← Book details Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Hangen Dala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da qyar suka barta ta qarasa falonta,tazube kan kujera cike da gajiya,salima na mata sannu da zuwa ta amsa tana dubanta sannan tace
"Me aka dafa yau a gidan,yunwa yunwa nakeji" dan tabe baki kadan salima tayi sannan tace
"Babu abinda aka dafa,suma gari na basu suka siyo da kudin da kika barmin muka jiqa muka sha" cike da mamaki take dubanta
"Gari kamar yaya?,bayan store dinmu cike yake da kayan abinci"
"To mmn ummi dai bata girka komai ba,amarya ma snacks ta baiwa baqinta dasu alkaki na gararta" shuru mmn amir tayi,tana mamakin halayen maryam din duk da baqinta bane,amma daga bisani ta rage wasu da zama yayi zama,shine yanzu takeson dawowa dasu?,rasa abun fada tayi har zuwa wani lokaci kafin tace
"Allah ya kyauta yarufa asiri,tashi kijr kitchen din,ki jawo qaramin gas dina ki dora mana indomie"
"Yeeyy,umma dama yunwa nakeji tun dazu,nagayawa mamana tace naje abba yabamu abincin" cewar usman da bashi da wani cikakken hankali ko wayo,saita dora hannunta saman kanshi
"Ba haka take nufi ba kaji usmanu,yanzu za'a dafa muku indomie kuci" kai ya gyada mata,saita bisu da kallon tausayi,daidai sanda amir yashigo da ledar rake ya aje mata
"Ga kayanki inji abba".

Jawo ledar tayi gabanta,ta bude ta rarrabawa yaran,itama tadauki wani tasoma sha ko zata rage yunwar da takeji,take kuwa dukkansu suka nutsu,kowa yasamu waje yazauna yasoma shan nasa sunata surutu.

Fuuu rufaidan tayi dakinta,yabi bayanta bayan ya baiwa amir ledan mmn amir din yace yakai mata.

Zaune yasameta kan hannun kujerarta rungume da hannyenta a qirji,ta cika tayi fam kamar zata fashe,dankwalinya gana goshinta,saiya zagayo yazauna kan kujerar da take zaune din,zumbur tayi zata miqe yacafke hannunta,ya kuma jawota ya riqeta gam,cikin fushi da bacin rai tace
"Sakanni jibril,aini wallahi ka bani mamaki,cikin kwana saya tal amma inata ganin abubuwan da ban tsammata ba daga wajenka,babu abu guda daya tal daka iya cikamin shi sai abubuwa kala kala,tun daga dare zuwa wayewar gari,daga wannan sai wancan"
"Haba mana amaryata uhumm?,kiyi haquri ki tsaya ki saurareni,nikaina bansan dukka abubuwan nan zasu taso haka ba,idan kin duba duka lalura ce,ni mutum ne me iyali dole nakula da haqqin kowa nakuma saukeshi,idan kika duba mmn amir kema wataran haka zata kasance akanki,zakiso nayi burus dake naqi bin lamuranki?" Saita kalleshi sosai
"Sai kuma akace ka dauki lokacina duka ka rabawa matanka da yaranka?" Shima sosai ya dubeta,duk da yanason shawo kanta ne amma hakan bai hanashi cewa ba
"Au...rufaida abunma babu kara,matana dai amma yara ai namune gaba daya ko?" Saita dan yatsina fuska tana jin takaici har cikin ra ta
"Sorry,ka fusatani ne,yaranmu to"
"Daga yau ba za'a sake ba kinji,haba amarya fushi baya miki kyau" ya fada yana lakace mata hanci,tanason jibril sosai,dole yasaki murmushi,sannan tashigar da qorafinta nabiyu
"Kuma sannan jibril baka isa da gidanka bane ko kuma dama haka ake zama da yunwa a gidanka?" Fuska yadan tsuke yanajin tambayar banbarakwai,tun tana gida dama yana dan fama da ita kan rashin iya magana,wani lokaci idan tayi wata maganar sai kaji kamar mecin kashi
"Kamar yaya?,wacce iriyar maganace wannan?" Gyara zamanta tayi sosai sannan tace
"Dole na fadi haka,yau babu abinda naci sai snacks da nazo dashi daga gidanmu,koda nayi baqima ka duba kaga abinda nabasu" tafadi taba numa mishi kwanukan da bata kwashe ba a wajen masu dauke da kayan gararta da lemo data bayar aka siyo mata a shagon layin
"Ba'ayi girki ba?,tome yaran sukaci?" Ya fada yana jeho mata tambaya,saita tabe baki wani takaici yana qumeta,wato bata ita ko baqinta yake bama,ta yaranshi yake?
"Oho" ta bashi amsa tana sake tabe baki
"Ina zuwa" ya fadi yana miqewa kana yafice,dariya tasaki tamiqe zuwa cikin bedroom dinta tana cewa
"Allah yasa ta kwabemusu,shegiya naga ta shegen daukan kai yau ai".

