Sashe 4
Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haba mmn ummi,wai sau nawa zan gaya miki wannan?,yanzu meye amfani ko ribar abinda kikeyi,maqota da masu wucewa duka sunajinki?,kafin a tsinewa baban amir sau daya an tsinemiki sau goma koda mala'iku kuwa" harara tayi kaman zata watsa mata saita fasa,cikin qunar rai da fusata tace
"Kome baban amir yayi yasamu goyon bayanki ne,tunda kinsan hannu daya baya daukar jinka,ba yadda banyi dake mutare abinnan ba amma kika qi bada goyon baya,yanzu kinsan muggan kalamai da alwashin da yarinyar takeci a kanmu nida ke?,to nida ke mu shirya kayanmu dukanmu gaba daya saita fitar damu" murmushi maman amir tasaki tana kada kai
"Kome ta gaya miki maman ummi kece kikayi babban kuskure,ina ruwanki da budurwar mijinki?,meye hadinki da ita?,kin fita kusa da mijinki,kin fita daraja koda ba haka bane to a wajen Allah haka ne babu kuma wansa ya isa ya kankare,koda tashigo gidan kuwa karki manta zata jima bata cimma matsayin dake kike kai ba,tunda ko banza kin rigata samunshi,kin rigata samar masa da diya,to me yayi saura?,me zai daga miki hankali?,maman ummi...." Ta kira sunanta cikin nuna da gaske zata furta mata maganar
"Inada yaqinin nafiki son abban amir,na kuma fiki kishinsa" saitayi jagale tana kallonta,magana takeson gaya mata kenan kome?
"Qwarai,ina tare da abban amir tun auren saurayi da budurwa,tun baida wani abun azo a gani,amma daga sanda yasoma neman aure na sanyawa kaina salama,inajin kishinsa kamar na mutu,ina kuka saboda kishi,ina kasa ci in kasa sha saboda kishi,amma dana fuskanci wanda nake abun saboda shi shi jin ransa yake kamar sallah saina sawa raina haquri da dangana,na kawo idanu na zuba akan duk wani abu da zaimin cikin sani ko rashin sani,wanda zumudi da rawar kaine ya sanyashi dama wanda yayi saboda radin kansa,yanzu gashi an wayi gari na barshi da kunyar abinda ya aikatamin a baya,na tsira da mutuncina da darajata a idanunsa saboda ban aikata duk wani abu da zai nuna rashin nutsuwata ba,babbar zubewar girma ko daraje a wajenki na matar gida budurwar miji ta zageki,bari na tambayeki..."shuru ta sakeyi tana dubanta
"Tunda kuke da baban amir har kika shigo gidan nan kin taba kiransa na daga wayar?,kona taba kiranki dai dai da rana daya?,kin taba jin muryata ko ganina?" Kai mmn ummi ta girgiza sannan tace
"Duka ban taba ba,amma Allah yagani ni mmn amir bazan iya koda rabin abinda kikayi ba,wayar dare,kiran dare amma ace duka baki nuna ko daukan mataki ba?,bazan iya ba wallahi,babu wata shegiya data isa ta takani wallahi ko wace saina maida mata,duk wadda ta nunani da yatsa saina karyashi" ajiyar zuciya mmn amir tayi tana kallon mmn ummin,shi yasa a rayuwa duk abinda kasan bakaso kada kayima wani,idan ba haka ba kuwa,watan watarana saiya fado a kanka,sai an maka,sai an ramawa wanda ka cuta ko ka cusgunawa koka zalunta.
"Shikenan,Allah yabada sa'a" ta fada tana miqewa gami da bar mata dakin.
******* **** *******
"Wai maman amir mu mmn ummi zata wulaqanta?,har ta ganmu ta dauke kai tawuce daki?haka ta koma?,to do n yaya zai qara aure shine me?,me za'a fasa?"
