← Book details Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duban tsakar gidan take adan kaikaice saboda yanayin tsaftarsa da tsarinsa bai mata ba,ba'a wani share yake fes yadda take masa ba,hakanan tawuce tana furta Allah ya kyauta,tadaga labule tashiga dakin mmn ummi.

Tana zaune falon tana shafa mai,da alama wanka tagama,ta daga kai fuskarta ba yabi ba fallasa ta amsa sallamar tana ci gaba da shafa manta.

Tana daga tsaye tasaki usman ya isa wajen mamarshi yaxauna yana gaya mata umma ce tayi masa wanka
"Wanne irin bacci kayi haka usman?" Ta tambayeshi tana dubanshi
"Ki barshi da yunwa ba dole yayi bacci ba,da kika hana yara abinci ke aisaiki hada kici" ta fada tana jefa mata harara,don sam ta kasa hadiye takaicinta,ta tsani a cuci yaro,shida bai gama sanin ciwon kansa bama bare na wani.

Dubanta mmn ummi tayi kawai batace komai ba tana ci gaba da shafa manta,itama saita juya tafice daga dakin,tana fitowa tanufi nata dakin tajiyo dariyar rufaida daga soro,saiga bbn amir na biye da ita,riqe take da hularshi,taci kwalliya da qananun kaya.

Sarai taga mmn amir na fitowa,hakan kuwa yayi mata dadi sosai,saboda haka ta tsaya anan tasoma shagwaba tana bubbuga qafafu kan saiya dauketa.

Shi sam baiga mmn amir din ba,saboda haka ya sungumeta,tahau kuwa qyalqyala dariya cikin jin dadi,bai ankare ba saidaya kusa da dakin rufaidan sannan yaga shigewar mmn amir dakinta da rufe qofarta,ya sauke rufaida da hanzari yana fadin
"Subhanallah,ashe matan gidan suna kusa" fuska ta turbune sannan tace
"Su waye matan gidan?,naga nima matar gidance,kuma kawai saboda wasu saika kama ka saukeni bayan baka qarasa dani ba" ta fada fuska kicin kici,cikin nuna fushi tayi gaba tashige dakin,yabi bayanta da hanzari yana kiranta.

Washegari mmn amir din tana zaune dakinta tana karyawa,yauma kamar jiyan bata leqa waje b,bbn amir din yashigo dakin cikin shirin fita kasuwa,ya kasa hada ido da ita saboda abun jiya,bayan sun gaisa yahau kame kame
"Kin zama hajiyar daka ko?,haka kawai kin koramin yara daga gida" kofin da take shirin kaiwa bakinta ta dakata ta dubeshi
"To ko aje a daukosu?" Ta fada cikin gatse gatse,don itasam bata sha'awar yaranma su dawo gidan nan kusa,saboda ta fuskanci take taken rufaidan,ko dazu tana jin ihunta daga daki,shima kuma yasan sarai sunji,abinda yasake sakashi kunya kenan,kuma ba wani abu yayi mata ba,kawai dan tsere ne haka da ba'a rasa ba na sababbin ma'aurata ya kamota shine tasaki wannan ihun,shi kansa abun yabashi mamaki don baikai tayi ihun ba
"Ni na isa,inna fa akai kaiwa su,aita isa damu gaba daya" shuru yadan ratsa don bata sake ce masa komai ba,sai kuma yayi gyaran murya
"Ni zan fita,ko akwai wani abun?" Kaita kada kawai tana ci gaba dashan shayinta
"Shikenan,saina dawo"
"Allah yatsare" ta amsashi a taqaice.

Har yakai qofa sai kuma tasake cewa
"Amm jimana" waiwayowa yayi yana dubanta,shi kansa sai yakejin wani shakka shakkarta yadda ta tsare gida,hakanan vabu wani abun magana da mutum xai tankata dashi,ta ga abubuwa amma kamar bata gani ba,taji amma kamar bata cikin gidan
"Don Allah kome zai faru kayi qoqarin kula da kiyaye tarbiyyar yaranka,don dukkaninsu sun taso,sannan kowanne da irin baiwa da kaifin basirar da Allah yabashi,so kome zai kasance yadinga zama cikin tsari da kiyayewa idanun yaranka" yasan magana ce tayi masa mai harshen damo cikin hikima da fasaha ba tare data kama sunan kowa ba,ya kuma fahimci inda tadosa,donko shidin yasoma wannan tunanin,saiya gyada kai
"Gaskiyane,nakuma gode da wannan tunasarwa uwar gida sarautar mata,Allah yayi albarka"
"Amin" ta amsa can qasan maqoshinta,saiya saka kai yafice daga dakin.