Kai tsaye dakin mmn ummi yanufa,baima kula da salima dake kitchen ba tana kunna wutar gas,ranshi ne kawai ke suya,taya za'ace yaranshi sun wuni basuci komai ba bayan za'a iya girki a gidan koda bai bada kudin cefane ba,tunda suna da komai.

Wannan karon tayi wanka ta shafe jikinta damai,tana sanye da dovuwar rigar material me gajeran hannu,kwance take abinta saman doguwar kujera tana kallo hannunta riqe da remote,ummi ma nakwance gefanta tana bacci,da alama ta matseta ne ta sanyata baccin dole.

Tunda ta amsa mishi sallamar bata kuma kallo shi ba taci gaba da abinda take,zama yayi hannun kujerar dake daura da ita sannan yace
"Lafiya kuwa yau kike?" Dubanshi tayi ta amsa mishi a taqaice
"Eh"
"Qalau kuma?"
"Ras" ta sake amsa mishi,kai yake jinjinawa,dama yayi tambayar ne don kada ya yanke hukunci bisa rashin sani
"Amma maryam don tsabar wulaqanci dason tozartani gidana akwai baqi ace an wuni ba'aci komai ba tun abincin safe?" Dama jira take yace wani abu,saboda haka tamiqe tazauna sosai
"Ka fito kafadi maganarka kanka tsaye mana,kace kawai ban girka na baiwa amaryarka da baqinta abinci ba,to bari kaji,wallahi wallahi dana dafa taci ita da baqinta gwara kowa yawuni da yunwa,kuma ni ai bamai aikinta bace dazan dafa mata tana zaune,aiba ita tafi kowa zane a duwawu ba,idan ta matsu maiya hanata shiga kitchen din ta girka?,aiba riqe mata qafafu akayi ba kuma qofar kitchen din a bude tawuni bare kace wani abu" daga haka takoma ta kwanta abinta,harya bude baki zai magana sai kuma ya fasa,yanajin akwai lokacin maganar,saiya miqe yafice daga falon ba tare daya sake ce mata komai ba.

Bakin layinsu yafita yaje ya qaro cefane,sanda yadawo salima harta gama dafa indomie din tana juyewa,sannu ya mata ya aje kayan yajuya zuwa dakin rufaida.

Itama kallon yataddata tanayi,ta sauya kwalliyar jikinta da wasu doguwar riga data matseta sosai,murmushi tasakar masa ya maida mata ya zauna yana cewa
"Ga kayan cefane can,kozaki taya yarinyar can salima ku gyara ta dora wani abun,don mmn amir ta gaji gsky,nasan tuni ta kama"
"Tashin balagar tsintsaye" ta fadi cikin ranta,amma a fili saita aje lemon hannunta
"Ina mmn ummin idan mmn amir ba zata iya ba?"
"Ajima zan ganku gaba daya,zaki ji koma meye" narke masa tayi sosai
"Yanzu dear jiya akawoni yau a ganni a kitchen?,idan nayi baqi suka gani aisai sucema bakasona" daga haka tasaki kukan qarya,lallashinta yasoma yi har aka bagarar da zancan,inda daga qarshe indomie yaje yasiyo musu da qwai.

"Anty bbn amir naga ya aje kayan cefane tun daxun,kuma naga ba wanda tafito bare ya taba" salima ta fada bayan ta aje musu indomie din sun soma ci,dubanta mmn amir tayi na wasu sakanni,ta gama gane abinda ke faruwa,ta kuma gama yanke hukunci na matakin da zata dauka
"Mu gama kuje keda rabi'a ta tayaki ku gyara ki kawo amir yakai markade,saiki dora koda shinkafa ce,ki dafa qwai ki hada salad"
"Tohm" salima ta fada tana ci gaba dacin abincinta.

Tanacin abincin tunani na zuwar mata,ta soma gane inda kowa yadosa,zakuma tadauki mataki cikin kwanciyar rai.