"Mtseweeew,kice fa kika damu wallahi,ni tayita kumburinta idan taso ma ta fashe,qarin aurene babu fashi sai yayishi ehe" murmushi kawai halima tasaki tana zama bayan ta aje musu kwanon abincin da ita da kanta tashiga kitchen tazubo musu,ganin mmn ummi dake da girkin bata da niyyar basu din,shuru tayi na sauraron qorafinsu da yadda kowacce ke zuba baqar magana kan mmn ummin,dubansu kawai take don bata data cewa,zuciyar musulunci da ilimin addini kadai daya ratsata yasanya taci gaba da mu'amala dasu,a shekarun baya babu tamkar ya maryam a wajensu,a sanda ya niyyaci qara auren babu abinda bata gani ba daga gunsu,basa boyewa har a gaban idanunta
"Na qagu wallahi maryam tashigo"
"Wai kinga matar yaya kuwa?,tabdi,wallahi yaya yayi zabe"
"Ke ai wannan kankat ce,tayi a rayuwa,ga ruwan mutunci zallarsa,bakiga yadda takesonmu muda umma ba"
"Kinga kyautar data aikowa umma da ita kuwa?,ke yaya kanshi fa yamato,donta iya soyayya"
"Nce gareta mafa,wallahi da yaya zai barta tsaf zata dinga fita aiki,amma tace masa ma ita tafison tazauna gida takula dashi" ire iren wadan nan maganganun dama wadansu wanda ba zata iya tunasu ba ba wanda basu fadi ba a gabanta,babu kara alkunya ko kawaici,sunsa qafa sun shure duk wani alkhairi nata kyautatawa da haba haba da take dasu,a lokacin ambaton Allah datake yawaita yi shi kadai yazame mata haske,uwa tagari kuma da take da ita tayi mata jagora,matakin farko data soma mata dannar qirji,ta kuma kwabeta,a yanzun taga alfanun hakan
"Wallahi maman amir ni yadda kike yafi komai burgeni" cewar jidda qanwar baban amir,sai a sannan tadago ta dubeta
"Kishi na hankali da nutsuwa ba irin nata ba na jakan mata,ai rannan rufaida ta gayamin komai,wallahi ta burgeni data rama abinda tayi mata" cewar jidda tana ci gaba dacin abincinta
"Indai rufaida ce dai dai da ita take,yarinyar da takejin quruciya da karatu akanta" dariya haula tayi
"Nifa harso nake naga ya zatayi idan rufaidan tashigo,gaskiya tana ruwa,maman amir kedai wallahi kinyi a rayuwa da kika iya kama girmanki,kaman baki da kishi" kai ta girgiza kawai tana fidda dan qaramin murmushi,sa'annan cikin nutsuwa ta dubesu
"Babu wata mace da bata da kishi,duk matar datace bata kishin mijinta toba shakka an samu matsala,kuma idan aka zurfafa bincike akwai wata a qasa,zan muku maganar daban taba muku makamanciyarta ba,abinda kawai zanja hankalinku akai shine,ku gane cewa dukkan mace macace,kuma ba'a cewa jifa idan yawuce kaina yafada kan uban kowa,koda baku da aure ke jidda kina dashi,kuma kuma wataran matan wasune,gidan wasu zaku je,cikin dangin wasu,Allah yasa kun fahimceni"
"Eh hakane,amma wallahi kawai dai duk wanda yadebo da zafine bakinsa,ni banga abun wannan kishi hakaba ina dalili?" Cewar jidda tana watsa hannu,sai kawai mmn amir din ta watsar da maganar tadauko musu wadda ta kawosun,wunin da za'ayi cikin gidan.
*BAYANA AWANNI*
Tunda ta kawo masa abincin ta tattarashi ta watsar,banda ma 'yan nasihun da maman amir tayi mata da babu abinda zai sanya ta saurareshi,shima cike yake da ita,hakan ya sanya baibi ta kanta ba yaci gaba dacin abincinsa,yana wasa da ummi daketa sabgarta saman carfet,lokaci lokaci yana diban abincin yana bata da cokali harya kammala,yasha ruwa yadauke ummin ya karkade mata jikinta yadorata saman cinyarsa sannan ya dubeta
"Me dame kike da buqata keda yara,inajin saura baifi sati uku ko biyu ba tariya" wani kallo ta watsa mata,kishi na tokare mata a qirji,ta rasa ma me zatace masa
"Kaje ka qarawa amaryar inaga hakan yafi armashi"
"Ohkey" kawai yace ya saba ummi a kafada yafice,binsa tayi da kallo,watoma bashi da lokacin lallashinta kenan barema ya biye mata suyita ba ko zata samu sassauci cikin ranta.