Daga nan dakin mmn ummi yanufa,don dama yakanbi girma girma ne,zaune yasameta itama ga abun karinta ta saka a gaba,saidai bata taba komai ba,sai usman da mubarak dake karyawa abinsu.

Qafarta na dore daya saman daya tana karkadata,kana kallonta sau daya zakasan akwai abinda ke cin zuciyarta kuma tanason ta amayar,da qyar ta iya amsa sallamarsa kamar wadda aka shaqe takuma bishi da banzan kallo,bai wani lura ba harsai daya gama biyewa yaranshi yana yiwa ummi wasa sannan ya dubeta
"Mun tashi lafiya" yasoma gaidata maimakon ita ta gaidashi
"Gashi nan kaga alama"
"To madalla" ya fada a taqaice,tunda yaga yanayinta da yanayin gaisuwarma yasan wani abune kuma na daban,bata rabo da qorafi sam a rayuwarta,kullum cikin matsala daga wancan sai wannan,shi yasa bai fiya jimawa a dakinta ba,hakanan ko ranar girkinta ba wani doguwar hira suke ba idan ba ita taso ba.

Da dafari sanda yake dokinta yana ganin tafi mmn amir iya komai saboda karatunta ya dara nata bai ganin illa da aibun dukka wadan nan halayen nata,saida tafiya tayi tafiya sannan ya tantance tsakanin aya da tsakuwa.

Yana dire ummi yace
"Xan fita,akwai wani abu?" Ya qarashe zancan yana dire mata kudin cefane,da harara tabi kudin kafin ta maida dubanta kanshi
"Wallahi wallahi kana bani mamaki jibril,bansan rainani dakayi dukka cikin matanka yakai haka ba,ku gama tiqa dariyar kaida waccar me zubin karuwan,kashig dakin mmn amir ka kusa kashe minti goma sannan nika shigo a wani tsaitsaye kabani kudin cefane,wato bauta itace aikina ko?" Yaran yaduba,baison wani cecekuce gabansu,wanda wannan dabi'ar mmn amirce takoya masa ita,da fari bai dauki hakan a bakin komai ba,sanda yake ganiyar neman auren mmn ummi yakan iya fadata da fada gaban yaran,koya caccaba mata maganganu,iyakaci tayi shuru,idan sun mata zafi da yawa tayi kukanta ta goge hawaye.

Sannu sannu sai Allah ya canzashi,wanda yasan ba komai bane yakawo hakan face addu'a data saka a gaba babu dare babu rana.

Yasha raba dare suna waya da mmn ummi suna kwance gado daya da mmn amir,baya shayi ko shakkarta,takan tashi ko kallonshi ba zatayi ba,tun a sannan bata da bandaki cikin falo sai tsakar gida,nan zata fito ta daura alwalarta ta koma falo tayi shinfida tahau sallarta,tabarshi shi kuma cikin dakin ya qaraci wayarshi har yayi bacci,wani lokacin bai sake ganinta sai zashi sallar asubahi.

Yakanyi mamaki idan washegari tatashi wasai tashiga sabgarta da yaranta,fuskarta cike da annuri,wanda duka hakan bai rasa nasaba da wannan sallar dare data kusa kwana yi.

"To tashiga hankalinta,idanma tanayine saboda muji n bata a gabana,saidai idan ita bata da tarbiyya mu muna da ita ehe" bai saurareta ba sai yunqurin danne zuciyarsa da yake,yasa kanshi yafice daga dakin.

Ya tabbatar da cewa kura ce tayi lafiya,ko kuma yakoma kan tarbiyyar mmn amir ne,inda ta sameshi a lokacin da yake a bbn amir dinsa bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman ba yana kallonta,koda bada shi take ba,saidai mmn amir ta zame masa mudubi,hakanan yakanji a karan kanshi bai kamata yayi wani abu naba dai dai ba,kobanza a yanzun iyali yake tarawa.

***** ***** ***** ******

Cikin kwanaki amarci sosai rufaida takeci yadda takeso,tasamu kusan duk abinda takeso daga wajen bbn amir din,don idan yadawo daga kasuwa babubinda yake sake fita yana tare da ita,hakan yakan mata dadi yana faranta ranta,takanyi kowacce shiga da take tunanin zata ja ra'ayinsa da hankalinsa,ta kuma samu yadda takeso,zub da habaici jirwaye da kamar wanka,dariya da darrarku na cusa haushi da takaici dukka ta baje abinta.

