsawa ciki ciki,saidai fuskarta babu fara'a sam.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
_Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA TARA*

Dukkanin idanun rufaida nakan bbn amir tana dubanshi,ranta a bace yake sosai saboda bata tsammaci zai mata haka ba,ta yaya zaice mata zaije yanzu yadawo amma kawai saita ganshi da matarshi?.

Saita maida kanta ga mmn amir tana qare mata kallo,wannan baqar matar ma zatafi mata sauqin gamawa aiki,saita zarce da qaremata kallo,saidai bayan baqin bataga wani abu na kushe tattare da ita ba,duk da cikin dake jikinta yasauya wasu daga cikin halittarta,amma mmn amir din black beauty ce ciki ya sanyata baqi,tana da idanuwa da hanci mai tudu na wani siriri mai tsini bane can,cikin dai yasanyashi budewa,duk da cikin jikinta batayi wata qiba ta azo a gani ba,duk da ta qara kauri,bata tsaho hakanan ba gajeriya bace,tana da yalwar gashin gira.

"Sannu amarya" mmn amie ta fada saboda yadda taga rufaidan ta xuba mata idanu,saita dan basar sannan murya ciki ciki tace
"Yauwa sannu" ta fada kamar batasan fuskan mmn amir din ba,bata kulaa ba hakanan bata damu ba tasoma qoqarin rabeta tawuce tana cewa
"Ya kwanan baqunta?"
"Lafiya lau" tasake fada ckki ciki,batako waiwayo ba ba bare tasan meke wakana tashige cikin gida abunta.

Da sallama tashiga tsakar gidan,tana iya jiyo surutun yaran daha dakinta,dakin mmn ummi labulenta na asake kamarma babu mutum cikin dakin.

Sunajin muryarta yaran gaba daya suka fito suna mata oyoyo
"Kuyi haquri karku kayar dani" ta fada tana murmushi itama,sau tari yaran sukan debe mata kewa da sakata walwala,sun shiga ranta sosai har takan damu da lamuransu fiye dana jama'ar gidan,da yaranta dana mmn ummi kusan dukansu kamarsu daya,hakanan tana musu kallon yaranta,shi yasa kome zatayi musu tanayi ne kamar ita ta haifesu bata banbantasu da natan.
Chapter 12 · 0% Book details