Kai tsaye dakin mmn amir yanufa,tana kwance saman doguwar kujera sanye da doguwar riga mara hannu,yaran duka na zaune qasa suna kallon tv,sallamarsa yasa kowanne maida hankalinsa bakin qofar yana fadin abba,abba,miqewa tayi daga kwanciyar datayi tana gyara zamanta,bayan ya gama da yaran ya dubeta
"Sannu" yace da ita yana dubanta,murmushi tadanyi sannan tace
"Yauwa"
"Ammm....nace dame dame kuke buqata kedasu ahmad gaba daya dasu ummi" ganin ya bata dama yasa lissafa masa iya abinda take ganin tana da buqata din,aljihunsa ya lalubo ya qirga kudi ya miqa mata,hannu biyu tasa ta karba sannan tayi masa godiya,ya sake qirgo wasu ya miqa mata
"Wannan nasu ummi ne,a musu siyayyar duka abinda ya dace" hannu tajanye tana kada kai
"A'ah,ka bawa ummansu ina ganin ta fisu sanin me dame suke buqata"
"Karbi nan,nasan da itadin ai nabaki ko?,banason jan zance" haka tasa hannu ta amsa badon son ranta ba,ta sake masa godiya,ya dubi amir
"Dauki ummi ka maidata wajen mamarta ta soma bacci" ya miqe yadauki yarinyar,shima yarufa masa baya.
Kudin ta irga,ya wucema yadda ta tambayeshin,tasan zai isheta tagama duk wata siyayyarta harda ma qari a sama,saita hada da kudinsu ummin ta adana da zummar gobe tasamu mmn ummin,da alama tamasa halin nata ne shi yasa ya watsar da ita shima.
*mrs muhammad ce*👑👁️🗨️👁️🗨️ *HANGEN DALA* 👁️🗨️👁️🗨️
_Ba shiga birni ba_
©️®️ *safiyya Abdullahi Musa Huguma*
*BABI NA HUDU*
Gidan babu kowa yayi shiru kasancewar yaran dukka sun wuce makaranta maman ummi tana dakinta wanda tun sape bata gilmawarta ba itam tana nata dakin saidatagama kintsa duk abunda xatai na ayyukanta sannna ta dauko kudin da baban amir yabata sannan tanupi dakin maman ummi akwance ta tarar da ita tana kallo ummi najin sallamarta tararrafo gunta tadauketa tana cewa xoki naushi dan uwanki na ciki yadda kikasaba sannann tai sallama takarasa parlourn tashi tai maman ummi tai tazauna fuskarta babu walwala maman amir takarasa tasamu daya daga cikin kujerun parloun tazauna tanacewa muntashi maman ummi murya acushe ta amsa tanacewa lafiya lau to madallah tafada tana mika mata kudin dake dake hannunta amsa tai sannan tace wannan kuma namaye maman amir tadubeta tace kayan siyayyar yarane jiya baban amir yabasu"
"Jiya da yaushe?"
"Sanda kike can kina sake kashe kanki wajen mijinki,mmn ummi bakyajin magana,amma Allah yagani nayi iya abinda zan miki,shine shaida" daga haka bata jira taji me zata fada din ba ta miqe tafice a dakin.
Da kallo mmn ummin ta bita takaici na cikata,wato kudin siyayyar 'ya'yan nata ma yafi qarfinta?,yafi qarfin yabata da hannunta saiya kaiwa kishiyarta?,qwafa taja ta dauki kudin ta irga,saita rabasu biyu tana ayyana abinda zatayi dasu,rabi kawai zatayi musu siyayyar dasu,saura kuwa zubin adashinta zatayi dasu,ribar qafa kenan ta fada cikin ranta.
******** ****** *********
"Wallahi wallahi babu shegiyar da zanwa girki,girki?,ni nace ka qaro auren kenan,idan sunsoma su rube saboda basuci abinci ba" ta qarasa maganar tana kashe famfo gami da daukar botikin wankanta tashige bandaki ta banko qofar.