Suna gamawar kuwa saliman tayi yadda tace din,ita kuwa sallar la'asar kawai tayi wadda lokacinta yadan gota ma sannan tasha magungunata tashige dakinta takwanta donta huta,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Sanda tafarka anata kirayen sallar magariba,nepa sun dauke wuta amma har bbn amir din ya tayar da inji,wanka takesonyi,saita miqe a hankali tafito falon,babu kowa falon amma tana dan jiyosu daga tsakar gida,fes falon yake yana qamshin turaren wuta kai bakace da yara a dakin ba,kamar dai yadda saliman taga tanayi,tazauna saman daya daga cikin kujerun tana qwalawa saliman kira.

Shigowa tayi da alama tayi alwala ne
"Gani anty"
"Kin gama ne?"
"Eh na gama,suna cikin coolers,na zubawa bbn amir nashi"
"Yauwa sannunki da aiki,yanzu ruwan wanka zaki doramin,idan kin dora din ki leqa dakunansu ki gaya musu abinci yana kitchen,kadan ruwan zai danyi zafi ki kowomin zanyi wanka"ta amsa mata da to ta juya tafita.

Wankanta tayi sosai ta shirya cikin wata doguwar rigar material,wadda tayi mata kyau sannan ta fidda cikinta sosai,ta kuma haska choculet colur fatarta,ta feshe jikinta da turare kamar yadda tasaba,sannan ta dan goga hoda daman lebe tadawo falon.

Suna falon amma zaune shuru sakamakon bitar karatun islamiyya da kowannensu yakeyi,saita samu gu tazauna ta jona dasu itama har aka sallaci isha'i,lokacin bbn amir yashigo,yaran suka tarbesu yariqesu kana ya qaraso,bai zauna ba ya shaidama mmn amir din yanason ganinsu a falonshi,ta amsa masa dato sannan yafice.

Gyara daurin dankwalinta tayi ta sake feshe jikinta da turare sannan tasake fitowa,hanifa tayi sauri tace
"Zan biki umma"
"A'ah ki zauna da salima,yanzu zanje nadawo" daga haka tayi gaba.

Shi dayane da alama sauran basu fito ba,tayi sallama tashiga falon,ya amsa mata yana murmushi kana ya dora da fadin sanda take shirin zama
"Sannu uwar biyu" murmushin itama tasaki,sai data zauna sannan tace
"Ni dayane a cikina,scanning ya nuna" baki ya kama yana murmushi
"Idan kuma Allah boye dayan yayi fa?" Dariya yabata sosai,wai duka yaran gabanshi basu isheshiba,kalen 'yan biyu yakeyi
"Dayanma an godewa Allah,banda abinka bbn amir duk yaran dake gabanka?,ga wanda idan Allah ya nufa amarya zata haifa maka?"
"Dozen biyu fa nakeso" sosai dariya ta qwace mata ganin bilhaqqi da gaske yake
"Ina zakakai dozen biyu"
"Da gaske nake miki,yara ai rahamane" tana dairiyar take gyada kai,daidai sanda rufaida amarya tashigo.

Sanye take da wasu matsatstsun baqaqen riga da skert da suka fidda dukkanin jikinta sosai,taku take d'ai d'ai tana taunar chewing gum tashigo da sallama.

Kai tsaye kusa da bbn amir tazauna kamar zata shige jikinsa,dauke kai mmn amir tayi kamar bata gani ba
"Kin sha magungunan dai ko?" Bbn amir yakuma fada yana dan janye jikinsa ganin yadda ta matseshi sosai,fuskarta a sake tana murmushi kamar dai daxun tace
"Bamu jima da dawowa ba dukka nasha,shinema nadan samu barci"
"To ma sha Allah,Allah ya qara lpy"
"Amin amin,na gode" ta fadi tana maida hankalinta ga wasu jaridu dake kusa da ita ba tare data dubi sashen da rufaidan ko bbn amir din yake ba.

Tanajin yadda rufaida ke janshi da hira irinta soyayya,amma sai tayi kamar batasan sunayi ba,ta maida hankalinta sosai tana duba jaridar,rufaidan rabin hankalinta nakan mmn amir din,so take taga sauyawar fuska ko yaya tattare da ita,saidai taqi bata dama,hakan yadan sosa mata rai,tasake bada qaimi,amma azahiri saikace ko a jikin mmn amir wai an mintsini kakkausa,duk da zuciyarta cike take da kishi fal.
Chapter 13 · 0% Book details