Babu wanda ke qunsar takaici irin mmn ummi,nafarko bata da wata sana'a da takeyi face zaman dabaro,zaman hira,zaman charting ko xaman kallo,uwa uba gaba duk wani motsi na rufaidan idanunta yana kai,kome take tana sane dashi tana biye dashi,hakan ya sanya tunda rufaidan ta fuskanci hakan saita qara qaimi,kullum burinta ta bullo da wani sabon abun dazai basu takaici.

Saidai ta bangaren mmn amir ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,wasu abubuwan tana sane dasu itama,amma data fuskanci zuciya na neman janta saita dawo da sana'arta,nan da nan taci gaba da saida ruwa da lemonta,kasancewar ta iya sosai,ga uwa uba tsafta,hakanan idan bata komai takan zauna tayi tilawar qur'ani,idan ta gaji ta kunna kallo ta taba,dama ita ba charting take ba,idan tagaji da kallon kuma takan kunna karatun qur'ani yadda zai cika dakinta ya hanata jin motsin kowa da komai,yara kam har yanzu bata daukosu ba,don haka wuni takeyi daki abinta,idan dare yayine takan nemi izini wajen abban amir tadan fita tayi tattaki kadan tadawo gida,takan leqa wani sa'in gidan mmn laila maqociyarsu,kuma qawarta qwaya daya da take da ita,bata fiya shiga gidan tayi fitowar banza ba,takan qaru da ita ta fanni da dama,kusan halinsu yaxo daya,hakan yasanya suke abota sosai.

Abu biyu zuwa uku ke damun rufaidan,yadda ta fuskanci jibril din mutum ne mai son yara,uwa uba baya yarda da wulaqanta kowa cikin matansa,amma ta fuskanci kamar mmn amir din yafi kaffa kaffa da lamarinta akan mmn ummi,hakan yasanya tasake daura damara gamida cin alwashi.

Cikin haka kwanakin amarcin amarya rufaida sukaci gaba da turawa,har mmn ummi tagama girkin yazamana a yanzun rufaidan ce zata karba.

******* ******** *******

Karfe bakwai na safiya ya farka daga baccin daya daukeshi bayan dawowarsa daga sallar asuba,yazauna saman gadon sosai yana kallon rufaida daketa sheqar baccinta,donko sallar asuba batayiba kasancewar tana hutun sallah.

Hannunsa ya saka saman filon da take kai ya bubbuga yana tashinta,daqyar ta iya bude idanunta da sukayi jaa saboda bacci,mugun dadin baccin takeji sosai
"Tashi ki doramin ruwan wanka,saiki dafamin wani abu,zan fita daurin aure qarfe tara da rabi nakeso nafita" lumshe idanunta tayi tanajin wani yaji yaji na bacci,ta yaya tana baccinta me dadi zaice tawani tashi tadora masa ruwa da abinci?,ruwanne bai iya dorawa ba ko abincin ne dole sai yaci,itafa ba abinda tatsana tun a gida irin ka hanata baccin safe,daka hanata bacci da safe gwara kayi mata koma meye
"To" kawai tace dashi ta maida idanunta ta rufe,ya zaci taji,saboda haka yamiqe yafita falo yashiga bandaki don ya rage cikinsa kafin ruwan yayi zafi.

Saidai abun mamaki koda yafito wajen minti ashirin saiya sake samunta kwance abinta,babu alamun tatashi ma,sake tashinta tayi,ta dago kao cikin fusata,wanda har taja tsaki ba tare data tuna a inda yanzun take ba
"Wai meye?,nifa gaskiya bacci nakeji,kabari idan natashi saina dora maka mana" tana kaiwa nan tasake maida kanta
"Ya zakici haka,tashi da Allah,ina gayamiki zan fita ne qarfe tara da rabi fa" cikin qunar rai kamar ta kutuntuma ashar tatashi tazauna,fuskarta a dinke tsaf,bacin rai kamar tayi me?,ta kalli agogo taga takwas saura
"Haka kawai saboda rashin sanin muhimmanci mutum a akama a tasheshi,toko a gida ni iyanzu ina kwance,babu kuma wanda yake tashi na,sai kawai yanzu azo a hau tashin mutum" ta sake jan tsako bayan ta gama qunquninta.
Chapter 15 · 0% Book details